Baban Sadik

Idan baka samu kasida ko maudu’in da kake nema ba…

A LURA:  Dukkan kasidun dake wannan shafi suna da tsayi, domin kasidu ne da suka kunshi bincike na ilimi, ba wai labaru bane.  Don haka, idan tsayinsu ya gundureka,  kayi hakuri.  Dabi’ar mahallin ne.

Hira da Masana
Baban Sadik

Hira da Edward Snowden (1)

Shahararren dan jarida Peter Taylor, wanda tsohon ma’aikacin BBC ne, ya samu daman hira da Edward Snowden, matashin nan dan kasar Amurka da ya hankado irin badakalar da ke kunshe shirin cibiyar tsaron kasar amurka na satar bayanan mutane da aiwatar da leken asiri cikin rayuwarsu, da sunan yaki da ta’addanci. Wannan kashi na daya ne.

Sauran bayanai »
Hira da Masana
Baban Sadik

Zuwa Sararin Samaniya: Abu Mai Yiwuwa da Mara Yiwuwa (1)

Edward Teller masani ne a fannin kimiyyar sararin samaniya da kimiyyar sinadarai (Physics and Chemistry), kuma ya samar da ka’idojin bincike da kere-keren kimiyya a duniya da dama.  Mutum ne mai wuyan sha’ani a lokacin rayuwarsa, kuma ya shahara wajen rajin kawo sauyin kere-kere a fannin kimiyyar sararin samaniya, inda ra’ayoyinsa suka bambanta matuka da ra’ayoyin abokan aikinsa a fannin ilimi.  Duk da haka, ya yi hasashen yiwuwan faruwa ko rashin yiwuwan faruwar abubuwa da yawa a fannin kimiyya; wasu sun tabbata haka, kamar yadda mai karatu zai gani, wasu kuma basu tabbata ko ba, ana zaman jiransu. Wasu kuma, tarihi ya karyata shi a kansu.  A yau za mu karantu wasu daga cikin hasashensa, wanda daya daga cikin masu karatu, mai kwazo da kokarin bincike, wato MALAM SADIK TUKUR GWARZO (sadiqtukurgwarzo@gmail.com) ya kawo mana.  A sha karatu lafiya.

Sauran bayanai »
Fasaha
Baban Sadik

Jawabin Steve Jobs (2005) – Kashi na Daya

Steve Jobs, wato shugaban kamfanin Apple dake kasar Amurka dai Allah yai masa rasuwa. Saboda wannan munasaba muka ga dacewar kawo wani jawabi da yayi wa dalibai yayin yaye su a Jami’ar Standford dake kasar Amurka, a shekarar 2005. Wannan shi ne kashi na daya. A sha karatu lafiya.

Sauran bayanai »

Waiwaye Kan Darussan Baya (7)

Ga duk wanda ya saba bibiyar wannan shafi tun farkon farawa, ya san mukan yi zama lokaci zuwa lokaci, don yin nazari kan kasidun da muka gabatar a baya, da fa’idar da suka samar, da kura-kuran da aka nusar dani a kai in har akwai, da sakonnin masu karatu, sannan mu ga nan gaba ina muka dosa.    Zuwa makon gobe in Allah Ya so za mu kawo sakonnin da kuka aiko ta waya ko ta Imel.  Akwai sakonnin masu karatu da yawa a tare; wasu ta akwatin Imel ne, wasu kuma ta Facebook, wasu kuma ta wayar salula.  Idan Allah Ya kaimu mako mai zuwa duk za mu zazzago su.  Wannan ita ce marhala ta bakwai, tun farkon fara wanann shafi a shekarar 2006, cikin watan Nuwamba.  Babu wani tazara ko ma’aunin watanni da muka sa don haddade kowace marhala.  Mukanyi irin wannan zama ne kawai idan lokaci ya samu; iya gwargwadon hali.

Sauran bayanai »

Waiwaye Kan Darussan Baya (6)

Wadanda suka saba karanta wannan shafi tun farkon farawa sun san cewa a duk karshen zango, mukan zauna don yin waiwaye, abin da Malam Bahaushe ke kira “Adon tafiya.”  A yanzu shekarun wannan shafi namu shida kenan da watanni shida cif-cif.  Kuma wannan shi ne zama na shida da za mu yi, don yin bitar darussan da muka yi ta kwasa a baya.  Ga wadanda basu san wannan tsari da shafin ke gudanuwa a kai ba, shafin Kimiyya da Kere-kere ya samo asali ne cikin watan Oktoba na shekarar 2006; farkon taken shafin shi ne: Kimiyya da Fasaha.  Mun kuma yi waiwaye karo na daya, da na biyu, da na uku ne a tsakanin shekarar 2006 zuwa 2008.  Zama na karshe da muka yi, wanda shi ne waiwaye na hudu, ya zo ne cikin watan Satumba na shekarar 2008, daidai lokacin da shafin ya cika shekaru biyu kenan.  Ga shi mun sake dawowa a yau don yin nazari kan kasidun baya, a karo na shida, kamar yadda masu karatu za su gani daga taken kasidar.

Sauran bayanai »

Waiwaye Kan Darussan Baya (5)

Wadanda suka saba karanta wannan shafi tun farkon farawa sun san cewa a duk karshen zango, mukan zauna don tattaunawa da juna, da kuma yin waiwaye, abin da Malam Bahaushe ke kira “Adon tafiya.”  A yanzu shekarun wannan shafi namu biyar kenan da watanni shida cif-cif.  Kuma wannan shi ne zama na biyar da za mu yi, don yin bitar darussan da muka yi ta kwasa a baya.  Ga wadanda basu san wannan tsari da shafin ke gudanuwa a kai ba, shafin Kimiyya da Kere-kere ya samo asali ne cikin watan Oktoba na shekarar 2006; farkon taken shafin shi ne: Kimiyya da Fasaha.  Mun kuma yi waiwaye karo na daya, da na biyu, da na uku ne a tsakanin shekarar 2006 zuwa 2008.  Zama na karshe da muka yi, wanda shi ne waiwaye na hudu, ya zo ne cikin watan Satumba na shekarar 2008, daidai lokacin da shafin ya cika shekaru biyu kenan.  Ga shi mun sake dawowa a yau don yin nazari kan kasidun baya, a karo na biyar, kamar yadda masu karatu za su gani daga taken kasidar.

Sauran bayanai »

Shafin Kimiyya Da Fasaha Ya Sauya Take

Na tabbata masu karatu sun lura da sauyin take da aka samu a wannan shafi, daga “Kimiyya da Fasaha” zuwa “Kimiyya da Kere-kere”.  Hakan ba kuskure bane na mashin, lokaci ne yayi da ya kamata wannan sauyi ya samu. A takaice ma dai, har wasu cikin masu karatu sun bugo waya don nuna farin cikinsu da wannan canji da aka samu. Duk da haka mun ga dacewar gabatar da fadakarwa da kuma dalilan da suka haddasa hakan.

Sauran bayanai »

Waiwaye Kan Darussan Baya (4)

A yayin da kamfanin Media Trust, mai buga jaridar AMINIYA ke bukin cika shekaru biyu da fara wannan jarida mai matukar farin jini, mu ma a wannan shafi na Kimiyya da Fasaha, bayan taya AMINIYA murnar kaiwa wannan lokaci, na farin cikin sheda wa masu karatu cewa a cikin mako mai zuwa, shafin Kimiyya da Fasaha zai cika shakaru biyu cur! Ga wadanda suka fara bibiyan wannan shafi daga lokacin da ya fara bayyana zuwa yanzu, watakil suna iya tuna kasidar farko da ta fara bayyana a wannan shafi, mai taken Fasahar Intanet a Saukake (1).  Hakan ya faro ne cikin watan Okotobar shekarar 2006.  A yau, cikin yardan Allah, sai ga mu gab da Oktoba ta shekarar 2008.  Shekara kwana, in ji Bahaushe!  Wannan tasa muka ga dacewar zama na musamman, kamar yadda muka yi a lokutan baya, don yin waiwaye; abin da Malam Bahaushe ke kira adon tafiya.

Sauran bayanai »

Waiwaye Kan Darussan Baya (3)

Idan mai karatu bai mance ba, makonni kusan ashirin da suka wuce ne muka zauna don yin Waiwaye Adon Tafiya kashi na biyu.  A yau kuma cikin yardar Allah gashi mun sake dawowa don maimaita irin wannan zama.  Kamar yadda muka sha fada, amfanin wannan zamfa shi ne don yin tsokaci, tare da kallon baya, da halin da ake ciki, da kuma inda za a dosa nan gaba.  A yau ma kamar sauran lokutan baya, mun kasa  wannan kasida zuwa kashi hudu da kuma kammalawa.   A bangaren farko za mu yi bita kan kasidun baya.  Sai kuma bayani kan mahangar da wadannan kasidu suka ginu a kai.  Daga nan sai muyi tsokaci kan wasikun masu karatu.  Ba wai nassin wasikun za mu kawo ba, don kusan duk na amsa su ko.  Sai abu na karshe, wato bayani kan inda muka dosa a zango na gaba.  Sai a biyo mu!

Sauran bayanai »

Waiwaye Kan Darussan Baya (2)

Duk tafiyar da aka kawata ta da waiwaye, to akwai watakilancin samun nasara cikinta, in Allah Ya yarda.  Da wannan muka ga dacewar ci gaba da wannan salo na “Waiwaye Adon Tafiya”, a wannan shafi mai albarka.  Idan masu karatu basu mance ba, wannan shi ne karo na biyu da muka sake zama don yin nazari kan kasidun da suka gabata, kafin mu sake canza salon tafiya don ci gaba.  A wancan karo mun yi waiwaye ne saboda ganin mun samu bayanai kan yadda ake sarrafa shafukan yanan gizo, da kuma tarihin da ke tattare da asalinsa.  Wannan shi ne daman abin da ya kamata mai koyo ya sani.  Hakan kuma ya faru ne a mako na bakwai da fara assasa wannan shafi.  A yau sai ga mu a mako na ashirin da takwas!  Tirkashi!  Don haka naga dacewar mu sake zama don kallon baya; ina muka fito?  A ina muke?  Kuma ina muka dosa?

Sauran bayanai »