Dabarun ‘Yan Dandatsa (Hackers) da Hanyoyin Dakile Su (1)

Daga yau za mu fara gabatar da bincike na musamman kan hanyoyin da yan Dandatsa suke bi wajen satar bayanai a kwamfutoci, da kuma hanyoyin da za a iya bi wajen dakile yunkurinsu. A sha karatu lafiya.

407

Tambaya:

Assalamu alaikum Baban Sadik, fatan kana lafiya yaya iyali kuma ya kokari?
Ina neman shawara ne akan “Ethical Hacking.”  Ta yaya zan fara shi?  Kuma wasu dokoki suka kamata inbi?  Bugu da kari, meye anfaninta?  Me ake nufi da “Ethical Hacking” (White Hat).  Allah huta gajiya Baban Sadik.   Sako daga me binka Umar Faruk Lagos


A yau cikin dacewar Ubangiji ga mu dauke da tambayar Malam Umar Farouk daga birnin Legas.  Na zabi amsa wannan tambaya ne ta hanyar bincike mai zurfi saboda yawaitar masu tambaya kan wannan maudu’i, tun shekaru biyu da suka gabata.  Saboda yawaitan tambayoyin ma, tun ina tara tambayoyin har aka wayi gari na barar dasu cikin tsohuwar wayata.  Wannan tambaya ce mai mahimmanci, musamman ga daliban ilimi dake karatun kimiyyar sadarwa da kariyar bayanai kan na’urori da hanyoyin sadarwa.

Mai tambaya na so ne, kamar yadda mai karatu zai gani a sama, in bashi shawara kan yadda zai kware a fannin da ake kira: “Ethical Hacking.”  Da dokokin da wannan fanni ke dauke dasu, na shari’a.  Da kuma amfani (har ma da cutarwar da fannin ke dauke dashi).  Kafin wannan tambaya, akwai wanda ya rubuto a gurguje, cewa yana son in sanar dashi yadda zai iya aiwatar da “hacking” daga wayarsa ta Android.  Wannan bawan Allah ya kagara sosai, domin bayan ya aika mini sakon ta wayata, bai ji amsa sadda yake son ji ko gani ba, ya sake hawa kan Taskar Baban Sadik yaje ya ajiye sako a wurin.  Ina kan karantawa sai naga ya sake zuwa Taskar Baban Sadik dake Facebook (www.facebook.com/taskarbabansadik) ya sake ajiye tambaya ko bukatarsa.  Da yaji shiru ma, ya darkakoni a “Inbox”, a babban shafina dake Facebook (www.facebook.com/babansadik), ya ajiye mini sakon.  A wannan karon bai boye gajen hakurinsa ba.  Sai na bashi hakuri, na kuma masa alkawarin nan ba da dadewa ba in Allah Yaso zan fara jero kasidu kan wannan fanni.

Darussan “Hacking”

Ga wadanda suka saba karanta wannan shafi mai albarka, sun san a baya mun dauki tsawon lokaci ko ince makonni ko ma watanni, muna bayani kan su waye ‘yan Dandatsa?  Meye aikinsu?  Wace hanya suke bi wajen aiwatar da ayyukansu, musamman satar bayanan jama’a da kuma yada kwayoyin cuta a duniyar sadarwa?  Taken da muka baiwa wadancan kasidu dai shi ne: “Mu Leka Duniyar ‘Yan Dandatsa.”

- Adv -

Duk wanda ya karanta wadancan kasidu, wadanda a yanzu suke zube a Taskarmu dake www.babansadik.com/category/kariyar-bayanai, zai ga suna bayani ne a zube, wato ba wani tsari na musamman muka dauko ba, irin na darasi.  A wannan karon, darasin namu zai sha bamban da na farkon.  Domin bayani ne da ya shafi fanni mai zaman kansa, wanda ake yin karatu don neman samun shedar kwarewa da kuma dabbaka ilimin da aka koya a matsayin sana’a halattacciya.

Meye “Ethical Hacking” Kuma?

Kalmar “Hacking” dai kamar yadda mun sha bayanai a kai, shi ne amfani da kwarewa a fannin na’urori da hanyoyin sadarwa, don isa ga bayanai dake wata na’ura, wanda a al’adance ba kowa ke iya isa gare su ba.  Ko amfani da kwarewa wajen iya sarrafawa da kuma mallake na’urori da hanyoyin sadarwa cikin sauki.  Idan aka ce: “Hack” a turancin sadarwa na zamani, yana iya daukan ma’anar amfani da kokari na musamman wajen ganin “kwakwaf,” kan yadda wata na’ura ko wata hanya ta sadarwa ke aiki.  Wannan halattacciyar ma’anar wannan kalma kenan.

To amma da tafiya tayi nisa, sai ma’anarta a kwakwalen mutane ta canza, saboda samuwar masu amfani da wannan kwarewa wajen aiwatar da ta’addanci ga kwamfutoci ko na’urorinsu, ko kuma hanyoyin sadarwa na zamani. Wannan yasa da zarar ka ji ance “Hacker” ko “Hacking,” nan take ba abin da zuciyarka za ta hararo maka sai aikin ta’addanci ta hanyar sadarwa, ko wani dan ta’adda a fagen sadarwa na zamani; wanda ke barkowa cikin kwamfutoci da na’urorin jama’a don sacewa ko gaurayawa ko jirkita bayanansu.

Sanadiyyar yaduwar wadannan mutane masu mugun nufi, da yadda hakan ya canza wa jama’a ma’anarta a kwakwalensu, yasa aka samar da hanyoyin karantar da yadda za a dakile ayyukansu na ta’addanci, a halacce.  Daga cikin fannonin dake karantar da hanyoyin dakile ayyukan ‘yan dandatsa akwai fanni mai take: “Ethical Hacking,” wanda cibiyar EC-Council ke koyarwa.  Wanda ya samu horaswa kuma yaci jarabawa a wannan fanni, shi ake kira: “Certified Ethical Hacker” (CEH).  A takaice dai, abin da “Ethical Hacking” ke nufi dai, shi ne: “Tsarin dandatsanci mai lasisi.”  Shi kuma “Certified Ethical Hacker” ka kira shi: “Dan dandatsa mai lasisi.”

An kira su da wannan suna ne saboda duk wanda ya mallaki shedar kammala wannan karatu zai iya zama ma’aikaci a fannin kariyar bayanai (Information Security).  Sun sha bamban da wadanda ke amfani da kwarewar wajen aiwatar da ta’addanci.  Duk aikin iri daya ne.  Bambancin dake tsakaninsu shi ne, wadancan ‘yan ta’adda ne masu yi da mugun nufi.  Su kuma wadannan masu shedar karatu da shedar kwarewa, suna dakile ayyukan wadancan ne, da izinin masu ma’aikata ko kamfanin da kwamfutocin suke.   Daukansu ake yi na musamman, don baiwa kwamfutocin dake wata ma’aikata ko masana’anta ko kampani, kariya ta hanyar kwarewarsu.  Bayani kan haka na tafe in Allah ya so.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.