Amfanin Fasahar Intanet

A ƙasidar da ta gabata, na yi alƙawari cewa zan turo bayanai kan yadda ake Gina Gidan Yanar Sadarwa (Web Designing) da kuma amfanin da ke tattare da fasahar Intanet. Amma hakan bazai yiwu ba a lokaci ɗaya, saboda tsoron tsawaita ƙasidar. Don haka, a wannan mako za mu kawo bayani ne kan amfanin Intanet, in yaso a mako mai zuwa sai mu kawo bayanai kan yadda ake gina gidan yanar sadarwa, in Allah Ya yarda. Don haka a gafarceni!

358

Wata Duniya Sabuwa

Fasahar Intanet wata duniya ce mai zaman kanta. Babban hadafin ƙirƙiro wannan fasaha a farkon lamari dai shi ne don sadarwa tsakanin jama’a ko ma’aikatu, kamar yadda bayanai suka gabata a ƙasidar farko. Amma saboda tasirin wani yanayi da turawa ke kira Killer Application, Fasahar Intanet a yau ta zama gagarau. Domin bayan hanyoyin sadarwa, a Intanet idan bayanai kake so tsagwaronsu, zaka samu ta hanyoyi da dama; ko dai ta hanyar Matambayi Baya Ɓata, wato Search Engines – Yahoo!, Google, AltaVista, Lycos dsr – ko kuma ta Tsararrun Hanyoyin Neman Bayanai, wato Directories. Har wa yau, akwai wasu nau’uka na bayanai waɗanda suka shafi sauti, irin na waƙe ko muhadara ko kuma hotuna, duk zaka iya samunsu ta hanyar Intanet.

Idan haduwa da mutane kake son yi, duk abu ne mai sauƙi. Daga waɗanda ka sani zuwa waɗanda baka sansu ba, duk akwai hanyoyin da zaka iya haduwa dasu. Idan ma hira kake son yi da mutum, har kaji ga-ka-ga-shi, shima wannan ba matsala bane. Shiga Yahoo Messenger, ko MSN Messenger ko kuma ICQ Chat Messenger, muddin wanda kake son hira dashi yana da irin waɗannan hanyoyi kuma ya bude su, yanzu zaku yi rubutacciyar hira. Kai, in ma muryarsa kake son ji, akwai yanda za ka ji har ma ka ga hotonshi yaga naka. Idan kuma mutane da dama kake son hira dasu a lokaci ɗaya, duk za ka iya.

Dangane da ilimi kuwa, a Intanet samun digiri (Degree) har da digirgir (Masters) da dingirewa (Phd), ba wata matsala bace. Za ka iya shiga makaranta ka dauki darasi, ka nemi bayanai wurin malaminka, kayi jarabawa har ka samu sakamako. Babban jami’ar da ke cin karenta ba babbaka a duniyar Intanet, ita ce Jami’ar Phoenix, wato Phoenix University. A kalla ta yaye dalibai sama da dubu arba’in da biyar. Intanet har wa yau wata duniya ce ta ma’adana bayanai, wato Laburare. Mutum ya zauna da jahilcin wani abu, bayan ya iya rubutu da karatu – alhali ga Intanet – shi ya so. Duk bayanin da kake bukata a kan menene, zaka sameshi (muddin wani yayi rubutu a kansa). Idan takamarka karatun jarida ne, an gama! Dukkan wata jarida da ka san ta shahara a duniya – New York Times, Washington Post (Amurka), Financial Times, The Guardian (Ingila), China Daily (Sin), Frankfurt Zeitung (Jamus), Al-Watan, Ukaaz (Saudiyya), Ath Thaurah, Tishreen, Al Ba’th (Syria) – duk zaka samesu a Intanet. Idan ma jaridun Nijeriya kake son karantawa, shi yafi komai sauƙi; daga Weekly da Daily Trust, zuwa Guardian, This Day, Punch, Vanguard, Gaskiya Tafi Kwabo, duk akwai su. Sai ka karanta su ma kafin a fara sayar da su a biranen da ake bugawa ko yaɗa su. Idan kana son karanta irin binciken da wasu masana suka yi kan wasu al’amura, duk samammu ne a Intanet. Dukkan wata ƙasa da ka sani zaka iya samun bayaninta a Intanet, ka karanta ko ka ma yi dukkan abin da ka ga daman yi dashi, ya rage naka.

In kuma abokiyar rayuwa kake so na aure, an gama. Ba mata kadai ba, har da maza suna nan; daga kowace ƙasa a duniyan nan, mai kowane irin matsayi – na addini, ilimi ko dukkan wani rabo na rayuwa – ga hotunansu nan birjik. In ma marasa hotuna kake bukuta duk suna nan.

Samun zaurukan hira da “Majalisun” Tattaunawa (Mailing Lists) kuma wannan wani abu ne da sai ka samu kanka a wurin. Zauruka na nan iri iri; akwai waɗanda zaka shiga ko da baka da rajista dasu, ka karanta abin da kake so a zaurensu, wato Bulletin Board. Kashi na biyu shi ne wanda sai kana da rajista zaka iya shiga ka ga irin wainar da ake toyawa. A zauruka ko”Majalisu” irin waɗannan, akwai kananan zauruka daban daban inda ake tattauna harkoki daban daban na rayuwa. Zaka ilmantu har sai ka ture karatu. Samun abokai maza da mata a irin waɗannan zauruka ba bakon abu bane. Don a ciki zaka samu dan ƙasar Sin, da dan ƙasar Amurka, da waɗanda suke dangi ne daga nan Afirka da sauran jihohin duniya baki ɗaya. Har wa yau, zaka ci karo da dan Nijeriya, dan Arewa ko ma wanda garinku ɗaya ne dashi.

A Intanet harkokin kasuwanci su suka fi yawa da bunkasa. Wannan a bayyane yake. Saye zaka yi ko sayarwa, duk kana da filin tallata hajarka. Zaka saya kuma ka sayar. Duk wani abin da ka san dan Adam na rayuwa dashi zaka sameshi ka saya a kasuwannin da ke duniyar Intanet. Duk da yake wannan ya fi shahara ne a kasashen Turai da sauran kasashen da suka ci gaba, a nan Najeriya ma an samu wani Gidan Yanan Sadarwa dake da shaguna da kantuna a Legas da sauran biranen Najeriya, inda zaka iya sayen kayayyaki, ka kuma biya da Naira, ba da Katin Adashin Banki ba, wato Credit Card. Zaka samu wannan Gidan Yanan Sadarwa a: www.shopforless.com. Daga kayayyakin masarufi, kayan ofis, kwamfuta, duk zaka iya zaba, ka aika da odarka, adireshin gida ko ofishinka, da kuma Lamban Adashin Bankinka, wayau Account Number da sunan bankin da kake ajiya. Kafin kace me? An aiko maka dasu duk inda kake a Nijeriya.

A bangaren addini ma ba a bar Intanet a baya ba. Wane mutum! Daga masallatai zuwa majami’ai (Churches), duk ba matsala bane saduwa da su. A kasashen da suka ci gaba, zaka samu kusan dukkan masallatai na da adireshin Wasikar Hanyar Sadarwa, wato E-mail. Zaka karanta Al-Kur’ani mai girma yadda kake so. In ma karatun ya ishe ka, zaka iya jona sifikan kwamfutarka don sauraro, kyauta! In kuma so kake ka rubuta ƙasida ko makala wanda a ciki akwai ayoyin Kur’ani, akwai Gidajen Yanan Sadarwa waɗanda aikinsu shi ne kawai su taimaka maka neman kowace aya kake so, a kuma kowace Sura ta Kur’ani ayar take, tsaf! In lokutan Sallah kake bukata na kowane birni a duniyan nan, akwai. Kai! Ba ma lokutan Sallah kadai ba, in kana son jin kiran Sallah a bayyane, zaka iya diro (Downloading) dashi zuwa kwamfutarka, ka jona sifika don sauraro. Idan ma so kake ka karanta Baibul (Bible), duk akwai shi; daga na harshen Turanci, Hausa, Jamusanci, Faransanci, duk sai ka ture.

- Adv -

A fannin lafiya ma fa ba a bar duniyar Intanet a baya ba. Komai da ruwanka kenan! Zaka iya hira da likita, ka gaya masa matsalarka, ya kuma baka shawara. Abin da sai ka biya kudi in asibitin kaje. Zaka samu bayanai akan kowane irin magani kake sha na wani cuta da tasirinsa; idan ma akwai wani nau’in maganin da ya bayyana a lokacin da kake wannan bincike, duk zaka gani a rubuce.

Idan kafar yada furofaganda kake nema, to ka samu, da zaran ka shigo Giza-gizan sadarwa ta Intanet. Domin babu hanyar sadarwar da tafi Fasahar Intanet tasiri wajen yada manufa da furofaganda. Duk wasu ƙungiyoyin duniya da ka sani, suna da Gidajen Yanar Sadarwa wanda suka tanada don yada manufarsu. Daga kan kungiyar Hizbollah da ke ƙasar Lubnan, Eta dake ƙasar Andalus (Spain), Hamas da ke Palasdinu, IRA da ke ƙasar Ailand (Ireland), Tamil Tigers da ke ƙasar Philiphines, da sauran kungiyoyin duniya, duk suna yada manufofinsu ta hanyar Intanet. Kai a kasashen Turai da Amurka, galibin harkokin siyasa duk ta Intanet ake gabatar dasu. Zaka samu kowane dan takara ya tanadi Gidan Yanan Sadarwa don yin kamfen. Hatta jam’iyyun siyasa duk ba a barsu a baya ba. Wannan na faruwa ne saboda a duniyar Intanet kowa na da ‘yancin fadin albarkacin bakinsa. Idan hakan yai maka zafi, sai ka zuba naka ra’ayin. Abu mai sauƙi!

Wani Hanzari. . .

Sai dai fa, idan ka hangi fari-fari daga nesa, inji Hausawa, da zarar ka matso kusa zaka ga baƙi-baƙi. A duniyar Intanet ma haka al’amarin yake. A hanyarka ta neman bayanai in baka yi hankali ba sai ka faɗa hannun miyagu! Ɓarayi kuwa yadda ka san a kasuwan kauye kake. Gidajen Yanar Sadarwa na batsa da wasan kwamfuta (Computer Game) da Caca kuwa, ruwan dare ne. In har ka sake ka samu kanka a farfadan ɗaya daga cikinsu, kafin ka fita sai kai da gaske. Wannan ya faru ne saboda miyagun na amfani ne da wata Masarrafa (Software) dake makure Dan Manunin Kwamfuta (Computer Mouse), wato Mouse- Trapping Software. Shafukan ɓatanci ma na nan, birjik. Wasu shafukan don ɓata ƙadarin wani addini aka tsara su, wasu kuma don ɓata kaɗarin wata al’umma da dai sauransu. Hanyoyin koyar da hakikanin ta’addanci kuwa mai sauƙi ne a Intanet. Daga yadda ake koyar da yin bam da gurneti da sauran kayayyakin sheɗanci, sai yanda ake shirya sharrurruka. Wasu Masana Manhajar Kwamfuta (Computer Programmers) kuma basu da wata manufa illa na ɓata ma al’umma kwamfutocinsu ta hanyar aiko da wasu Rikitattun Bayanai (Virus) masu haukatar dasu. Hanya mafi sauƙi wajen magance waɗannan matsaloli shi ne kasan inda za ka tafi, kawai. Muddin ka san inda ka dosa, ba ka da matsala. Amma idan ka tsaya walagigi da gutsiri-tsoma, kai ka jiyo!

Siffofin Intanet

Duk wannan haɓaka da Fasahar Intanet ta samu na da nasaba ne da wasu siffofi guda uku da suka banbanta ta da sauran hanyoyin sadarwa. Da farko dai zuwan Intanet ya haddasa ƙirƙire-ƙirƙire da dama, na abin da ya shafi dukkan harkokin rayuwa. Na biyu, Intanet wata fasaha ce da ta game dukkan duniya baki ɗaya, wata ƙasa ba zata iya kebance ma kanta ba. Na uku kuma yayin da ta bunƙasa, duk sai ta laƙume sauran fasahar sadarwa da ake dasu irin su wayar tarho, radiyo, jaridu da talabijin. Dukkan waɗannan in kana son yin mu’amala dasu da zaran ka jona Intanet za ka same su ta hanya mafi sauƙi. A taƙaice dai ya sauƙaƙa ma al’umma hanyoyin mu’amala gaba ɗaya.

A halin yanzu tunda mun ji bayanai kan ma’ana da yadda Intanet ke samuwa, da takaitaccen tarihin ƙirƙirarsa, da kuma amfanin da ke tattare da wannan fasaha, a mako na gaba cikin yardan Allah, zan gabatar da bayanai kan yadda ake Gina Gidan Yanan Sadarwa (Web Desiging). Domin gidajen yanan sadarwan ne ake mu’amala dasu a duniyar Intanet. Duk mu’amalar da mai ziyara zai yi, dasu ko a cikinsu zai ƙare yawace-yawacensa.

A dakace ni!

- Adv -

You might also like
2 Comments
  1. Muryar Hausa24 Online Media says

    MASHA ALLAH

    ALLAH YA KARA KAIFIN BASIRA DA NISAN KWANAKI MASU ALBARKA

  2. Auwalu Adamu says

    Masha Allah
    Allah kara basira. Mungode

Leave A Reply

Your email address will not be published.