Bangarorin Wayar Salula (1)

Kashi na takwas cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

321

Mabudin Kunnuwa

Kasancewar wayoyin salula kayayyakin fasaha ne da aka kera su da na’urori da sinadaran fasaha da kimiyyar lantarki, ya zama wajibi mu san irin tsarin da suke gudanuwa a kai. Wannan zai sawwake mana lalurori da dama.  Misali, idan muka san tsarin babbar manhajar da waya ke amfani da ita, za mu san yadda ake sarrafa waya mai irin wannan manhaja. Idan muka san tsari da nau’in batirin da take amfani dashi, hakan zai taimaka mana wajen fahimtar tsarin caji da za mu rika yi.  Idan muka san dabi’ar waya ta hanyar yanayi da kirarta, hakan zai sawwake mana matsaloli da dama.  Wannan tasa yau muka dauko wannan bangare don gabatar da bayanai iya gwargwado, kan bangarorin wayar salula.  A yau mai karatu zai san dukkan karikitan da wayar salula ke dauke dasu; masu motsi da marasa motsi; wadanda ake gani da wadanda ba a ganinsu sai dai a hankalci tasirinsu kawai.  Kafin mu kutsa cikin wannan bayani, zai dace mu yi ‘yar gajeriyar gabatarwa kan dukkan wadannan karikitai.

Ita dai wayar salula na dauke ne da muhimman bangarori guda biyu; bangaren gangar-jiki da kuma bangaren ruhi ko rai.  Wannan shi ne tsarin da dukkan kayayyakin sadarwa ke gudanuwa a kai, irinsu Kwamfuta, da na’urar daukan hoto, da talabijin irin na zamani da sauransu.  Kowannesu na dauke ne da gangar-jiki da kuma bangaren ruhi.  Bangaren gangar-jiki shi ne ake kira Hardware, ko kuma kwarangwal a Hausar zamani.  Shi ne bangaren da mai karatu ke gani, kuma yake iya tabawa.  Sai bangaren ruhi ko masarrafa, wanda a turance ake kira Software ko Firmware a turancin sadarwa ta zamani.  Wannan bangare ya kumshi ruhin da wayar ke gudanuwa a kansu, wanda mai mu’amala ke iya gani a fuskar wayar ko masu gudanuwa a karkashin kasa.  A halin yanzu ga bayanai nan dalla-dalla kan wadannan bangarori.  Sai a kasance tare damu.

Gangar-jikin Wayar Salula

Gangar-jikin wayar salula, kamar yadda bayani ya gabata a sama, shi ne “kwarangwal” ko kuma dukkan wani abin da za ka iya tabawa a jikinta. A turance su ake kira Hardware.   Su ne bangare na biyu da ke da muhimmanci a wayar wajen sadarwa.  Abu na farko cikin wannan bangare shi ne inji, wanda ke dauke da sauran bangarorin ta hanyoyi dabam-daban.  Wannan bangare dai shi ne kashin bayan wayar baki daya. Yana dauke ne da karafa, da robobi, da batir, da kuma cibiyoyi masu muhimmanci ga rayuwar wayar; irinsu Cibiyar Sadarwa (Network Point), da Cibiyar Wutar Lantarki (Circuit), da Cibiyar Samar da Caji (Charging Point) da dai sauransu.  Har wa yau, wannan bangare na dauke ne da ramuka kanana, da layukan wutar lantarki masu nuna hanyar da kowace waya ke bi don isar da wutar lantarki ko sinadaran sadarwa a yayin da ake amfani da wayar ko take zaman dirshan.

- Adv -

Abu na biyu bayan gangar-injin shi ne Cibiyar Sadarwa, wato Network Point.  Kamar yadda mai karatu yaji sunan, aikin wannan bangare shi ne samar da sinadaran sadarwa ko kuma tsarin sadarwa (wato Network).  Idan mai karatu ya dubi fuskar wayarsa zai ga alama ko tambarin da ke nuna halin sadarwar da ke tsakanin wayarsa da kamfanin sadarwar da yake amfani da katin SIM dinsu.  Wannan cibiya ce ke daidaita sahu tsakanin wayar da tsarin sadarwar da ke bigiren da mai wayar ke zaune.  Wasu lokuta yanayin sadarwa yayi sama, wasu lokuta kuma yayi kasa.  Har wa yau, karfin wannan cibiya wajen jawo yanayin sadarwa ga mai amfani da wayar ya danganci nau’in wayar da yake amfani da ita.  Misali, wayoyin Nokia sun yi suna a duniya wajen karfin jawo yanayin sadarwa a waya fiye da sauran wayoyi.

Ire-iren wayoyin da ke fitowa daga kasar Sin a halin yanzu (masu arha da matukar kara wajen kidi), galibinsu basu da karfin inganci wajen jawo yanayin sadarwa a waya.  Shi yasa idan kana waje daya da mai wayar salula ‘yar kasar Sin, kai kuma kana rike da ta asali irinsu Nokia ko Motorola, sai ka fi su samun yanayin sadarwa a lokaci guda.  Duk da yake hakan ya danganci wurin da kake ne, da kuma karfin na’urar kamfanin da ke baka sadarwa.  Wannan cibiya ta sadarwa dai a karshe, tana jone ne da kunnen sadarwar wayar salula, wato Antenna, wacce ke gine cikin galibin wayoyin salula na zamani.

Bangare mai muhimmanci na uku shi ne Cibiyar Wutar Lantarki, ko Circuit a turance.  Wannan bangare ne ke samar da wutar lantarkin da wayar ke amfani dashi wajen sarrafa sauran gabobinta.  Bangaren na like ne da ramin samar da caji, ko Charging Port a turance.  Cibiyar Wutar Lantarki na like ne a jikin inji, kamar yadda Cibiyar Sadarwa take.  Kuma ita ce ke samar da wutar lantarki ga injin wayar, ta hanyar batir.  Kamar Cibiyar Sadarwa, Cibiyar Wutar Lantarki ita ma tana da alama ko tambari a fuskar wayar, wanda ke nuna yanayin caji ko karfin wutar lantarkin da ke dauke da wayar a kowane lokaci.  Idan caji yayi kasa, sai alamar ta gangara, kamar yadda muka saba gani a fuskar wayoyinmu.

Bangare na hudu kuma shi ne batir, wanda na san masu karatu sun sanshi.  Yana daya daga cikin shahararrun bangarorin wayar salula; saboda tasiri da kuma amfaninsa wajen baiwa wayar rayuwa a dukkan lokuta.  Shi batir na dauke ne da sinadaran lantarki nau’uka dabam-daban, dangane da yanayin aikinsa.  Galibin batiran da kamfanonin kera wayoyin salula ke kerawa suna dauke ne da sinadaran Lithium-ion Phosphate.  Wadannan sinadarai aikinsu shi ne taskance karfin lantarki (Electric Current) da ke shigowa ta kogon lantarkin (Charging Port) mai mu’amala da na’urar caji, wato Charger.  Idan wadannan sinadarai na lantarki sun shigo sai a taskance su tsibi-tsibi.  Da zarar sun cika, sai wayar taci gaba da amfani dasu.  Wadannan batira dai sun sha bamban da batiran rediyo da muka saba amfani dasu.  Su batiran rediyo (kanana da manya) da zarar an gama zagwanyar da karfinsu, sai  su mace.  Amfaninsu ya kare kenan.  Sai dai a siyo wasu.

Amma su nau’in Lithium-ion Phosphate taskance sinadaran lantarkin suke yi, idan suka samu iya gwargwadon da suke bukata, sai su daina karban sinadaran lantarkin. Daga nan sai a ci gaba da amfani da su har zuwa lokacin da zasu zagwanye.  Idan suka zagwanye, sai a sake jona su cikin lantarki don su kara taskance wadannan sinadaran lantarki kamar yadda aka yi a baya.  Akan dauki a kalla shekara guda ana amfani dasu kafin tagomashinsu ya kare. 

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.