Gina Gidan Yanar Sadarwa (Web Design)

Kamar yadda nayi alƙawari makon da ya gabata, yau ga ni ɗauke da bayani kan Gina Gidan Yanar Sadarwa.  Sai dai wani hanzari ba gudu ba. . .masu karatu za su ji dandanon wannan ƙasida ta canza, sabanin yadda aka saba jin bayani tiryan-tiryan.  Hakan ya faru ne saboda wahalan da ke tattare da wannan ɓangare na Gina Gidan  Yanar Sadarwa.  Domin wani ɓangare ne da ke buƙatar dogon bayani da misalai masu tsawo, wanda wannan fili bazai iya ɗaukewa ba a lokaci ɗaya. Ilimi ne har wa yau, da ke buƙatar dabbaka shi a aikace.  Don haka abin da na gabatar a nan kawai ‘yar takaitacciyar mukaddima ce, don a fahimci abin da Gina Gidan Yanar Sadarwa ke nufi, ba wai a koya ma mai karatu hakikanin yadda ake ginin ba.

438

 Ma’anar “Web Design”

 Gina Gidan Yanar Sadarwa wanda a turance ake kira Web Desiging, shi ne tsara Shafukan Yanar Gizo (Web Pages)  masu Rariyar Likau (Links), ta hanyar amfani da ɗaya daga cikin masarrafan gina gidan yanar sadarwa, wato Web Design Software.  Kowane Gidan Yanar Sadarwa na ɗauke ne da ɓangarori biyu muhimmai; ɓangaren farko shi ne fuskan Gidan Yanar Sadarwan, wato Zaure kenan, ko Home Page a turance.  Wannan shi ne shafin farko na kowane Gidan Yanar Sadarwa, kuma shi ne ɓangaren da ke ɗauke da muhimman bayanai kan irin nau’in abin da Uban Gidan Yanar (Webmaster) ke tallatawa, ko yake son masu ziyara su sani, a takaice.  A wannan Zaure mai ziyara zai samu jagora zuwa ɓangare na biyu da ke Gidan Yanar Sadarwan.  Wannan ɓangare kuwa shi ne ɗakunan gidan yanar sadarwa, masu ɗauke da cikakkun bayanai – ƙasidu, hotuna, sautuka, hotuna masu motsi da sauransu – waɗanda mai ziyara zai yi mu’amala dasu.  Waɗannan su ake kira Web Pages a turance.  Ga taswiran dan ƙaramin Gidan Yanar Sadarwa mai ɗauke da tarihin Uban Gidan Yanar (Malam Sadau, tare da iyalinsa) nan, don misali:

 Gina Gidan Yanar Sadarwa

Idan kana son gina gidan yanar sadarwanka, dole ne ka tanadi kayayyakin aiki, kamar dai yadda za ka tanada idan asalin gidan zama za ka gina.  Muhimmai daga cikin waɗannan kayayyaki su ne:

Ilimin Gina Gidan Yanar Sadarwa: Wannan shi ne abu na farko; ka samu ilimin fasahan gina Gidan Yanar Sadarwa.  Akwai ilmummuka da dama da ake son mai gina gidan yanar sadarwa ya samu, kafin ya fara aiki, duk da yake ya danganta da irin abubuwan da zai zuba cikin gidan/shafukan.  A taƙaice dai yana buƙatar ilimin Hypertext Markup Language da nau’ukansa; irin su Extensive Hypertext Markup Language (XHTML), Extensible Markup Language (XML) da kuma ilimin Cascading Style Sheets (CSS).  Idan gidan yanar sadarwanka na buƙatan hotuna masu motsi (Animations) da sauti (Multimedia) ko kuma kana buƙatan runbun bayanai mai dimbin yawa wanda masu ziyara za su yi mu’amala dasu (Database), dole ka mallaki wani ɓangaren ilimin gina manhajar kwamfuta (Programming), irin su: Java, PHP, SQL, Pearl, C, C++, JavaScript, Flash da sauran irinsu.  Idan duk baka da ko ɗaya, sai ka samu masu yi, kuyi jinga don su gina maka ka biya su.

 Kwamfuta:  Kana buƙatar kwamfuta, wacce a kanta za ka gabatar da dukkan aikace-aikacenka.  Muhimmancin kwamfuta wajen gina gidan yanar sadarwa kamar muhimmancin fuloti ne, ga mai gina gida.  Ba sai lalai ka samu mai cilla gudu ba, a a.  ‘Yar madaidaiciya ma ta isa.  Kwamfutar nan mai talabijin ce (Desktop) ko tafi-da-gidanka (Laptop) ce, duk za ka iya samun kowacce.

Rariyar Tsallake-tsallake (Browser): Wannan itace masarrafan da za ta taimaka maka wajen gwaji, lokacin da kake aikin tsara shafukan gidan yanar sadarwarka.  Babban aikinta shi ne budo duk wani shafi da aka rubuta ko tsara shi ta amfani da ilimin gina gidan yanar sadarwa  mai rariyar likau, Hypertext Markup Language (HTML).  Da wannan masarrafa ne duk wani mai lilo da tsallake-tsallake a Yanar Gizo yake lilawa.  Don haka, da zarar ka tashi gwaji, sai ka kira ta, za ta buɗo maka shafukan kamar yadda mai ziyara zai gansu idan ka ɗora a Giza-gizan sadarwa ta duniya.  Galibi ana samun wannan masarrafa a dukkan sabuwar kwamfuta, kuma akwai nau’uka daban-daban.  Shahararru daga cikinsu sune: Internet Explorer, na kamfanin Microsoft, da Netscape na kamfanin Netscape, sai kuma Firefox na kamfanin Mozilla.

- Adv -

Masarrafan Gina Gidan Yanar Sadarwa: Daga nan sai ka nemi allon rubutu, wanda dashi ake gina shafukan da ke kowane gidan yanar sadarwa.  Akwai su iri iri su ma.  Shahararru daga cikinsu sune: Notepad, Frontpage, Wordpad, Mcrosoft Publisher, Dreamweaver, da JEdit. Ba ka buƙatar sayan hudun farko, don suna zuwa cikin manhajar Windows da ke kowace kwamfuta. Idan gidan yanar da kake son ginawa ya tattaro hotuna da sauti da hotuna masu motsi (video clips, animations), a nan kana buƙatar masarrafan tsara hotuna da daidaitasu, irin su Photoshop, Paintshop Pro, Corel Draw ko Fireworks na kamfanin Micromedia, da kuma masarrafa irin su Micromedia Flash ko Freehand.  Duk hotunan da za ka ci karo dasu a gidajen yanar sadarwa, kashi casa’in cikin ɗari da waɗannan masarrafan aka gina ko tsara su.

 Makamashi:  Sune kayayyakin da za ka zuba a cikin ɗakunan da ka gina da waɗannan masarrafa da bayanarsu suka gabata a sama, don masu ziyara su rinka mu’amala dasu.  Waɗannan karikitai kuwa sune: bayanai (haruffa – baƙaƙe, ƙasidu), sauti, hotuna – masu motsi da marasa motsi – taswira da sauransu.  Waɗannan duk ana shigar dasu cikin masarrafan a matsayin rubutu – wato haruffa – ta hanyar wani lugga na fasahar gina gidan yanar sadarwa, wato Hypertext Markup Language Tags, ko kace HTML Tags, a takaiceDa zarar an shigar dasu, sai a adana (saving) cikin tumbin kwamfuta (Hard Drive).  Daga nan sai ka matsa Rariyar Tsallake-tsallakenka, wato Browser.  Ita ce za ta karanta umarnin da ka bata a masarrafan gina gidan yanar sadarwa (Notepad ne ko Dreamweaver), ta kuma budo maka shafin kamar yadda ka umarceta.  Ga gajeren misali nan da masarrafan Notepad, wanda na rubuta don gwaji:  Abin da nace mata a nan shi ne, “ki tsara mini shafin yanar gizo mai tambarin “BABAN SADIQ”, ki kuma bayyana “DUNIYA SALAMU ALAIKUM!” da manyan baƙaƙe, kumburarru (bold) a cikin shafin.”

Don haka, ga abin da Rariyar Tsallake-tsallaken ta bayyana nan ƙasa (a lura da gurun saman shafin (wato Title Bar), za a ga tambarin BABAN SADIQ, sauran bayanai kuma na cikin ainihin shafin, kamar haka):

Haka za ka ci gaba da gina shafukan Yanar, ɗaya bayan ɗaya.  Idan ka gama, sai ka zabi shafi guda, ka mayar dashi Zauren Gidan Yanar, wato Homepage, shafin da dukkan mai ziyara zai fara cin karo dashi, da zarar ya shigo Gidan Yanar Sadarwanka. Za ka jona dukkan shafukan da juna, daga Zauren Gidan Yanar, zuwa ƙananan ɗakunan, don masu ziyasa su samu sauƙin  zirga-zirga cikin gidanka ba tare da wata wahala ba.  Da ka gama, sai ka doshi mataki na gaba, wato Masu Sadarwa.

Masu Sadarwa:  Sai ka nemi kamfanonin da ke sadar da kwamfuta da Intanet, wato Internet Service Providers – ISPs.  Su za su maka abubuwa biyu; suyi maka rajistan adireshin da ka zaɓa, a matsayin adireshin Gidan Yanar Sadarwanka; su kuma ajiye maka shafukan Gidan Yanarka, wato Web Hosting, cikin Uwar Garkensu – Web Servers.  Kowanne daga cikin waɗannan ayyuka biyu na da farashinsa daban.  Don haka, da zarar ka biya su, sai su riskar ko kuma ɗora shafuka ko ginannen Gidan Yanar Sadarwanka a Giza-gizan Sadarwa ta Duniya, inda kowa zai iya ziyarta, ta hanyar adireshin da kayi rajista dashi.

Mataki na karshe shi ne abin da yafi komai wahala, wato lura da Gidan Yanar Sadarwanka, a kullum, ko duk wata, ko shekara.  Ya danganci irin nau’in bayanar da ka tula a ciki.  Idan gidan yanar sadarwan ta jarida ce, a kullum sai kai aiki a ciki kenan; wajen cirewa da kuma zuba sabbin bayanai (labarai da ƙasidu da sauransu).  Idan kuma ta kashin kanka ce, wanda ka zuba tarihinka a ciki, to duk lokacin da wani bayani ya canza, sai ka mayar da wani a madadinsa.  Ka zama Webmaster kenan.

A mako na gaba in Allah Ya yarda, zan aiko bayanai kan yadda ake lilo da tsallake-tsallake a Giza-gizan Sadarwa ta Duniya, wato Web Browsing ko Surfing, a turance.  Kafin nan, ina taya mu murnar ganin ƙarshen wannan wata mai alfarma lafiya. Allah Ya karbi ayyukanmu, Ya kuma sa mu amfana da darussan da muka koya cikinsa, amin.  Barka da Sallah!

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Nazifi Ado Muhammad says

    kai amma fa mun gode Allah ya saka da alkhairi Ameeen bababn sadiq. good of you as a brother in Islam.

Leave A Reply

Your email address will not be published.