Hanyoyin Inganta Al’umma a Kimiyyance (1)

A cikin watannin baya da suka shige idan masu karatu basu mance ba, mun gudanar da bincike na musamman kan hanyoyin ciyar da Najeriya gaba a fannin kimiyya da kere-kere. A wannan karo za mu dora da bayani kan hanyoyin ciyar da al’umma gaba a fannin kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya.

228

Mabudin Kunnuwa

Daga tambayoyin da na amsa a kwanakin baya a wannan shafi mai albarka akwai tambayar Malam Ali Fancy dan mutan garin Garko, wanda ya nemi sanin ko gaskiya ne cewa masu aiki da na’urar gano cuta mai suna X-Ray Machine a asibiti ko dakin bincike, ba su yin tsawon rayuwa, sanadiyyar sinadaran da ke dauke cikin wannan haske na X-Ray mai dauke da guba mai cutarwa ga lafiya.  Na bashi amsa ne ta hanyar kawo illolin da ke tattare da wannan haske, da bashi shawara don zuwa wajen likita da neman tabbaci kan zancen da yace ya ji a bakin wani likita da ke amsa tambayoyi a sashen Hausa na rediyon BBC.

Amma bayan wasu ‘yan kwanaki sai na lura cewa wannan amsa da na bashi, tare da wanda ya ji daga bakin wancan likita, na iya sa shi jin wata nakasa a cikin zuciyarsa. Ba shi kadai ba ma, har da ma duk wanda ya karanta wannan amsa.  Wannan nakasa kuwa ita ce: ya ji cewa ashe wannan ba fannin da ya kamata a karanta ko a koya bane.  Musamman ganin yadda muke da kasala a yau, wajen neman sauki da kauce wa mutuwa. Tabbas dabi’a ce mutum ya ji ba ya son mutuwa, amma duk yadda mutum ya kai da shiga hadari, sai kwanakinsa sun kare sannan zai mutu.  Don haka na zurfafa tunani da bincike, don jaddada mana hanyoyin da za mu bi wajen ciyar da al’ummarmu gaba a dukkan fagen ilmi, musamman a bangaren kimiyya da kere-kere, wato Science and Technology.

Fannonin Ilimi

A tabbace yake cewa kowane fanni na ilmi na da wani nau’i na fa’ida wajen ciyar da ita gaba.  Amma al’ummomi sun sha bamban wajen wani fanni ne suka fi bukata wanne ne suke da karancin bukata gare shi.  A yayin da mu a nan (wato kasashe masu tasowa) muna da bukatuwar kusan kowane fannin ilmi na zamani sanadiyyar halin da muke ciki, a kasashen da suka ci gaba a fannin tattalin arzikin kasa sai dai su haddade fannonin da suke da nasaka a cikinsa.  Wajibi ne a kan kowace al’umma tayi nazari kan al’ummarta, da irin ci gaban da tayi, da abin da take da karancinsa wajen ci gaba a zamanance ne ko a addinance, musamman idan mai addini ce.  Bayan wannan nazari ne za ta fahimci nakasarta, da ci gabanta, da fannonin da take da karancin bukatuwa zuwa gare su.

Dangane da abin da ya shafi kasarmu Najeriya a jimlace, da nan Arewacin kasar a takaice, fannin da muka fi tsananin bukata gare shi shi ne fannin  kimiyya gaba dayansa.  Wannan fanni ne mai fadin gaske, domin ya kunshi likitanci, da fannin lissafi, da kimiyyar sadarwa –  da dukkan bangarorinsa – da kuma kere-kere.  Duk da shekarun da jami’o’inmu suka kwashe suna karantar da wannan fanni, da himmar da gwamnatoci suka bayar ko suke bayarwa, har yanzu da sauran rina a kaba. Muna da karancin likitoci, da kwararru a fannin sadarwar zamani, da kuma kwararru a fannin kere-kere. Wani abin bakin ma shi ne, duk da karancin kwararru da muke fama da shi a wadannan fannoni, ‘yan kadan din da muke dasu galibi duk sun gudu zuwa wasu kasashe saboda karancin kayan aiki don dabbaka abin da suka koya, ko rashin kula a bangaren hukuma da dai sauran matsaloli da muka sani.  Wannan a bangaren wadanda suka kammala karatun kenan.

- Adv -

Dalilan Rauni

A daya bangaren kuma, galibin matasanmu basu cika son karanta fannonin da suka shafi kimiyya da kere-kere ba, saboda dalilai masu dimbin yawa. Wadannan fannoni su ne wadanda a baya na kawo su.  Galibi suna gudan wadannan fanno ni saboda wasu dalilan da basu taka kara ba balle su karya.  Abu na farko shi ne tsoron fannin lissafi. Wannan fanni na lissafi yana da muhimmanci matuka a rayuwar dan adam. A takaice ma dai, babu wani abin da yafi game rayuwar dan adam, wanda dan adam ya fi yinshi a dukkan jujjuyawar rayuwarsa irin lissafi. To amma saboda fanni da ke bukatar natsuwa, da hazaka, da hakuri, da kuma juriya, sai ya zama ba kowa ke iya daurewa wajen cin gajiyarsa ba. Da yawa daga cikin matasanmu kan fadi jarabawar wannan fanni tun daga matakin sakandare.  Wannan ke sa idan suka tashi zuwa jami’a suke neman wani fanni mara kalubale, wanda kuma ba a bukatar fannin lissafi a matsayin ka’idojin daukar dalibai.

Abu na biyu shi ne tsaurin karatu. Da yawa daga cikinmu mun sa a zuciyarmu cewa fannin kimiyya da kere-kere wani fanni ne mai tsaurin karatu a cikinsa. Wannan karaya ta zuci ce ke sa mu kasa yin wani hobbasa wajen gwada karanta shi balle koyonsa.  A kullum muna son fannoni masu sauki, masu dauke da zallar rubutu da karatu. Wannan yasa a karshe ma hatta ire-iren fannonin da muke komawa gare su muka shantake a cikinsu, ba mu ci balle mu fita da wani abin azo a gani.

Daga cikin dalilai da galibin matasa ke kawowa wajen guje wa fannin kimiyya da kere-kere a makarantu akwai matsalar “yawan bincike” kamar yadda suke cewa. Wai wadannan fannoni na kimiyya an cika yawaita bincike a cikinsu, wato: “Practicals” kenan.  Su kuma basu son duk wani abin da zai caza musu kwakwalwa. Wannan tsananin kasala ne da don jin dadi, wanda duk mai son ci gaba da rayuwa, ba zai taba samu ba muddin yana biye wa jikinsa da abin da ransa ke so.  Wata hujja da wasu ke bayarwa ita ce “Yawan shekarun karatu,” inda galibin fannonin da ke cikin fannin kimiyya da kere-kere duk shekarunsu sun fi tsawo wajen karatu idan aka kwatanta da sauran fannonin ilimi a jami’a. Wannan ma wata hujja ce ko kadan bai kamata a dogara gare ta ba. Dole lokutan karatunsu su tsawaita duk da cewa a wasu kasashen ba haka lamarin yake ba, amma fannoni ne da ake bukatar dalibi ya kware a cikinsu, ya zauna daram da kafafunsa, don kwatanta abin da ya koya ba tare da matsala ba.  Musamman ganin cewa fannoni da suka shafi rayuwa da lafiyar mutane kai-tsaye, kamar likitanci misali.

Hujja ta gaba ita ce “Hadarin da ke tattare da wasu fannoni” ga lafiyar dalibai, kamar yadda Malam Ali Fancy ya kawo, cewa an ce masu aiki a fannin Hasken X-Ray suna fuskantar karancin rayuwa a duniya, sanadiyyar sinadaran tururin haske, wato Radiation, wanda ke tattare da duk inda wannan nau’in haske yake. Ga wanda bai tsawaita bincike da tunani ba, sai ya ga ai wannan ba fannin da mutum zai je ya karanto bane, tunda an ce rayuwarka ba za a ta tsawaita ba sanadiyyar haske mai dauke da guba.  Ire-iren wadannan tuntuntuni na iya tsartuwa a zuciyar matashi ya kyamaci wani fanni na ilmi musamman da ya shafi kimiyya da kere-kere, wanda kuma watakila Allah ya bashi hazakar karatu, kawai himmar ce ta karye sanadiyyar gurguwar mahanga.  Ai idan muka yi la’akari za mu ga babu wani abin da a rayuwa ba ya dauke da hadari.  Hatta abinci a sadda kake cinsa, yana dauke da hadari. Domin akwai wadanda sun fara ci amma basu kare cin abincin da lafiyarsu ko ransu ba, sun wuce.  Balle a koma bangaren kasuwanci; komai a rayuwa akwai wani nau’i na hadari (ko ince hasara idan mai karatu ya fahimce ni sosai).  Muddin mutum yace bazai iya fuskantar hadari ba a rayuwa, to gwamma ya lume karkashin wannan kasar, ya daina rayuwa a kanta, zai fi masa sauki.

Akwai wadanda kuma suna da himmar, da kwazon, da kuma damar karatun, amma sun rasa wanda zai basu shawara ce ingantacciya kan fannin da ya kamata su fuskance shi wajen koyo. Wannan shi ake kira “Guidance & Counselling,” abin da kusan da yawa daga cikin matasa musamman a arewacin Najeriya suka rasa kenan. Domin a galibin makarantun sakandare da wahala ka samu bangaren da ke lura da wannan fanni mai matukar alfanu. Haka ake shiga makarantar, ayi karatun, a zabi abin da aka ga wasu sun zaba cikin abokai, a kuma kare. Wasu kan yi sa’ar iyaye su basu shawarwari kan fannin da zasu karanta. Amma galibin matasa, musamman wadanda iyayensu ko wasu ‘yan uwansu basu yi karatun zamani ba, sai abin da suka ga damar zaba ko fannin da ya musu zaki a zuci kawai suke kutsa masa. Wasu kuma shiriyar Ubangiji ce kawai ke sa su fuskanci abin da al’umma ke bukata.

Wata matsala da zan dakata a kanta ita ce matsalar kasala da son sauki. Galibinmu mun fi son sauki wajen karatu. Wannan kuwa ba zai yiwu ba. Da jiyar da jiki dadi da cin nasara wajen cin gaban rayuwa ba su taba haduwa.  Ko dai ka hakura da jin dadi na dan wani lokaci, daga baya ka samu ni’imar rayuwa kafin mutuwa, ko kuma ka biye wa son jin dadi, ka dakile a wuri daya a rayuwa. Zuciyar dan adam ta gaji son hutu ne da jin dadi. Duk kuwa wanda ya biye mata ba zai taba ci gaba a rayuwarsa ba.  Wannan na cikin matsalolin da suka jefa mu cikin halin da muke ciki a bangaren ilmin zamani, musamman matasanmu.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. MURYAR HAUSA24 ONLINE MEDIA says

    MASHA ALLAH

Leave A Reply

Your email address will not be published.