Ciyar Da Najeriya Gaba a Fannin Kimiyya da Kere-Kere (5)

Wannan shi ne kashi na karshe, kuma mun dubi hanyoyin da za su kawo mana ci gaba ne a wannan fanni. Da fatan masu karatu sun amfana da abin da aka bijiro dasu musamman na bangaren dalilan rashin ci gaba, da kuma hanyoyin gyara.

413

Hanyoyin Ci Gaba

Hanyoyin ci gaba a fannin kimiyya da fasahar kere-kere ga kowace kasa ce, a fili suke, musamman a wannan zamani da ke cike da hanyoyin mallakar ilmi masu yawa kuma cikin sauki.  Duk da cewa ba wai hanyoyin bane muka jahilta, a a, sadaukar da kai ne kawai muka rasa da kishin kai.  Amma duk da haka, kogi ba zai ki dadi ba. Don haka a yau muka gabatar da wasu cikin shawarwarin da  muke kyautata zaton za a kai ga gaci muddin aka dabbaka su.  Wannan shi ne bangaren karshe na wannan doguwar kasida da muka faro cikin makonni biyar da suka gabata.  Ga wasu daga cikin hanyoyin nan:

Nazarin Kerarrun Fasahohi Daga Waje

Akwai kayayyakin kere-kere da hanyoyin ci gaba a fannin kimiyya da suka shigo mana har muke amfani da su.  Me zai hana gwamnati ta kafa cibiyoyi na musamman don yin nazari da “dubiya” kan tsari da kimtsin yadda aka kera wadannan kayayyaki?  Galibin kasashen da suka ci gaba basu mallaki kwarewar da suke takama da ita ba sai ta ire-iren wadannan hanyoyi.  Wannan zai taimaka mana a hanyoyi biyu; na farko shi ne za mu rika kera wadannan kayayyaki cikin sauki kuma a kasarmu, sannan kuma ‘yan kasa za su mallaki fasahar kera su ba tare da sai sun je asalin kasashen da aka kero su ba.  A wasu lokuta ma idan zuwa kasar ta kama, ana iya zuwa.  Ga motoci nan bila-adadin, ga kerarrun mashinan zamani, ga injinan kera abubuwa da yawa – daga na tatse lemun tsami, da gyada, da na markade da dai sauransu – duk muna iya bibiyar asalin fasahar da aka yi amfani da ita wajen kera su.  Wannan ba ya nufin a yanzu ba mu da wannan fasaha ko hanyar kere-kere, muna da fasahar.  Amma babu tsari, sannan hatta hukuma bata ma san mutum nawa ne ke da kuduri wajen yin hakan a kowane fanni ba, balle har a amfana da fasaharsu.  Idan har aka kafa cibiyoyin da za su rika lura da ire-iren wadannan ayyuka, to za a samu fa’ida mai dimbin yawa.

“Satar Fasaha” (Industrial Espionage)

A fannin ilmin ci gaban kasuwanci da kere-kere, “Satar Fasaha”, wanda a turance ake kira “Industrial Espionage”, shi ne leken asiri kan asalin ilmin fasahar yadda ake kera wasu kayayyaki – kamar injina, da mashina, da motoci, da sauran hajojin kasuwanci – ta hanyar karkashin kasa.  Wannan hanya, duk da cewa a zahiri haramtacciyar hanya ce, amma a aikace babu wani kamfani ko kasa da ta tsira daga aikata shi a duniya baki daya.  Da wannan tsari ne galibin kamfanoni ke amfani wajen satar fasahar yadda wasu kamfanonin ke kera hajojinsu.  A aikace dai, a iya cewa wannan tsari ne halastacce; domin duk kasa ko kamfanin da ya ce haram ne, to za ka samu shi ma ya taba aikata shi a baya.  Da wannan tsari, muna iya mallakar hanyoyin ci gaba mai dimbin yawa.  Hakan kuwa na samuwa ne ta hanyar bincike a Intanet, da littattafai, da nemo bayanai ta karkashin kasa daga ma’aikatan wasu kasashe ko kamfanin da ke kera irin fasahar da ake bukatar habbakawa.  Duk wannan, idan za mu yi da gaske, ba wani bane mai wahal ko kadan.  Sadaukar da kai kadai muke bukata da kishin kasa.

Samar da Yanayin Karatu Mai Kyau a Makarantu

A tabbace yake cewa ilmi ba ya samuwa ta sauki, amma hakan ba ya nufin a yi ta yinshi ne cikin wahala da kunci.  Akwai irin yanayin da karatu ke bukata kafin ya tabbata a zuciya ko kwakwaklwar wanda ke daukansa.  Idan ba a samu wannan yanayi ba, to babu yadda za a yi ya zauna, balle har a iya amfana da shi. Hakan ya hada da samar da malamai masu nagarta, da samar da tarbiyya ta hanyar lura da doka da oda a ko ina ne cikin kasa, da samar da kayan daukan darasi da karatu masu inganci, irin su littattafai, da azuzuwa masu dauke da wutar lantarki, da ruwan sha, da dakunan dalibai masu inganci, da kayayyakin binciken ilmi masu inganci, da kuma saukaka farashin karatu, ba mu ce dole sai an baiwa ‘yan kasa ilmi kyauta ba – tunda gwamnati ta dade tana kururuwar cewa bata da kudi.  A gaskiya galibin makarantunmu ba a cikin yanayi mai kyau suke ba.

Bayan rashin tarbiyya, wanda ke dakushe karshashi da kaifin basira da ilmi, akwai matsalar rashin muhallin karatu mai kyau.  Maimakon karatu ya amfani dalibai, sai cutar da su ma yake yi.  Abin da nake nufi da cutar da su kuwa shi ne, maimakon a samu sauki lokacin karatu, tsanani ake samu, ko dai daga wajen malaman ko kuma sauran dalibai ‘yan uwansu.  Bayan haka, galibin tsarin karatarwa a makarantunmu sun koma da baki kawai ake yi kamar karatun Aku (theoretical), babu bangaren kwatance (practical), in ka kebe wasu daga cikin fannonin ilmi da suka shafi likitanci da bangaren lafiya.  Dangane da haka, ga abin da Farfesa Otubanso, wani kwararren farfesa a fannin kimiyyar sinadarai (Chemistry), yake cewa:

“…a yanzu dalibai sun daina koyon karatu a aikace (saboda rashin  kayan aiki a makarantu), sai dai a rubuce kadai.”

Da wannan tsari kuwa, babu yadda za a yi a ce makarantunmu sun yaye dalibai kwararru kan harkar kere-kere.  In kuwa haka ta kasance, ban san inda muka dosa ba, duk kudi da dogayen gidajenmu.  Wannan ya tuna min da zancen Martin Luther King, inda yake cewa: “Ci gaban kowace kasa bai tsaya a yawan dukiyar da ta mallaka ba, ko yawan kudaden shiganta ba, ko tsauraran ganuwar tsaronta ba, ko kuma dogayen gine-gine da ta mallaka masu ban sha’awa ba, a a, ya ta’allaka ne da iya adadin kwararrun da ta mallaka, masu ilmi, wayayyu, kuma mutanen kwarai.”  Ya kamata mu sake lale.

- Adv -

Tallafi Ga Cibiyoyin Bincike Ilmi

Cibiyoyin bincike su ne kashin bayan ci gaban kowace kasa wajen kimiyya da kere-kere.  Daga kasar Amurka zuwa Ingila, da Sin, da Malesiya, da Singafo, har zuwa kasar Indiya da Jafan, duk da cibiyoyin binciken ilmi suke takama.  A wasu kasashe ma ba wai gwamnati kadai ke mallakar cibiyoyin ilmi ba, hatta kamfanonin kere-kere na da su.  Tabbas tafiyar da cibiyar binciken ilmi abu ne mai wahala, domin yana bukatar makudan kudi da kwarewa da kuma tallafin wasu kasashe, amma duk da haka, wannan ba ya nufin ba za mu iya ba, tunda ga kasashe masu yawa, wadanda ma ake ganin ba kowa bane su, sun rike ire-iren wadannan cibiyoyi.  Muna da cibiyoyin binciken ilmi, tsakanin fannin hada magungunan cututtukan jikin dan adam zuwa na dabbobi, har zuwa na binciken kananan kwari, amma idan ka shiga cikinsu sai ka tausaya musu.  Cikin farko-farkon wannan shekara ne ministan Kimiyya da Fasahar Kere-kere yayi ta kira ga gwamnatin tarayya wajen samar da wani tsari da zai tabbatar da tallafi ga cibiyoyin binciken ilmi a kasar nan, amma har yanzu shiru kake ji, wai Malam ya ci shirwa.  Galibinsu da kyar suke dogaro da kansu.  Kudaden da ake tura musu na biyan albashi ne kadai, ba wai na gudanar da binciken ilmi ba.  Akwai hukumomi da yawa a sauran kasashen duniya da ke bayar da tallafi a fannonin binciken ilmi da yawa, wajibi ne ga gwamnatin tarayya ko na jihohi su samar da wani tsari da zai tabbatar da yiwuwar hakan, don ciyar  kasarmu gaba.

Bayan haka, dole ne gwamnatin tarayya da na jihohi har wa yau, su rika ware wasu kudade na musamman a matsayin tallafi don gudanar da binciken ilmi a wasu fannonin da muke da nakasu a cikinsu.  Alkaluman bayanai daga wasu kasashen za su tabbatar da cewa tallafin da gwamnatin tarayya ke bayarwa a wannan fanni, in ma tana bayarwa, ba komai bane idan ka gwama shi da na wasu kasashe.  Misali, mujallar The Nigerian Engineer, bugu na 35, lamba ta 4, wacce ta fito cikin Disamba na shekarar 2003, ta tabbatar da cewa a shekarar 1985, kasar Indiya ta ciyar da dalar Amurka biliyan uku wajen tallafi ga wasu cibiyoyin binciken ilimi guda dubu daya da dari uku da ta mallaka.  Mujallar kuma ta kara da cewa a duk shekara, hukumar Indiya na ciyar da kashi 1.5% na arzikin da take samu daga sauran kasashe don habbaka fannonin kimiyyar lantarki da bincike kan sararin samaniya, a yayin da kasar Amurka take ciyar da kashi 2.5% a wannan fanni ita ma.  Amma tunda aka samar da Najeriya, a cewar wannan mujalla, mafi girman abin da ta bayar a matsayin tallafi a bangaren binciken ilmi bai wuce kashi 0.43% ba.  Misali, a shekarar 1983 ta bayar da kashi 0.43%, a shekarar 1992 ta bayar da kashi 0.05%, a shekarar 2003 kuma ta dan haura zuwa kashi 0.23%.  In har wannan shi ne abin da gwamnatin tarayya ke ciyarwa, duk da kudaden shiga da muke samu daga danyen mai da kudin fito, a fili yake cewa babu wata kima da hukumar tarayya ta baiwa wadannan cibiyoyin bincike a aikace, balle a yi maganar manufar gwamnati wajen habbaka kimiyya da kere-kere a kasar baki daya.

Samar da Makamashi na Hakika

Gwamnatin tarayya ta dade tana ta bikon masu zuba jari a wannan kasa tamu a kowane fanni ne kuwa, musamman fannin kimiyyar sadarwa.  Lokacin da kamfanonin wayar salula irin su MTN da Econet (Zain) da Glomobile suka yanki lasisi kan wannan harka, babu irin wahalar da talakan Najeriya bai sha dasu ba, wajen yawan cajin kudin kira, da rashin yanayin sadarwa mai kyau, da kuma tsadar wayar salula.  Duk da cewa an samu saukin wasu daga cikin wadannan matsaloli, a bayyane yake cewa lallai farashin da muke biya wajen kiran waya yana daga cikin masu tsada a duniya.  Ba komai bane ya haddasa mana hakan sai tsadar rayuwa, wanda rashin makamashi na hakika ke jawo shi – daga kan kamfanoni ko masana’antu, zuwa kan talaka da ke sayan kayayyaki ko hajojin da suke fitarwa.  Ba mu da ingantacciyar wutar lantarki.  A kasar Gana har yanzu, sai an yi sanarwa a gidan rediyo ko talabijin idan za a dauke wuta a wata unguwa ko gari, tare da sanar da mutanen wannan bigire tsawon lokacin da hakan zai dauka, da ranar, da kuma lokacin.  Galibin lokuta, idan hukumar lantarki ta sanar cewa za a dauke wutan na tsawon mintina biyar ne, a karshe cikin mintina uku da daukewa, za ka ga an dawo da wutar.

Cikin watan da ya gabata ne daya daga cikin jihohin Najeriya da ke makwabtaka da kasar Kamaru ya fara tunanin jawo wutar lantarki daga kasar Kamaru zuwa jiharsa, don samun ingantacciyar wutar lantarki ga al’ummar jihar.  Kada mai karatu ya mance, har yanzu Najeriya ce ke baiwa kasar Kamaru, da Nijar da sauran makwatanta wutar lantarki.  Me yasa ba za  mu iya alkinta abin da muke da shi ba?  Akwai kamfanoni da yawa masu son zuwa Najeriya don zuba jari, amma babbar matsalar da suke dubawa bayan cin hanci da rashawa, ita ce matsalar wutar lantarki.  Domin ko ba a samar da hanyoyi ba, in dai akwai ingantacciyar wutar lantarki, hatta karamin ma’aikacin gwamnati na iya tsara rayuwarsa, duk karancin albashinsa kuwa.  Idan muka yi la’akari da kasashen da suka ci gaba a fannin kimiyya da kere-kere, za  mu ga basu samu wannan matsayi ba sai da suka yaki zuciyarsu wajen tabbatar da samuwar ingantacciyar wutar lantarki a kasarsu.  Wannan zai sa makarantu su samu ilmi mai inganci, sanadiyyar ingantacciyar karantarwa daga malamai.  Shi zai sa kamfanonin kere-kere su samu kwanciyar hankali, ya zama damuwarsu kan bincike ne kawai da abin da za a kera, amma ba a kan makamashi ba.  Wannan zai sa har wa yau, a samu karkon kayayyakin kere-kere da ake amfani da su.  Idan kuwa gwamnati ba ta yi haka ba, to da sauran rina a kaba.

Lura da Bukatun Kasa/Al’umma

Abu na kusa da karshe da hukuma za ta yi shi ne ta lura da bukatar ‘yan Najeriya.  Me ye muke da tsananin bukatuwa zuwa gare shi?  Kuma yaya za a tabbatar da samuwarsa?  Wannan shi ne abin da ya kamata  mu lura da shi, ba wai mu zama “’yan abi Yarima a sha kidi” ba – don kasar Amurka ta je duniyar wata, wannan ba shi zai sa mu ma dole mu je ba.  Don kasar Sin ta harba kumbo, ba shi zai sa mu ma dole mu harba ba.  Don kasar Indiya ta kera makamin Nukiliya, har wa yau, ba wannan bane zai zama mana dalili dole mu ma sai mun kera ba.  Don me?  Bukatunmu kadai ya kamata mu duba.  Idan muka  dubi kasa irin Malesiya misali, za mu ga cewa duk da ci gabanta, ba ta damu da kera makamin Nukiliya ba, balle har ta kama cuku-cukun zuwa duniyar wata.  Abin da kasar ta sadaukar da kanta wajen samarwa shi ne ingantaccen ilmi, da bunkasa fannin kere-kere da fasahar sadarwa, da kuma samarwa tare da tabbatar da doka da oda a kasarta.  Duk wanda ya ziyarci wannan kasa zai fahimci haka.

To amma ta yaya muka yanke shawarar harba tauraron dan adam, alhali ba mu da cikakken tsarin doka da oda, ba mu kawar da ci hanci da rashawa ba iya gwargwado, ba mu samar da ingantaccen ilmi ba, balle har mu tabbatar da samuwar ingantacciyar wutar lantarki?  Idan mun ce ai ba a Najeriya bane tauraron ke da asali, amma ai muna da cibiyar da ke lura da shawagi ko bayanan da yake tarkatowa daga sararin samaniya a nan kasar, wadda kuma dole ne sai da janareto take dogaro.  Anya, wannan ba tufka bane da warwara?

Shugabanci na Gari

Dukkan shawarwarin da muka kawo a sama, samuwarsu ta dogara ne kacokan kan shugabanci na gari; wani abu mai tsada da kasar nan ta rasa, tun shekaru kusan arba’in da suka gabata.  Da shugabanci na gari ne kadai gwamnatin tarayya za ta iya sadaukar da kanta wajen ganin wannan kasa ta gyaru, ta kimtsu, ta zama ‘yantacciya daga kangin talauci, da kaskanci, da cin hanci, da rashawa, da dukkan abin da yake mata tarnaki wajen ci gaba.  Don haka, dole ne mu tabbatar da cewa mun zabi shugabanni na gari.

Allah mana gamo da katar!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.