Ciyar da Najeriya Gaba a Fannin Kimiyya da Kere-Kere (2)

A wannan makon ma mun ci gaba da yin mukaddima ne kan wannan maudu’i mai matukar mahimmanci, inda muka gwama ci gaban kasarmu da na sauran kasashen dake makwabtaka damu. A sha karatu lafiya.

155

Hakika ina sane da yadda galibin ‘yan Nijeriya suke yanke kauna a kullum dangane da yiwuwar ci gaba a wannan kasa tamu ta kowane bangare.  Sai dai abin da nake gaya  mana shi ne, kowace kasa da irin tafarki da kuma tsarin ci gabanta.  Kamar mutane ne; tsarin jikinmu ba daya bane.  Don haka yanayin girmanmu da ci gabanmu ba zai taba zama daya ba.  Ana iya haifan jarirai guda biyu a rana daya, a lokaci daya, amma daya ya riga daya girma, ya riga shi yin arziki, ya kuma riga shi mutuwa in ta kama.  To haka kasashe suke.

Tarihinmu ya sha bamban da na sauran kasashen da suka ci gaba, hatta wadanda suke makwabtaka da mu a Nahiyar Afirka.  Duk wanda ya je kasar Gana a misali, sai ya sha mamakin ganin yadda suke da tsari, suke girmama dan Nijeriya, kudinsu na da daraja, al’ummarsu na bin doka sau da kafa, jami’o’insu na da inganci fiye da namu, suna da kima a idon kasashen duniya fiye da mu, bayan haka, suna da wutar lantarki mai inganci, kuma Hukuma na girmama talakawanta, kamar yadda su ma suke girmama doka da oda iya gwargwado, da dai sauransu.  Idan aka koma bangaren kimiyya da kere-kere ma, suna da kokari matuka, sannan Allah ya hore musu karfin zuciya da hazaka wajen sake-sake da kokarin sarrafa albarkatun kasa da Allah ya hore musu, duk da cewa kasarmu ta fi kasar Gana dukiya nesa ba kusa ba.  A takaice dai, bunkasar Nijeriya da ci gabanta abu ne mai yiwuwa; ba dole bane ya zama yanzu-yanzu, domin gyara na daukan lokaci.  Barna ce ake iya yinta cikin kankanin lokaci.

A cikin kasidun da ke tafe, za mu kawo bayanai ne kan tarihin ci gaban wannan kasa a fannin kimiyya da kere tun kafin samun ‘yancin siyasa a shekarar 1960.  Sannan mu dubi halin da muke ciki yanzu; shin gaba muka ci ko baya?  Idan baya muka ci (wanda shi ne galibin tunaninmu) to me ya haddasa hakan?  Sannan a karshe za mu kawo jerin shawarwari daga bakin kwararrun masana kuma ‘yan Nijeriya, wadanda suka kware a fannin kimiyya da kere-kere; irin shawarwarin da muddin aka dabbaka su, to kasar nan za ta ci gaba in Allah Ya yarda.  Amma kafin nan, ya kamata mu dubi dukiyar da Allah Ya hore mana na albarkatun kasa, sannan mu dora kasarmu kan wasu ka’idoji guda shida da masana harkar kimiyya da kere-kere a duniya suka yarda cewa sai kasa ko al’umma ko daula ta cika su sannan za a iya cewa ta ci gaba a wannan fanni.

Muna Da Arziki

Alal hakika duk wani dan Najeriya da ya san ciwon kanshi ya san cewa wannan kasa Allah ya hore mata tarin albarkatun kasa da na sararin samaniya.  Ba wai tsabar kudade da muke samu daga cinikin danyen mai nake nufi ba; tsantsar arzikin kasa nake nufi. Bayan tarin albarkatu irinsu azurfa da zinare da tagulla da da nau’ukan karafa da Allah ya tara mana a karkashin wannan kasa tamu, ita kanta kasar da muke takawa a makare take da albarka irin ta noma.  Kada mu mance, shekaru kusan sittin da suka gabata, lokacin da kasar Malesiya ta zo da kokon baranta neman irin shuka na kwakwar manja, bayan mun bata ta tafi da shi kasarta, ta shuka, wannan iri bai yi kai ba.  Saboda yanayin kasarsu bai da sinadaran da wannan itaciya ke bukata.  Sai da suka dawo Najeriya, suka debi kasarmu cikin jirgin ruwa, suka tafi da shi.  A can ne suka gudanar da bincike mai kyau kan irin sinadaran da wannan kasa tamu ke dauke da su, sannan suka cakuda wannan kasar da suka debo daga Najeriya da nasu kasar, sannan suka fitar da wani irin kasa na musamman da zai iya baiwa wannan itaciya ta kwakwar manja sinadaran da take bukata don yin yabanya da yado.

- Adv -

A yanzu duk duniya babu kasar da ta kai kasar Malesiya arzikin kwakwar manja.  Daga tuwon siddin mota har zuwa tsantsar manjar miya, wannan kasa na sarrafawa – domin babu abin da wannan kasa ke watsarwa daga kwakwar manja.  Idan har sai da kasar Malesiya ta wahala wajen tarbiyyantar da kasarta kafin kasar ta iya daukan wannan shuka, me za a ce ga kasarmu?  Yanzu idan ka je Kudu, za ka samu gonakin kwakwar manja sun zama saura.  Babu ruwan gwamnati da abin da ya shafi wannan sina’a.  Idan mai gonar ya ga dama ya noma, ko kuma ya mayar da itaciyar zuwa tulun banmi, ya rika tatsa yana sha; ba ruwanta.

Dangane da abin da ya shafi yanayi kuma, wato Weather, Allah ya mana arziki har babu iyaka.  Bayan sinadaran hasken rana da muka kasa sarrafa shi (sai dai mu shanya kayayyakinmu da abincinmu kawai), wani ma’aikacinmu ya sanar da ni cewa ya je ziyara kasar Amurka inda ya hadu da wani masanin yanayi, kwararre.  Bayan sun tattauna, sai baturen ke tambayarsa daga wace kasa ya fito, ya ce shi dan Najeriya ne.  Sai baturen yace masa, ai ya dade yana burin ya zo wannan kasa tamu, domin ya dade yana bincike (na karatu tsantsa) dangane da yanayin kasar.  A karshe sai ya sanar da wannan aboki nawa cewa, duk wani yanayi na muhalli da ake da shi a sauran kasashen duniya, to, akwai irin shi a Najeriya.

Kada mu mance cewa, a kasar nan ne kadai za ka iya shuka itaciyar tuffa (Apple) har ta fitar da ‘ya’ya sama da daya a kowane zangarniya.  A sauran kasashe kwaya daya-daya take fitarwa.  Wannan ke nuna tsabar albarkar da ke wannan kasa.  Wani babban malamin musulunci ya bamu wani labari mai ban dariya da takaici, shekaru kusan shida da suka wuce, inda ya ce wani dan kasar Sin (Chinese) ya kama hanya zuwa kasar Abiya (Abia State) da ke Kudu maso gabashin kasar nan.  Yana cikin wata tawaga ce ta ‘yan Najeriya, suna tafiya a cikin mota.  Da suka fara shiga kurmi, sai wannan mutumin ya fara mamakin irin yadda Najeriya “ke noma” babu kakkautawa.  Sai daya daga cikin ‘yan Najeriya da ke tawagar ya tambaye shi, me ya gani?  Sai yace ai ya ga ko ina ya duba, sai ya ga shuki ne zalla; gaba daya kasa ta zama koriya!  Bai san duk tarin ciyayi bane, wadanda ruwan sama ya tsirar da su.  Daga nan sai aka sanar da shi cewa ai duk wannan tarin ciyayin Allah ne da yake ciyar da dabbobi da su, ba wai shuka su aka yi ba.  Sai mamaki da bakin ciki ya kama shi nan take.  Ya ce a kasarsu sai sun tarbiyyantar da kasa, sun cakuda ta da wasu dabarun kimiyya sannan take musu yadda suke so.  Tare da haka, kasar Sin na cikin kasashe masu ciyar da duniya a bangaren noma.  Labarai makamantan wannan ba za su kare ba.

Abin da nake son kara tabbatar mana shi ne, muna da arzikin da zai iya juya wannan kasa tamu ta shallake kowace kasa ne wajen ci gaba a kowane fanni a duniya.  To amma kaico, kamar yadda larabawa ke cewa: ga rakumi dauke da tulun ruwa a cikin sahara, kishirwa na gab da kashe shi, saboda bai samu wanda zai sauke masa wannan ruwa ba balle ya kwankwada. Bayan wadannan bayanai takaitattu da muka koro kan albarkatun kasarmu, shin, a wani matsayi muke yanzu?

(Za mu ci gaba)

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.