Dandalin Facebook a Mahangar Binciken Ilimi (3)

A yau ga mu dauke da kashi na uku cikin jerin kasidun da muke gudanar da bincike mai zurfi kan Dandalin Facebook. A sha karatu lafiya.

102

Yin Rajista a Dandalin Facebook

Kamar yadda bayanai suka gabata a baya, kafin ka fara mu’amala da mutane ko abokananka a Dandalin Facebook, dole kana bukatar yin rajista.  Yin rajista babu wahala, kuma kyauta ne.  Sai ka je shafin dandalin da ke http://www.facebook.com.  Kana shiga shafin, za ka inda aka rubuta “Sign Up – It’s Free, and Always Will Be.”  A kasan wannan bayani za ka samu dan karamin fam da za ka cike.  Wannan sabon tsari ne da suka bullo da shi don saukaka wa masu son yin rajista.  Amma a baya alamar “Sign Up” za ka matsa, sai a kaika inda wannan fam yake.  To, da zarar ka gangaron inda wannan fam yake, za ka samu yana dauke ne da wuraren shigar da bayanai guda bakwai, da kuma alamar da za ka matsa don yin rajistar, a can kasa.

Da farko sai ka shigar da sunanka na farko a inda aka rubuta “First Name”, sannan ka shigar da sunan mahaifinka a inda aka ce “Last Name”.  Ba dole bane sai ka shigar da “hakikanin sunayen”; idan ka ga dama kana iya amfani da lakabi kadai – misali kace “Baban” a wurin farko, da “Sadiq” a wuri na biyu, duk zai dauka.  Daga nan kuma sai ka shigar da adireshin Imel dinka a wurin da aka ce “email” – fasaha2007@yahoo.com, misali.  Sai ka kara gangarawa kasa inda aka ce “Re-enter Email”, ka kara shigar da adireshin Imel dinka.  Bayan ka shigar a karo na biyu, sai ka sake gangarawa inda aka ce “Password”, ka shigar da kalmomin iznin shiga da kake son tsare shafinka da su.  A nan, kirkira za ka yi, wasu kalmomi da suka hada da lambobi ko alamu, daga hudu zuwa goma sha biyu, misali.  Bayan ka shigar, sai ka gangara zuwa inda aka rubuta “Sex”, ka zabi jinsinka: “Male”, idan na namiji ne, ko “Female”, idan mace ce.  Sai kuma kafa ta karshe, inda za ka shigar da tarihin haihuwarka, wato “Date of Birth”.

A can kasa karshe, sai ka matsa alamar da ta ce: “Sign Up”.  Matsa wannan alama ke da wuya, za a budo maka wasu haruffa a sifar alamu, da ake son ka shigar da su cikin wata ‘yar akwati.  Wannan shi ake kira “Security Checker”; kuma kariya ne ga shafinka baki daya.  Da zarar ka shigar, sai a zarce da kai shafin da ka bude kai tsaye, inda za a baka zabin zaban abokanai, ko shigar da sunayen wasu mutane da ke da alaka da yanayin sunanka ko jinsinka.  A daya bangaren kuma, kana iya zarcewa jakar Imel dinka nan take, inda za ka samu sakon Imel da aka aiko maka, ana maka maraba da shigowa Dandalin Facebook.  A cikin sakon har wa yau, akwai wata alama da za a umarce ka da matsawa, don karasa rajista.  Da zarar ka matsa alamar, nan take za ta zarce da kai shafinka ba tare da bata lokaci ba.  Wannan, a takaice, shi ne yadda ake yin rajista a shafi ko Dandalin Facebook.  Mai karatu ba ya bukatar wani bayanin da ya wuce wannan.  Sauran abubuwan da kanka za ka koyi yadda ake yinsu.

Yaduwar Dandalin Facebook a Duniya

Kamar yadda dukkan masu karatu suka sani, Dandalin Facebook ya shahara a duniya, kamar rana da wata.  Dalilan da suka haddasa wannan shahara kuwa ba a nesa suke ba.  Na farko dai asalin wannan dandali su ne matasa.  Daga matasan da ke jami’a, zuwa ‘yan sakandare, har zuwa kan kananan yara masu sama da shekaru goma sha uku.  Wadannan matasa su ne kusan kashi sittin cikin masu rajista a wannan dandali.  Galibin ‘yan jami’a duk sun yi rajista; daga samari zuwa ‘yan mata.  Kuma su ne masu raya wannan Dandali wajen harkar abota da yada bayanai.

- Adv -

Abu na biyu da ya kara wa wannan dandali shahara shi ne samuwar kafafen yada labarai ta hanyar dandalin.  Galibin gidajen yanar sadarwa masu yada labarai ko samar da bayanai, duk suna da shafi a dandalin Facebook.  Daga gidajen rediyo irinsu BBC da VOA da Deustchwelle, har zuwa gidajen talabijin irinsu CNN, da sauransu, duk sun mallaki shafuka a wannan dandali.  Hakan ya karkato akalar masu karatunsu zuwa shafin ko dandalin Facebook, inda su ma suka mallaki shafuka don samun saukin mu’amala da labaran da suke nema a wadancan shafuka.  Haka kuma, kafafen jaridu da mujallu ma sun mallaki shafuka a wannan dandali. Duk samuwar hakan na cikin manyan dalilan da suka kara wa wannan dandali shahara nesa ba kusa ba.

Abu na gaba kuma shi ne samuwar kafofin kasuwanci zuwa wannan muhalli na Facebook.  Da farko dai wannan dandali an kirkire shi ne don abota da tattaunawa a tsakanin mutane daga wurare daban-daban.  Amma da tafiya ta yi nisa, sai gidajen yanar sadarwa na kamfanonin kasuwanci da ke kasashen Turai da Amurka da Asiya suka fara bude shafuka a dandalin.  Bayan su, akwai kamfanonin saye da sayarwa na Intanet da ke saka tallace-tallacen hajojinsu a dandalin.  Sannan a karshe, akwai ‘yan kananan shagunan saye da sayarwa a kowane shafi ka bude, wato Market Place.  Samuwan wadannan kafofin saye da sayarwa a shafin Facebook na cikin abin da ya dada kara wa shafin shahara.

Dalili na gaba kuma shi ne yaduwan hanyoyin yada ra’ayoyin siyasa musamman.  Wannan ya ba da damar yaduwar shafukan yada ra’ayoyin jam’iyyun siyasa daga kasashe daban-daban.  A halin yanzu, babu wani shahararren dan siyasa a duniya da bai mallaki shafi a dandanlin Facebook ba.  Ko dai ya zama shi ya bude da kansa, ko wasu suka bude da umarninsa, ko kuma, a karo na karshe, ya zama an bude ne don yada ra’ayoyi da manufofinsa na siyasa a dandalin.  Daga kan shugabannin Amurka, da na Ingila, zuwa kan sarakunan gargajiya na kasashe daban-daban, duk za ka samu sun mallaki shafuka a Facebook.  Ba nan kadai ba, akwai kungiyoyin sa-kai masu kokarin tabbatar da wasu manufofi ko na siyasa, ko na gargajiya, ko kuma na tsarin zamantakewa; su ma suna da shafuka a wannan dandali.  Kari a kan haka, akwai kungoyoyin addini – musamman na kirista – a jam’ance ko a daidaikun mutane, duk sun bude shafuka.  Wannan tsari shi ma, yana cikin abin da ya kara wa Dandalin Facebook shahara a duniya.

Abu na gaba shi ne samuwar masarrafai masu sawwake mu’amala a dandalin baki daya.  Masarrafai, ko kace “applications” a turance, su ne kananan sinadaran da ke baka damar aiwatar da abubuwa da dama; daga shigar hotuna, zuwa karban rokon abotar wasu, har zuwa nemo sunaye ko adireshin wasu, duk da wadannan masarrafai za ka yi.  Su ne kayan aiki a dandalin. Su ne kanwa uwar gami.  Sannan, kana iya makala alamar shafinka a wani gidan yanar sadarwa ko Mudawwanarka.  Bayan haka, kana iya amfani da wadannan masarrafai wajen makala adireshin gidan yanar sadarwa ko Mudawwanarka a shafinka na Facebook.  Dukkan wadannan na cikin abin da ya kara wa dandalin shahara a tsakanin jama’ar Intanet.

Sai kuma sauki da tsarin dandalin ya sifatu da shi.  A bayyane yake cewa, neman sauki dabi’a ce ta dan Adam.  Duk inda sauki yake, to shi ma yana wajen.  Wannan dandali na Facebook ya shahara ta bangaren saukin mu’amala a yayin da mai ziyara ke mu’amala da shafi ko abokan huldarsa a dandalin.  Akwai sauki wajen yin rajista.  Akwai sauki wajen shiga.  Akwai sauki wajen sanya hotuna.  Akwai sauki wajen neman abokai.  Akwai sauki wajen yada bayanai.  Akwai sauki wajen neman bayanai.  Akwai sauki wajen karanta bayanai da sakonni.  Akwai sauki wajen rubutawa da aikawa da sakonni.  Akwai sauki wajen mu’amala da masarrafan da ke shafin. Sannan, a karo na karshe, akwai sauki tattare da mu’amala da abokan hulda a shafin baki daya.  Wannan dabi’a da sifa ta sauki, na cikin ababen da suka kara wa shafin Facebook shahara a duniya baki daya.

Bayan sifar sauki da dandalin ya dabi’antu da ita, abu na gaba shi ne yawan sauye-sauyen da masu dandalin ke yi a shafin, da kuma damar da suka baiwa kwararru kan manhajar kwamfuta don ginawa tare da ajiye kananan masarrafai masu sawwake mu’amala a shafin.  Kamar yadda bayanai suka gabata a makonnin baya, akwai kwararru kan harkar kwamfuta, wato Developers, sama da dubu arba’in da hudu masu rajista kuma suke taimakawa wajen gina kananan masarrafai don amfanin masu rajista a dandalin.  Ire-iren wadannan sauye-sauye na cikin abubuwan da suka kara wa wannan dandali shahara a tsakanin masu amfani da Intanet.

Dalili na karshe, shi ne shahara a bakin mutane.  Akwai da dama da suka saba da Kalmar “Facebook” a bakinsu, amma ba su ma taba shiga shafin ba.  Wannan ke nuna cewa lallai shaharar ta kasaita, tunda har wadanda ma basu taba shiga shafin ba sun san sunan shafin a bakinsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.