Hira da Edward Snowden (2)

Ga kashi na biyu na hirar Peter Taylor da Edward Snowden. A sha karatu lafiya.

437

Peter Taylor:  Amma kuma wannan bai baka damar kwashe bayanan gaba daya ka tafi dasu ba (kamar yadda kayi yanzu).

Snowden:  Akwai wani gagarumin kalubale dake fuskantar lamarin sanadiyyar muhawara da jama’a ke kanyi tun sadda na handako wadannan bayanai a shekarar 2013.  Wannan kalubale kuwa shi ne, wajibi ne a matsayinmu na ‘yan kasa mu damka bayanan da suka shafi rayuwarmu gaba daya a matsayin amana ga wadannan hukumomi na tsaron kasa…

Peter Taylor:  A yayin da su kuma hukumomin suke damka wannan amana a hannunku, amma ga shi kai kaci wannan amana…

Snowden:  Ko kadan babu wata amana da naci.  Domin da zarar an dauke ka aiki a hukumar CIA, wadda hukuma ce dake karkashin Hukumar Tsaro ta Kasa (NSA), za a umarceka ne da ka rantse da Allah cewa za ka baiwa Dokar Kasar Amurka kariya daga kowani irin abokin gaba; a cikin gida yake ko a waje.  Idan kuwa har wadannan hukumomi za su aikata wani abin da zai zama taka dokar kasa ne – wanda kuma kotunan kasar Amurka ma sun goyi bayana kan cewa abin da wadannan hukumomi suke yi ya saba wa doka –  to, su daina sa mu muna yin rantsuwa don kare wannan abin da suke yi.  Don haka, ni nayi aikina ne wanda ya dace da rantsuwar da nayi, wanda su suka kasa.

Bayan haka, babu wani riba da naci sanadiyyar hankado wadannan bayanai.  Kari a kan haka ma, ban taba yada wadannan bayanai a wani shafi na kashin kaina ba.  Ina hadin gwiwa ne da ‘yan jaridun kasar Amurka, wadanda su ne ke wakiltar jama’ar kasar Amurka wajen tabbatar da abin da yayi daidai da ra’ayin jama’a dangane da hujjojin da suka bayyana.  Amma a fili yake cewa galibin lokuta gwamnati sai tayi gum, taki magana.

Peter Taylor:  Lokacin da ka kuduri aniyar hankado wadannan bayanan sirri, ka yi tunani kan abin da zai biyo bayan haka, na barin kasarka zuwa wata kasa, musamman ma ga shi ka tsinci kanka a kasar Rasha.  Ka kuma yi tunanin hukumar Amurka da za ta saka a gaba da tuhuma, har sai ta kama ka da laifi?

Snowden: Sosai kuwa…(ya fashe da dariya)

Peter Taylor:  Dole kayi wannan tunanin.

Snowden:  Ban tunanin akwai wani mahalukin da bazai yi tunani irin wannan ba (kafin ya aiwatar da wannan abin da nayi)…

Peter Taylor:  …watakila ma har da zaman kaso na shekaru masu yawa.  Ba ka tunanin hukumar Amurka ba za ta hakura ba har sai ta kama ka?  Na dai tabbata sai kayi tunani irin wannan.

Snowden:  Na fi damuwa da mummunan tasirin wannan tsari na hukuma ga al’ummar kasar Amurka baki daya, da yadda zai shafe su.  Da yadda wasu zasu fuskanci hatsari mai girma.  Abin da yafi damuna ma shi ne, tunanin ta yaya za mu iya sanin abin da ya kamata mu sani a matsayinmu na ‘yan kasa, don mu kare kanmu (daga irin wannan leken asiri), da kuma yadda za mu iya baiwa al’umma kariya daga dabi’un gwamnati wajen satar bayanansu, musamman a wannan zamani na habbakar hanyoyi da na’urorin sadarwa na zamani.

- Adv -

Peter Taylor:  Mece ce alakar dake tsakanin hukumar tsaron Amurka ta NSA, da kuma kishiyarta ta kasar Burtaniya mai suna GCHQ?

Snowden:  Hanya mafi sauki da za a fahimci wannan alaka ita ce: ita hukumar GCHQ tamkar wani reshe ne na hukumar NSA.  Hukumar NSA na baiwa GCHQ tallafi na miliyoyin daloli a duk shekara, tana bata kayayyakin aiki, da shawarwari, da kuma irin nau’ukan bayanan da za ta rika tatsowa.  A nata bangaren kuma, hukumar GCHQ na baiwa hukumar NSA kafofin tatsar bayanan da take tarawa ne daga al’ummar kasar Burtaniya, da sauran kasashen da ita Burtaniyan take da ruwa da tsaki wajen tafiyar dasu.

Peter Taylor:  A duk fadin duniya kenan?

Snowden:  Eh, a duk fadin duniya.  Wadannan bayanan sun hada da dukkan bayanan da GCHQ ke tarawa cikin kasar Burtaniya.  Amma abin mamaki, hukumar Amurka na riya cewa wai ba ta musayar bayanai da kasar Burtaniya, amma a fili yake cewa suna yi.

Peter Taylor:  Da hukumar NSA da GCHQ suna cewa, “Eh mun yarda cewa muna tatsar bayanan jama’a masu dimbin yawa, amma kuma bayanan da muke bukata daga cikinsu kadan ne matuka.  Ba ruwanmu da abin da mutane suke yi.  Wadansu daidaiku ne cikin mutane muke nema.”  Kuma idan ka dubi tsarin yadda suke tatso bayanan, za ka ga cewa a hankali za su iya kaiwa ga wadanda suke newa, wato ‘yan ta’adda, da masu manyan laifuka, tare da masu safaran miyagun kwayoyi.  To kuwa ka ga in haka ne, muddin suna son kama wadanda suke hari, dole ne su tatsi bayanai masu dimbin yawa, don ta haka ne za su iya kama wadanda suke nema.

Snowden:  Eh to, mu ma kaddara abin da suka fada haka ne a zahirin rayuwa.  Mu kaddara har wa yau suna tatsar bayanan dukkan jama’a….suna fa sanin duk abin da kake yi, da duk wuraren da kake zuwa…

Peter Taylor:  To amma ai basu bukatar irin wadannan bayanan…

Snowden:  Eh na yarda ba su bukatar irin wadannan bayanan, na yarda suna amfani da bayanan ne a lokacin da wata babbar matsala ta taso.  Wadannan dalilai na iya kama da hujjoji abin yarda, wadanda za su iya basu damar amfani da Majalisar dokoki don samar da dokar da za ta halatta musu wannan aiki.  To amma me ya hana su yunkurin samar da wadannan dokoki ta hanyar majalisa, don halatta musu aikin?

Peter Taylor:  Da yawa cikin mutane a Burtaniya na iya cewa, “Eh, mun yarda gaskiya ne hukumar GCHQ na tatsar bayanan mutane a sirrance, bamu damu ba muddin hakan zai taimaka musu wajen gano miyagu cikin al’umma.  Kuma bayan haka ma, mu mutanen kwarai ne, ba abin da za mu boye (wa hukuma).

Snowden:  Mutane da yawa baza su fadi haka ba.  Kuma masu fadin wancan magana basu yi kuskure ba, domin wannan wani lamari ne da za a iya muhawara a kansa.  Amma tambayar da ta kamata a musu ita ce:  shin, da gaske ne wannan tsari na leken asiri da hukuma ke yi ga ‘yan kasa, zai samar mana da tsaro?  A kasar Amurka mun ga irin gagarumin leken asirin da hukuma ke gudanarwa kan jama’a, sama da shekaru goma yanzu.  Hukumar White House ta nada wasu kwararru biyu don gudanar da bincike kan wannan tsari.

Sakamakon da suka fitar shi ne, wannan tsari na leken asiri da tatsar bayanan jama’a bai da tasirin da zai iya hana ‘yan ta’adda kawo mana hari.  Amfanin wannan tsari kadai shi ne don hada bayanan sirri.  Amma inda matsalar take shi ne, sai a rika gaya wa al’ummar Amurka cewa dalilin aiwatar da wannan tsari shi ne don kare kasa daga ta’addanci.  Tabbas tsarin na da tasiri wajen hada bayanan sirri.  Amma wannan ya sha bamban da ace wai hakan wata hanya ce ta kariya ga kasa kai tsaye.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.