Fasahar “Fiber Optics”: Daga Kunun Gilasai Zuwa Silin Gashin Haske (1)

Daga cikin nau’ukan wayoyin dake dauke da sinadaran sadarwa a zamanin yau akwai nau’in “Fibre Optics”, wanda ke samuwa ta hanyar gilasai da ake nikewa a dama shi kamar kunu. Daga wannan mako za mu fara bincike don fayyace hakikanin wannan sabuwar fasaha. Wannan shi ne kashi na farko. A sha karatu lafiya.

211

Mukaddima

Sau tari na sha samun tambayoyi daga masu karatu masu neman Karin bayani kan irin wayoyin da kamfanonin sadarwar wayar salula na Nijeriya ke binnewa a manyan tituna da hanyoyin kasar nan.  Wadannan masu karatu ko masu tambaya na son sanin amfanin wadannan wayoyi ne, da kuma alakarsu da hanyoyin sadarwa na wayar-iska.  Tunda an ce galibin hanyoyin sadarwa ta tarho, musamman ta salula, na amfani ne da tsarin sadarwa ta wayar-iska, wato Wireless Communication System, to meye kuma na shimfida wayoyi a karkashin kasa don “inganta” sadarwa?  Wadannan tambayoyi ba daga wajen masu karatu kadai nake samunsu ba, hatta daga wajen abokanai na, musamman ma wadanda nake musu ganin ya kamata a ce sun san alakar da ke tsakanin wadannan wayoyi da tsarin sadarwa ta zamani.

To amma ilmi fadi ne da shi, kuma ba abin mamaki bane don mutum yace bai san wani abu ba. Domin a burbushin kowane mai ilmi, kamar yadda Allah Ya tabbatar a Kur’ani, to akwai wani masani.

Cikin watanni hudu da suka gabata ne daya cikin masu karatu ya rubuto tambaya kan haka;  sunansa Ibrahim Yahaya Dan-hutu, in ban mance ba.  Cikin amsar da na bashi ne nayi alkawarin samun lokaci don gabatar da kasida ko jerin kasidu na musamman masu bayani kan irin wadannan wayoyi da kamfanonin wayar tarho ke binnewa a kasa; me ye yanayinsu?  Da me aka kera su?  Me ye alakarsu da tsarin sadarwa ta tarho ko zamani baki daya?  Shin akwai ma wasu fannoni na rayuwa da wadannan nau’ukan wayoyi ke tasiri a cikinsu ne, ko kuwa fannin sadarwa ne kadai?  Duk wadannan na cikin abubuwan da za mu tabo, cikin wannan kasida da za mu fara ta a yau, kan Fasahar Optical Fiber, wato kunun gilasai da aka markada su zuwa silin gashi don samarwa tare da aika bayanai cikin gaggawa da inganci, a tsari ko yanayin haske.

- Adv -

Wayoyi Nau’in Fiber Optics

Wayoyin sadar da bayanai ta tsarin haske da ake kira Fiber Optics Wire”, wadanda kuma ake samar da su ta fasahar Optical Fiber, wayoyi ne na “kunun gilasai”, wadda aka tsattsaga gwargwadon kaurin silin gashin kai.  Yadda abin yake shi ne, gilasai ake narkawa, ko damawa kamar kunu, sannan a sandarar dasu, tare da yayyanka su filla-filla, ko sille-sille, ko sili-sili, gwargwadon kaurin gashin kai, sannan a hada su wuri guda, a suturce su da gasassun robobi (plastics), sannan a maye samansu da dafaffiyar roba (rubber).  Wannan nau’in waya ita ake kira “Fiber-Optics Wire”. Fasahar da aka yi amfani da ita wajen kera wayar kuma ita ce “Optical Fiber”.  Kuma su ne wayoyin da suka fi saurin isar da sakonnin murya da bayanai na haruffa da bidiyo, da kuma hotuna, saboda suna tafiya ne a matsayin haske, cikin gaggawa ba bata lokaci.

Idan kana son fahimtar yadda tsarin saurin isar da sako da wannan waya ke yi, ka dubi yadda haske ke saurin isa idan aka haska tocila daga bakin wani bututu, zuwa  karshensa. Nan take zai isa.  Idan ma bututun ba a saiti yake ba, sai ka dubi inda yake da kwana, ka sanya gilashi a wajen.  Da zarar ka kara haskawa, dungun da ke dauke da gilashi zai cilla hasken zuwa gaba, har ya isa inda ake son yaje.  To idan ka dubi wannan waya da aka kera da gilasai, sai ka ga cewa da zarar ballin haske ya sauka kan silin waya guda daya, to duk zata haskaka sauran, tare da isar da hasken da ke dauke da bayanan cikin gaugawa.  Wannan kuma ya shafi hasken da ke dauke da murya ne (Tarho da Rediyo), ko bayanai (Intanet), ko kuma hotuna masu motsi da daskararru (TV da Bidiyo), misali.

Don haka kake ganin kamfanin MTN (da ma GLO) suna binne wannan waya, don inganta tsarin sadarwarsu tsakanin tashoshin sadarwarsu da suka game dukkan jihohin kasar nan.  Kai ba nan kasar kadai ba, galibin manyan tekunan duniya na dauke ne da wadannan wayoyi a cikinsu, ko karkashinsu, wadanda kamfanonin sadarwa na kasashe dabam-daban ke binnewa don isar da sadarwa cikin gaugawa da sauki a duniya baki daya.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Abdullhi says

    don Allah ragowar

Leave A Reply

Your email address will not be published.