Bincike Kan Bacci da Mafarki a Mahangar Kimiyya (4)

Wannan shi ne kashi na hudu na kasidarmu kan bacci da mafarki a mahangar kimiyya. A sha karatu lafiya.

282

Bacci a Mahangar Musulunci

Bayan bayanan da suka gabata daga masana fannin kimiyya da dabi’ar dan adam dangane da ma’ana da samuwar bacci, da abin da suka gano da kuma abin da ya bace musu, lokaci ya yi da ya kamata mu koma bangaren Musulunci mu ji me yace dangane da bacci, da kuma nau’ukansa, da tsarin yinsa, da kuma dalilan da suka sa a musulunce aka kawo yanayi da tsarin yadda ake bacci.  Shin, akwai fahimtar juna tsakanin nassoshin Kur’ani da na Hadisai a bangare daya, da na malaman kimiyya da fannin dabi’ar dan adam kan abin da ya shafi bacci, a daya bangaren?  Wannan shi ne abin da za mu duba kafin mu shiga bayani kan mafarki shi kuma, da yadda yake samuwa.

Bacci a Kur’ani

A cikin Kur’ani mai girma malaman musulunci suka ce Allah ya ambaci kalmar “bacci” (An-Nawm) a wurare tara, da kalma daya, sannan ya ambaci nau’ukan bacci guda biyar da a baya mai karatu ya karanta yanayinsu, wadanda Malaman Kimiyya suka gano daga baya sosai.  Wannan, a cewar Farfesa Ahmad BaHammaan, kwararre a fannin kiwon lafiya kuma masani a bangaren cututtukan da suka shafi bacci a daya daga cikin jami’o’in kasar Saudiyya, na daga cikin dalilan da ke nuna matukar muhimmancin da addinin musulunci ya baiwa bacci a addinance.  Domin bayan yawan ambato, wanda hakan ke nuna himmatuwa da abu, ya kuma ambaci bacci a yanayi a kalla biyar.  Wadannan ayoyi duk suna cikin Kur’ani mai girma da muke karantawa dare da rana safe da yamma. Mu dauke su daya bayan daya mu gani.

Wuri na farko na cikin Suratul Baqara aya ta 255, wato Ayatul Kursiyyu kenan.  A farkon wannan aya Allah yace: “Allah, babu abin bautawa a bisa cancanta face Shi; Rayayye, Dawwamamme; gyangyadi ba ta kama Shi balle bacci…”  A nan Allah na nuna mana girman kudurarsa ne, da dawwamarsa, inda ya zama a kullum a tsaye yake wajen tafiyar da lamuran bayinsa, dare da rana safe da yamma.  Abu na biyu da ayar ke nuna mana shi ne raunin dan Adam, da cewa ba zai taba rayuwa babu gyangyadi ko bacci ba.  Sai wuri na biyu, cikin Suratul A’araaf aya ta 97, inda Allah ke cewa: “Shin, mutanen  alkaryu sun amince wa azabarmu ta je musu da dare, alhalin suna bacci?”  Wannan aya ita ma tana nuna mana karin raunin dan adam ne, da nuna cewa bacci dabi’arsa ce, kuma a sadda yake bacci, rauninsa na kara ninkuwa ne, sai yadda aka yi da shi.

Sai wuri na uku cikin Suratul Anfaal aya ta 43, inda Allah ke cewa: “A lokacin da Allah ke nuna maka su suna kadan, a cikin baccinka…”  Wannan aya ta zo ne cikin jerin ayoyin da ke bayani kan abin da ya faru lokacin yakin Badar, da cewa Allah Ya nuna wa Manzon Allah adadin kafirai cikin mafarki, amma sai aka ambaci bacci, saboda mafarki na samuwa ne cikin bacci.  Sai wuri na hudu cikin Suratul Furqaan aya ta 47, inda Allah ke cewa: “Kuma Shi ne wanda ya sanya muku dare ya zama tufa, kuma bacci ya zama hutu…”  Wannan aya na nuna mana cewa bacci na cikin ni’imomin Allah ga bayinsa, domin lokaci ne da jikin dan adam ke sake sabunta yanayinsa baki daya, kamar yadda likitoci suka tabbatar.

Sai wuri na biyar, cikin Suratur Room aya ta 23, inda Allah ke cewa: “Kuma daga cikin ayoyinsa akwai baccinku cikin dare da yini…”  Wannan ma tana magana ne kan cewa lallai bacci ni’imar Allah ce ga bayinsa.  Sai wuri na shida cikin Suratus Saaffaat aya ta 102, inda Allah ke cewa: “To, a lokacin da ya isa aiki tare da shi, sai yace: ‘Ya karamin da na! Lalle ne na gani a cikin bacci lalle ina yanka ka…”  Wannan ayar na bayani ne kan dalilin da ya sa Annabi Ibrahim (AS) yayi yunkurin yanka dansa Annabi Isma’il, amma daga baya Allah ya fanshi dan.  Abin da ayar ke fa’idantarwa dangane da maudu’in zancenmu shi ne, ta hanyar mafarki Allah ya umurci Annabi Ibrahim ya yanka dansa, kuma wannan, kamar yadda muka sani, shi ke nuna cewa lalle bacci na daga cikin hanyoyin da Allah ke yi wa Annabawa da Manzanni wahayi, tunda ga shi har ya yi azama zai aiwatar da abin da ya gani.

- Adv -

Sai wuri na bakwai cikin Suratuz Zumar aya ta 42, inda Allah ke cewa: “Allah ne ke karbar rayuka a lokacin mutuwarsu, da wadannan da basu mutu ba, a cikin baccinsu…”  Wannan ayar na cikin ayoyi masu dauke da babban abin al’ajabi dangane da bacci, da hanyar yinsa.  Bayani zai zo kan al’amuran da suka shafi sakon da ke cikinta nan gaba.  A takaice dai mun fahimci cewa Allah ya ambaci bacci a cikin wannan, da cewa yana karbar rayuka a lokacin bacci.  Sai wuri na takwas a cikin Suratul Qalam aya ta 19, inda Allah ke cewa: “Wani mai kewayawa daga Ubangijinka ya kewaya a kanta (ya kone ta), alhalin suna bacci…”  A nan Allah na bamu kissar wasu samari ne marowata da Ubansu ya mutu, alhali mai karamci ne shi, su kuma suka sha alwashin hana zakka da hana masakai daga abin da suka gada na amfanin gonar Ubansu, amma kafin su girbe, sai Allah ya aika Mala’iku suka kone ta cikin dare, sannan suna bacci.  Wannan ke nuna karin raunin dan adam sadda yake bacci, da kuma cewa yadda Allah ke da iko a kanshi sadda yake farke, haka ake da iko a kanshi sadda yake bacci.  Sai wuri na karshe a cikin Suratun Naba’i aya ta 9, inda Allah ke cewa: “Kuma muka sanya baccinku hutawa…”  Wannan ma kari ne kan sauran ayoyin da ke bayanin ni’ima da ke cikin bacci da Allah ya samar wa dan adam.

Wadannan su ne wurare tara da Allah ya ambaci bacci da suna daya a larabce, wato: “An-Nawm.”  Wannan kalma, inji malamai, na magana ne a kan bacci a sake, ba tare da wani kaidi ba.  Amma dangane da abin da ya shafi nau’ukan bacci kuma, suka ce su ma Allah bai barsu ba sai da ya ambace su a cikin Kur’ani.

Nau’ukan Bacci a Kur’ani

A baya mai karatu ya ji cewa akwai nau’ukan bacci guda biyar, wadanda aka samo su daga kalolin bacci guda biyu, wato bacci mai nauyi da bacci madaidaici.  Wadannan nau’ukan bacci ba haka kawai masana kimiyya suka tashi suka ambace su ba, sai da suka kwashe shekara da shekaru, da karni da karnoni suna bincike, cikin wahala da nishadi, cikin sanyi da zafi, kafin suka gano su.  To amma duk da wannan dawainiya da suka yi, tuni Allah ya ambaci wadannan nau’ukan bacci. Sai dai da yake galibin masu wannan bincike ba musulmi bane, ba lallai bane hankalinsu ya zo kan wadannan ayoyi. Kuma ko da hankalinsu ya zo kan ayoyin ma, ka’ida ce irin ta malaman kimiyya, cewa abu kaza ne, bai sa su yarda, sai sun gudanar da bincike. To, a ina Allah ya ambaci wadannan nau’ukan bacci guda biyar?

Wuri na farko da Allah ya ambaci nau’in bacci na farko na cikin Suratul Baqara dai har wa yau, cikin Ayatul Kursiyyu, wato aya ta 255 kenan, inda Allah ke cewa: “…gyangyadi ba ya kamashi balle bacci…”  Malaman kimiyyar dabi’ar dan adam suka ce a nan an ambaci gyagyadi da kalmar “Sinah,” don shi ne mafi karancin nau’i ko matakin bacci.  Wannan matakin farko kenan cikin nau’ukan bacci mai nauyi, idan masu karatu basu mance ba.  Sai wuri na biyu, inda aka ambaci mataki na gaba, wato gyangyadi mai dan zurfi.  Wannan na cikin Suratu Aal Imraan aya ta 154, inda Allah ke cewa: “…sannan (Allah) Ya saukar a kanku bayan bakin ciki, wata aminci (a halin) gyangyadi da ke lullube wani bangare daga cikinku…”  A nan Allah ya yi amfani da kalmar “Nu’ass” ne, wadda aka samo asalinta daga kalmar “An-Na’ass.”  Wannan aya na ishara ga abin da ya faru ne lokacin Yakin Uhudu, sadda wasu daga cikin Sahabbai (Allah kara musu yarda) suka gudu suka haura saman tsaunin Uhudu, amma a karshe Allah Ya dora musu wata ‘yar gyangyadi, don samun nishadi da kuzari.  Haka ma a cikin Suratul Anfaal aya ta 11 Allah Ya sake sanar damu yadda ya saukar da gyangyadi makamancin wannan ga Sahabbai sadda aka zo Badar, kafin a fara gwabzawa.  A nan Malaman kimiyya suka ce wannan gyangyadi ta taimaka wa Sahabbai ne wajen rage gajiya, da kuma samun natsuwa.  Shi yasa ma suke cewa duk wanda ke yin baccin rana (kailula) na tsawon minti 10 a kalla, kowace rana, to zai samu kuzari, da kuma kaifin basira, sannan yana taimakawa wajen rage hauhawan jini (High Blood Pressure).  Wadannan nau’ukan gyangyadi guda biyu su ne matakan bacci mai nauyi na daya da na biyu, kamar yadda bayanai suka gabata a baya.

Sai wuri na uku da ke cikin Suratul Kahfi aya ta 18, inda Allah ke cewa: “Kuma kana zaton suna farke, amma bacci suke yi…”  Wannan daya ne daga cikin ayoyin da ke bayanin yanayin da Samarin kogo suka shiga, tsawon shekaru 300 ko sama da haka. Kalmar da Allah yayi amfani da ita itace: “Ruqood” wacce aka samo asalinta daga kalmar “Ar-Raqdu,” wadda ke nufin bacci mai tsawo. Kamar yadda masu karatu suka sani, wadannan samari sun yi shekaru 300 ne da ‘yan kai suna bacci, don haka aka yi amfani da kalmar “Ar-Ruqood,” wadda ke ishara ga bacci mai tsawo.  Sai wuri na hudu da ke cikin Suratuz Zaariyaat, aya ta 17, inda Allah ke cewa: “(Mumminai) Sun kasance kadan cikin dare suke bacci…”  A wannan aya Allah ya yi amfani ne da kalmar “Al-Hujoo’”, wadda ke nufin “Baccin dare.”  Wannan na daya daga cikin matakan bacci biyar da bayaninsu ya gabata.

Wuri na karshe na cikin Suratun Naba’i, aya ta 9, inda Allah ke cewa: “Kuma muka sanya baccinku hutawa.”  Haka ma a cikin Suratul Furqaan aya ta 47, ya yi ishara da cewa ya mayar da bacci ya zama hutawa ne.  Malamai suka ce a nan Allah ya nuna cewa ya mayar da bacci ya zama hutawa, ya kuma yi amfani da kalmar “Ja’ala,” wacce a ka’idar larabci idan tazo kafin kalma, ta kanyi aiki ne a kan sunaye biyu.  Idan haka ta kasance kuwa, to ana nufin sunan farko ne aka juya shi zuwa suna na biyu.  To me yasa Allah yayi amfani da kalmar “As-Subaat” da nufin bacci?  Farfesa Ahmad BaHammam yace saboda kalmar “Subaat” asalinta daga kalmar “As-Sabt” ne, wadda ke nufin “Yankewa daga wani abu.”  Yace a nan ana ishara ne zuwa ga nau’in bacci mai zurfin gaske ne, wanda ke yanke zatin dan adam daga harkokin duniya gaba daya, wanda kuma hakan ne ke haddasa masa samuwar hutu, kafin lokacin farkawarsa tayi.

Daga bayanan da suka gabata, mai karatu zai ci karo da kalmomi guda biyar masu ishara zuwa ga nau’ukan bacci biyar.  Wadannan kalmomi kuwa su ne: “Sinah,” da kalmar “Nu’ass,” da kalmar “Ruqood,” da kalmar “Hujoo’,” sai kuma kalma ta karshe, wato “Subaat.”  Farfesa Ahmad BaHammaam yace wadannan su ne nau’ukan bacci biyar da malaman kimiyya suka tabbatar a bincikensu.  Ya ce mai bacci na farowa ne daga matakin “Sinah,” ya shiga matakin “Nu’ass,” ya kai matakin “Hujoo’,” daga nan sai ya haura matakin “Ruqood,” kafin ya tike a mataki na karshe, wato “Subaat” kenan.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.