An Kaddamar da Jami’ar Kimiyya ta Sarki Abdallah

Kamar yadda watakila masu karatu suka ji ko gani a kafafen watsa labaru na gida da ketare, ranar Laraba, 24 ga watan Satunba ne aka kaddamar da “Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Sarki Abdullah” (King Abdullah University of Science and Technology – KAUST) da ke kasar Saudiyya. Wannan biki da aka gudanar ya samu halartar baki daga kusan dukkan kasashen da ake ji dasu a duniya, ciki har da Shugaba Umaru Musa ‘Yar Adua na Nijeriya, sanadiyyar gayyatarsa da aka yi. Ga dan takaitaccen bayani nan kan wannan sabuwar Jami’a.

244

Wannan Jami’a, kamar yadda masu karatu suka ji a labaru, na daya cikin Jami’o’in da ake ji dasu wajen kayayyakin aiki, da kyawawan tsari, da kuma muhallin karantarwa mai kayatarwa.  Hukumar Saudiyya ta dauki tsawon lokaci tana tanadi wajen kafa wannan jami’a, inda aka dauki nauyin masana suka yi ta jele tsakanin manyan kasashen duniya da suka ci gaba a fannin Kimiyya da Fasaha; irinsu Amurka da Nahiyar Turai da Malesiya da Singafo da sauran kasashen da suka ci gaba, don dauko samfurin tsarin da ake ake amfani dasu a jami’o’in wadannan kasashe. An kuma kashe a kalla dalar Amurka biliyan goma ne wajen gina makarantar, wajen naira biliyan dubu daya da dari biyar da arba’in kenan kudin Najeriya.

Wannan Jami’a ce ta Kimiyya da Fasaha tsantsa, kuma tana dauke ne da kwasa-kwasai guda tara rak, wadanda ake iya yin Digirin farko (BSc), da Digirin Digirgir (Masters), sai kuma Digirin Digirgir da Dingirewa (Doctorate Degree) a kansu.  Wadannan kwasa-kwasai dai sune: Fannin Kimiyyar Lissafi ta Kololuwa (Applied Mathematics and Computational Science), da Fannin Kimiyyar Halittu (Bioscience), da Fannin Kimiyyar Sinadarai (Chemical and Biological Engineering), da Fannin Kimiyyar Kwamfuta da Sadarwa (Computer Science), da Fannin Kimiyyar Karkashin Kasa (Earth Science and Engineering).  Sauran fannonin sun hada da Fannin Kimiyyar Lantarki (Electrical Engineering), da Fannin Kimiyyar Muhalli (Environmental Science and Engineering), da Fannin Kimiyyar Makamashi (Material Science and Engineering), sai kuma Fannin Fasahar Kere-kere (Mechanical Engineering).  An tsara wadannan kwasa-kwasai ne don baiwa dalibai ilimi mai amfani da gamsarwa, wadanda zasu iya ciyar da al’umma gaba a ko ina suka samu kansu a duniya.  Kuma kamar yadda bayani ya gabata, shahararrun malaman jami’a da ke kasashe dabam-daban ne suka tsara manhajar karantar wadannan kwasa-kwasai.

Jami’ar bata tsaya wajen samar da muhallin karatu mai gamsarwa da inganci kadai ba, hatta tallafin karatu tana baiwa dalibai.  Ga dukkan alamu, idan bai zo na daya a duniya ba, tallafin da wannan makaranta ke baiwa dalibi na sahun na gaba-gaba a duniya, inda ta sha alwashin bayar da tallafin dalar Amurkar dubu talatin ($30,000) a kalla, ga dalibi. Idan muka juya wannan kudi zuwa nairan Nijeriya, zamu samu a kalla naira miliyan hudu da  dubu dari shida da ashirin kenan (=N=4,620,000). Bayan haka, akwai kuma tallafin kayan karatu da take bayarwa, har da kwamfutar tafi-da-gidanka, wato Laptop, ga dalibai.  Wannan ba wani abin mamaki bane ga kasar Saudiyya, domin tana da makarantu na Jami’a da dama inda take daukar dawainiyar dalibai daga kasashen waje suyi karatu kyauta. A wasu lokutan ma idan kana son aikin karantarwa suna iya baka tun kafin ka bar kasar.  Misali, a Jami’ar Binciken Kimiyyar Fetur da Injiniyanci ta Sarki Fahad da ke birnin Dhahran, gwamnati na baiwa dalibai tallafin karatu – daga kudi, zuwa muhalli, da kayan karatu, da kuma shawarwari daga kwararrun malamai da ke tare da dalibai a unguwanninsu.

Idan ka gama, kayi kokari, kuma kana da sha’awar zama a makarantar, suna iya baka aikin karantarwa ko malanta.  Wannan haka yake a Jami’o’in Madina da Makka (Muhammad bn Sa’ood) da Riyad, da Jidda da sauran wurare.  Har wa yau kasar na da manyan cibiyoyin binciken kimiyya da fasaha, musamman ta hanyar sadarwar kwamfuta bila-adadin.  Kamar yadda masu karatu ne suka sani, kasar na samun kudin shiganta ne galibi daga kudin danyen man fetur da take sayarwa, kamar kasarmu, duk kuwa da cewa Nijeriya ta riga Saudiyyar samun man fetur da shigar dashi kasuwannin duniya a matsayin hajar kasuwanci.

- Adv -

Daga karshe, ga wasikar da wani masoyin shafin Kimiyya da Fasaha ya aiko mana nan, kan batun kaddamar da wannan babban Jami’a ta Kimiyya da Fasaha na Sarki Abdullah.  Malam Umar Albasheer mutum ne mai sha’awar fannin Kimiyya da Fasaha, musamman a ce da harshen Hausa ake karantar dashi ko koyonsa.  Kuma yana daga cikin masu begen ganin watarana mun samu Jami’a ta musamman mai karantar da wannan fanni a harshen Hausa, kuma a kasar Hausa.  Allah nuna mana wannan rana ko zamani, amin. Duk wanda ke bukatar Karin bayani dangane da wannan kamaranta, yana iya ziyartar shafin yanarta da ke karshen wasikar Malam Albasheer.  A yanzu dai ga wasikar Malam Umar Albasheer din nan kasa.  A sha karatu lafiya:

……………………………………………………

An bude Sabuwar Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Sarki Abdullah

Salam

Baban Sadiq, ya iyali ya kuma ayyuka? Na rubuto ne, domin ganin cewa
ya dace mutanenmu su san tasiri da mahimmancin bude Sabuwar Jami’ar Fasaha da Kimiyya ta Sarki Abdullah da aka
yi yau a Saudi Arabia, (24th September, 2009), wacce ina ganin har Shugaban Kasa Alhaji Umaru Musa Yar’adua ya samu halarta.

A gaskiya na dade ina bin bayanan kafa Jami’ar tun wajen 2008, sa’ilin
da manazarta daga Saudi da kuma Kasashen Asiya, suka fara gewaya
Jami’oin Fasaha na Kasashen Yammacin Turai, Malaysia, Singapore da dai
sauransu.

To Alhamdulillah, yanzu dai jami’a ta kammalu, domin har an yi taron
bude ta a yau.  Saura dame, kalubalen dake gaba shine, da farko dai,
jami’ar na bada gurbin karo ilmi mai zurfi (M.Sc) da kuma gurbin
karatu na digrin digir-gir wato (Ph.D)  (Schoolarship)  karo karatu na musamman, wanda zai daukewa dalibi kudin makaranta, kudin littafai, kudin magani, in takaita zance har da kudin kwamfutar tafi-da-gidanka wato laptop.

Bugu da kari, suna bada tallafin kudin aljihu na dalar Amurka $30,000.00

Saboda haka, yana da kyau ayi wa jama’a bayani cewa ga wata dama ta samu, wadanda ke karatu a jami’oi ko suke shirin kammala karatunsu a jami’oi, dake karatun fannoni irinsu;

*  Applied Mathematics and Computational Science (AMCS)
* Bioscience (B)
* Chemical and Biological Engineering (CBE)
* Computer Science (CS)
* Earth Science and Engineering (ErSE)
* Electrical Engineering (EE)
* Environmental Science and Engineering (EnSE)
* Materials Science and Engineering (MSE)
* Mechanical Engineering (ME)

Na samu wadannan labaru ne daga shafin yanar gizon jami’ar wato :
http://www.kaust.edu.sa, da kuma daga labarun sha biyun rana na gidan talabijin  Aljazeera.

Daga Mai begen ganin kafuwar Jami’ar Kimiyya Da Fasaha Ta Hausa A Nijeriya.

Umar Albasheer
CEO : My NextGeneration Hosting
http://www.mynextgenerationhosting.com

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.