Alakar Katin “Shedar Zama Dan Kasa” Da Mahimmancinsa Ga Ci Gaban Kasa (1)

Bincike na musamman kan fa’idar katin shedar zama da dan kasa da alakarsa da ci gaban kasa. Wannan shi ne kashi na daya.

411

Matashiya

Ranar Alhamis, 28 ga watan Agusta ne shugaban kasar Najeriya ya kaddamar da sabon katin shedar zama dan kasa irin na zamani mai dauke da kariya, wato: National Electronic Identity Card (e-ID), wanda a cewarsa, nan gaba shi ne zai zama katin shedar zama dan Najeriya ga kowane dan kasar nan, bayan wasu fa’idoji day a zayyana, kamar yadda Hukumar Lura da Shedar Zama Dan Kasa (National Identity Management Commission – NIMC) ta sha sanarwa, kafin wannan rana da aka taru don kaddamar da katin.

Bayan zama shedar kasancewarka dan Najeriya, wannan kati zai ba ka damar aiwatar da abubuwa da dama, a zamanance.  Daga ciki akwai iya aiwatar das aye-da-sayarwa ta hanyar na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani a jimlace, wato “Electronic Payments/Transactions” kenan.  Sannan, a cewar wannan hukuma, kana iya amfani da katin wajen cire kudadenka daga na’urar ATM (Automated Teller Machine) da ke kafe a kofofin bankunan Najeriya, ko iya biyan kudin hajar da ka saya ta amfani da na’urar cinikayya dake kafe a galibin shagunan sayar da kayayyakin masarufi a biranen kasar nan, wato: “Point of Sales” (POS), da dai sauran hanyoyi ko na’urori masu iya fahimtar sakonnin dake like a jikin kati ta hanyar siginar bayanai na zamani.  Wannan, a cewar shugaban wannan hukuma ta NIMC, ba karamar ci gaba bace.  Domin ‘yan Najeriya za su samu damar shiga sahun kasashen da suka ci gaba a wannan fage, ba tare da bata lokaci ba.

A wannan mako za mu dubi wannan tsari ne na bayar da katin shedar zama dan kasa, da siffofinsa, da fa’idojinsa ga daidaikun ‘yan Najeriya, da kuma gamammiyar fa’idar ci gaba da ake hasashen wannan tsari zai iya samarwa, don kawo ci gaba.  A karshe kuma za mu dubi kalubale da wasu ke ganin wannan tsari zai iya cin karo da shi – musamman ganin tambarin kamfanin “Mastercard” na kasar Amurka a jikin katin da aka fara bugawa a yanzu –  da shirin da hukumar tace tayi wajen ganin ba a samu matsala ba.  Galibin tattaunawarmu zai ta’allaka ne ga mahangar tsarin sadarwa na zamani.

- Adv -

Tarihi da Asali

Sabanin yadda wasunmu za su yi tunani, wannan tunani na samar da Katin shedan zama dan kasa ba sabon abu bane.  Ba tsari bane da tsohon Shugaba Obasanjo ko Babangida ko kuma Jonathan suka fara tunanin kawowa ba.  A a.  Tunanin samar da katin shedar zama dan kasa ya samo asali ne tun shekarar 1976; tsakanin lokacin mulkin Marigayi Murtala Muhammad da Obasanjo. To amma saboda wasu dalilai na siyasa ko dabi’ar shugabanci, hakan bai samu ba.  Bayan gushewar wannan gwamnati har wa yau an samu wani yunkuri na kokarin samarwa ko tabbatar da wannan tsari na katin shedar zama dan kasa a lokacin mulkin Shugaban kasa Shehu Shagari.  Mataimakinsa, wato Alex Ekweme ya tabbatar da cewa lallai yayi kokari matuka wajen ganin gwamnati ta samar da wannan tsari a sadda suke mulki, amma nan ma, saboda wasu dalilai na dabi’ar shugabanci, abu bai samu ba.  Bayan wannan kokari, dawowar tsohon Shugaba Obasanjo ma an dawo da wannan tsari, wanda ya sha kasa; ba a samu wata natija mai fa’ida ba, kamar yadda na san mai karatu ya san wannan tarihi gajere.  Sai kuma yunkurin da wannan gwamnati mai ci keyi wajen tabbatar da wannan tsari.  Duk wata fa’ida da za a zayyana ko yi hasashen samunta karkashin wannan tsari, ta ta’allaka ne kacokam ga karfin zuciyar gwamnati wajen ganin tsarin ya cinma nasara.

Manufa

Manufar samar da wannan tsari dai ita ce don tabbatar da tsari a kasa.  Wannan a fili yake ga duk wanda ya san abin da ke gudana a kasashen da suka ci gaba da masu tasowa.  Kusan dukkan wata kasa da za ka zayyana ta a duniya yanzu za ka samu tana da wannan tsari.  Wannan tsari na samar da wani Rumbun Bayanai ne na kasa, wato “National Database” wanda ke dauke da bayanan ‘yan kasa gaba dayansu; da shekarunsu, da launin fatansu, da launin idanunsu, da matakin iliminsu, da matsayinsu a rayuwa, da tsawon jikinsu, da sana’a ko aikinsu, da kwarewarsu a fanni ko sana’a ko aikin da suke yi, da abubuwan da suke sha’awa a rayuwa, da addinansu, da al’adunsu, da bangaren da suka fito a Najeriya, da inda aka haife su, da inda suke zaune a sadda aka basu katin, da makarantun da suka yi karatu, da tambarin yantsun hannayensu guda goma, da hotunan fuskokinsu, da sauran bayanan da suka shafe su da nan gaba za a iya lodawa a shafukansu.

Wadannan bayanai, idan ka hada su gaba daya, na yawan ‘yan Najeriya da suka cika shekaru 16 zuwa sama, za ka ga samu wani kundin bayanai ne mai tsada, wanda a duk duniya babu irinsa.  Muddin komai ya tafi daidai, wannan zai taimaka wa hukuma ne wajen aiwatar da abubuwa da yawa da za su samar da ingancin rayuwa da ci gaban kasa baki daya.  Wannan tasa hukumomi a wasu kasashe tuni suka yi nisa wajen wannan tsari.  A galibin kasashe ta hanyar wannan Rumbun Bayanai na kasa hukuma ke yin alaka tsakaninta da talakawan kasarta.  Don haka, babbar manufar samar da wannan tsari shi ne don tsara bayanan da suka shafi ‘yan Najeriya wuri daya, da yin amfani da wadannan bayanai wajen ci gaban kasa.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.