Binciken Malaman Kimiyya Kan Tsibirin Bamuda (1)

Daga cikin wurare masu hadari a duniya akwai tsibirin Bamuda, wanda aka fi sani da suna: “Bermuda Triangule.” Daga wannan mako zuwa makonni biyu nan gaba, za mu gudanar da bincike na musamman kan wannan tsibiri, da irin abubuwan dake faruwa a cikinsa na mamaki da al’ajabi. Wannan shi ne kashi na daya. A sha karatu lafiya.

415

Maimaici Mai Fa’ida

Assalaamu alaikum Baban Sadik, da fatan alheri a gare ka.  Don Allah idan zai yiwu ka maimaita mana kasidar “Tsibirin Bamuda” mana.  Lokacin da na fara karanta jaridar AMINIYA ka riga ka gabatar da kasidar, kuma ni ba ni da adireshin Imel balle ince a turo mini.  Kuma na lura lallai babu kasidar da ta kai wannan kasida ta Tsibirin Bamuda farin jini.  Da fatan za ka taimaka idan babu damuwa.  Allah ya kara basira, amin.  –  Ummu Haidar, Gombe

Wa alaikumus salam, Maman Haidar barka da warhaka. Lallai kamar yadda kika fada, wannan kasida mai take: “Binciken Malaman Kimiyya kan Tsibirin Bamuda (Bermuda Triangle),” ta shahara sosai, nesa ba kusa ba.  Ni kaina ban san sau nawa na aika wa masu karatu ba, a bisa bukatarsu.  Kasida ce da na rubuta tun shekarar 2007; shekaru kusan bakwai kenan a halin yanzu. Amma ko cikin makon da ya gabata akwai wadanda suka bukaci in tura musu, kuma na tura.  Sannan akwai masu karatu irinki, marasa adireshi ko akwatin Imel, kuma masu sha’awar ace sun kara karanta wannan kasida a karo na biyu ko ma farko.  Ganin sakonki ne ya kara mini kaimi wajen kara yin nazari kan kasidar, da gyatta wasu kalmomi don kara musu amo da tsari a ka’idojin rubutu, duk da cewa babu wani abu sabo da ya sake aukuwa na mamaki a wannan tsibiri tsakanin bayyanar kasidar a karon farko zuwa yanzu.  Da fatan wadanda basu samu karanta kasidar ba a karon farko za su amfana. Allah sa mu dace, amin.

………………………………………

 Mabudin Kunnuwa

Duk da cewa akwai bigirorin duniya da dama da abubuwan mamaki ke faruwa a cikinsu ba tare da dan adam ya fahimci musabbabansu ba, Tsibirin Bamuda (Bermuda Island ko Bermuda Triangle) ne kadai yafi shahara a bakunan mutane sanadiyyar haka.  Wannan shahara ta samo asali ne daga nahiyar Kudancin Amurka (South America), a hankali labarin yaci gaba da yaduwa zuwa sauran kasashen duniya.   Manyan ababen mamakin da ake ikirarin suna faruwa a muhallin tekun da wannan tsibiri yake sun hada da bacewar jiragen sama – masu dauke da fasinjoji ‘yan kasuwa ko na soji – da jiragen ruwa – manya da kanana da na shawagi.  Idan suka bace a galibin lokuta, ba a ganin buraguzan jirgin balle a kaddamar da bincike kan dalilan da suka haddasa faruwar hadarin.  Wannan al’amari abin al’ajabi, a cewar masu bayar da labarai, bai tsaya a bacewar jirage ba tare da ganin buraguzansu kadai ba, har da wasu labarai masu caza kwakwalwa kan irin yanayin da tekun ke kasancewa na launi da kuma sulmuya a wasu lokutan, ko kuma wasu irin dabi’u da ake ikirarin gira-gizan da ke saman tekun ke shiga, a yayin aukuwar hadarurrukan da suka fara faruwa shekaru kusan dari biyu da suka gabata.  Ire-iren wadannan labarai sun samo asali ne daga irin jawaban da masu lura da na’urar filin saukan jiragen sama da ke tsibirin ke bayarwa. Ko wadanda ake tarawa wajen binciken da hukumomin gwamnatin Amurka da ke lura da ire-iren wadannan hadarurruka ke yi.  Da wannan, marubuta suka sa wa wannan muhalli suna: The Bermuda Triangle (Kusurwar Bamuda), ko kuma The Devil’s Triangle (Kusurwar Shedan).

A halin yanzu da dama cikin wadanda suka taba jin labarin wannan bigire na Bamuda, sun yarda cewa wani wuri ne mai cike da almara, kamar yadda galibin turawa masu bincike suka fada.  Da kuma cewa babu wanda ya san abin da ke haddasa wannan al’amari, sai Allah (ga wadanda suka yarda da Allah kenan), ko kuma dabi’a ta shu’umcin wurin.  Wasu suka ce aljanu ne a wurin.  Wasu suka ce akwai wasu halittu ne na musamman da a harshen Turanci ake kira Aliens, masu haddasa hakan.  Wasu suka ce a a, irin yanayin wurin ne kawai. Da dai sauran ra’ayoyi masu kama da haka.  Shin, meye gaskiyar wadannan zace-zace da ake ta yi kan wannan tsibiri?  Wani irin bincike aka yi wajen gano hakan?  Jiragen ruwa da na sama guda nawa suka bace a wannan mahalli? Rayuka nawa suka salwanta?  Wa da wa suka yi rubuce-rubuce kan haka cikin Malam Kimiyya da masu sha’awar rubutu kan al’amuran mamaki a duniya?  Meye ra’ayin nazarin da Malaman Kimiyya suka yi kan dalilin faruwar wadannan ababen mamaki?  Shin, wai ma tukun, a duniya akwai wasu wurare ne masu irin wannan dabi’a, ko dai tsibirin Bamuda ne kadai?  In eh akwai, to me yasa na tsibirin Bamuda ya sha bamban, ya shahara fiye da sauran a duniya?  Wadannan, da ma wasu tambayoyi, zamu samu amsoshinsu cikin makonni masu zuwa in Allah Ya yarda.

A Ina Tsibirin Yake?

- Adv -

Kafin mu yi nisa, asalin tsibirin Bamuda, watau Bermuda Islands, yana gab da tsakiyar tekun Atlantika ne, Arewa da Jihar Fulorida da ke kasar Amurka.  Kuma duk da cewa ana danganta wannan wuri ko kusurwa da tsibirin Bamuda, sai dai ba a wannan tsibiri kadai wannan kusurwa yake ba.  Kusurwar Bamuda wani wuri ne da ya hada manyan gabar tekunan kasashe guda uku da ke nahiyar Arewaci da kuma kudancin Amurka.  Kusurwar farko ta faro ne daga gabar Fulorida ta kasar Amurka, ta zarce zuwa gabar  babban tsibirin Puerto Rico da ke yamma maso-kudu da gabar Fulorida.  Daga tsibirin Puerto Rico kuma kusurwar ta cilla Arewa, inda ta tike a gabar tsibirin Bamuda da ke kusa da tsakiyar tekun Atlantika.  Wannan wuri ko mahalllin teku da ke tsakanin wadannan gabobi guda uku, shi ake kira The Bermuda Triangle, ko The Devil’s Triangle. 

An danganta wannan kusurwa da tsibirin Bamuda ne saboda a nan ya tike, kuma galibin ababen hawa kamar su jiragen sama da na ruwa wadanda ake amfani da su wajen  kasuwanci da shawagi da atisayen soji a wannan nahiya, duk a can suke tikewa kafin su komo inda suka taso.  Ko kuma daga can suke wucewa zuwa wasu nahiyoyin, irin su Turai da Arewacin Amurka da kasashen Asiya.

Wannan kusurwa ta Bamuda ita ce bigiren da jiragen sama da na ruwa ke shawagi fiye da kowane wuri a duniya.  An kiyasta cewa a kalla akan samu sawun jiragen sama daga wannan nahiya zuwa kasashen turai da sauran nahiyoyi, sama da dubu hamsin a shekara.  Bayan haka, akwai jiragen ruwa da na kasuwanci da na shawagi ko yawon bude ido, da kuma jiragen saman atisayen soji da Hukumar Sojin Amurka ke turawa suna shawagi, watau kai-komo don yin atisaye. Har wa yau akwai masu shawagi da kananan kwale-kwalen shakatawa wadanda a harshen turanci ake kira Pleasure Boats, da  kuma jiragen ruwan tsere da ake kira Yatchers.  Bayan haka, akwai filayen saukan jiragen sama a dukkan kusurwoyin nan uku, tare da tashar jiragen ruwa masu karban manya da kananan jiragen da ke shawagi a wannan wuri.  Sannan kuma sai miliyoyin masu zuwa yawon bude ido daga sauran kasashen duniya, musamman ma Amurka da Turai.  A takaice dai, wannan wuri rayayyen wuri ne da sawun jirgin ruwa da na sama da na masu ziyara ba su daukewa; daga shekara zuwa shekara.

Zai dace mai karatu ya rike wannan karatu kan yawan zirga-zirgar da ake yi a wannan wuri, domin zai taimaka masa wajen karba ko rashin karbar dalilan da wasu marubuta suka bayar wajen yanke hukuncinsu na karshe.

Yaushe Abin Ya Fara?

Wannan kusurwa da ake wa take da “Kusurwar Shedan” – ko Devil’s Triangle – ya fara cin jiragen sama da na ruwa ne shekaru kusan dari biyu da suka gabata, duk da cewa ba a fara fahimtar hakan ba sai wajen shekaru casa’in zuwa dari da suka wuce.  Daga nan ne aka fara danganta hadarurrukan da suka gabata da wannan yanayi mai ban mamaki.  Kamar yadda bayanai suka gabata, wannan kusurwa ta Bamuda ta yi kaurin suna ne wajen hadararruka masu ban mamaki, inda bayan hadarin ake rasa abin da ya haddasa shi, ko kuma a ma kasa samun buraguzai ko gawawwakin wadanda suka rasa rayukansu da ma na jirgin gaba daya.

A wasu lokuta a kan samu sakon neman agaji daga direbobin jiragen sama cewa suna ganin wasu abubuwa masu ban tsoro ko firgitarwa.  Kafin a mayar da jawabin ceto garesu, sai kawai a nemi hanyar sadarwa a rasa.  Wani kuma zai bugo ne cewa ba ya ganin gabansa, bayan kuma a na’urar lura da yanayin sararin samaniya babu wata matsala da na’urar ke hangowa: babu yanayin hazo mai firgitarwa, babu ruwan sama, babu alamar mahaukaciyar guguwa mai yi wa jiragen ruwa dibar karar mahaukaciya, amma sai kawai a ji hanyar sadarwar ta yanke.

Mafi shahara daga cikin abubuwan mamaki da suka faru a wannan kusurwa shi ne hadarin tawagan jiragen kai hari da darkake abokan gaba na kasar Amurka masu suna Flight 19, wadanda hukumar sojin sama na kasar Amurka ta aika don yin shawagi a wannan kusurwa  cikin shekarar 1945.  Duk da cewa ana lura da tafiyar wannan tawaga na jirage ta hanyar na’ura hangen nesa sadda suka baro cikin kasar Amurka, sai dai cikin lokaci guda kawai sai aka neme su aka rasa.  Da aka nemi sadarwa da shugaban tawagar, sai yace: “A yanzu muna shiga wani irin farin ruwa ne…al’amura sun fara lalacewa.  Bamu san inda muke ba a halin yanzu…ruwan kore ne…a a, fari ne!”, sai sadarwa ta yanke a tsakanin masu lura da na’urar da wannan shugaban tawaga.

Bayan faruwar wannan lamari, an yi ta bincike cikin teku ba a samu buraguzan wadannan jirage ba balle wadanda suke ciki.  Babu wanda ke da wani bayani gamsasshe kan abin da ya haddasa wannan hadari har zuwa yau, balle bayani kan hakikanin wurin da abin ya auku.  A lokacin da aka tura wata tawaga ta manema jirage, da suka isa wurin da na’urar ta sanar da faduwarsu, babu abin da aka gani a wurin.  Daga nan aka ci gaba da samun ire-iren wadannan hadarurruka masu ban mamaki da al’ajabi.  Wasu a kan samu bayanai kan batansu, bayan tsawon lokaci; wasu kuma ko alama ba a samu, sai dai kawai a hakura.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Rabiu mu'azu wurjiwo says

    Muna godiya da jin dadin wannan kokari naka Allah yasaka maka da alkhairi

Leave A Reply

Your email address will not be published.