Jirage Masu Sarrafa Kansu: Wani Sabon Salon Yaki a Duniya (1)

Daga cikin fasahar dake kan sharaha a fannin kere-kere yanzu a duniya akwai kirar jirage masu sarrafa kansu da ake kira: “Drones” a harshen Turanci. Daga wannan mako zamu fara bayani tarihi da samuwar wadannan nau’ukan jirage, da kuma yadda kasashen yamma ke amfani dasu cikin wani irin sabon salon yaki na zamani a duniya.

498

Mabudin Kunnuwa

Da yawa cikin masu lura da al’amuran yau da kullum kan harkokin duniya musamman a bangaren siyasar kasashe da zaman lafiya kan yi mamakin yadda kasar Amurka, ta hanyar Hukumar Tsaron Kasar (Department of Defence – DoD) ke amfani da wasu jirage da na’urorin zamani na sadarwa ke sarrafa su daga wata uwa duniya, don kashe ko darkake shahararrun abokan gabanta da suka yi fice wajen adawa da yadda hukumomin kasashen Turai da Amurkan ke gudanar da manufofinsu na siyasa, da kuma tasirin hakan ga kasashe musamman na Gabas-ta-Tsakiya. Galibin hare-haren da kasar Amurka ke kaiwa a bakin iyakar kasashen Pakistan da Afghanistan – inda ake kashe fararen hula, da ma sojojin kasar Pakistan – duk da wadannan jirage masu sarrafa kasar take amfani.

Cikin watan da ya gabata ne har wa yau Hukumar kasar Iran ta sanar da cewa ta bugo wani jirgi mai sarrafa kansa na kasar Amurka, wanda ya shigo iyakar kasarta da wajen tazarar Mil 44.  Bayan kwanaki biyu da wannan ikirari ne Gwamnatin kasar ta nuna wa manema labaru wannan jirgi da ta kado, a yayin da yake shawagi a cikin kasarta don leken asiri ko tattaro bayanan sirri, kamar yadda ta sanar.  Haka kuma, mako guda bayan wannan lamari na kasar Iran, sai ga sanarwa a kafafen yada labaru cewa wani jirgin kasar Amurka mai sarrafa kansa ya fado ko yayi hadari a daya daga cikin kasashen da ke Gabas-ta-Tsakiya.

A halin yanzu da nake wannan rubutu dai, kasar Amurka na da ire-iren wadannan jirage masu sarrafa kansu da take girke a kasar Djibouti, wanda daga cikinsu ne daya ya fado kasar Iran, har ta kado shi, duk da cewa ba a samu wata alamar karaya ko harbi ko ballewa a jikin jirgin ba.  Ba ma kasar Amurka ba kadai, a yanzu akwai kasashe 44 da ke da irin wadannan jirage masu sarrafa kansu na yaki, wato Drone ko Pilotless Aircraft.  Daga cikinsu akwai kasar Ingila, da Kanada, da Jamus, da Isra’ila, da Rasha da sauran kasashen nahiyar Turai.  Akwai alamar fannin Kimiyya da Kere-kere (Science and Technology) na taka rawa sosai wajen haddasa yaduwar ire-iren wadannan sababbin kayayyakin fasaha.

Wannan ya tuna min da wata kasida da babban Malami Sheikh Yusuf Al-Qardhaawi ya gabatar shekaru kusan bakwai da suka shige, kan mummunar tasirin binciken kimiyya a duniya, da yadda hakan ke zama sanadiyyar halaka rayuka da dukiyoyi a duniya baki daya.  Babban Malamin ya nuna cewa ba komai ya haddasa hakan ba sai karkatacciyar manufar da masu wannan ilmi ko bincike suke da ita, na son duniya, da rashin yarda da samuwar Allah a matsayin mahalicci abin bauta.  Wadannan munanan cututtukan zuci da Malamin ya zayyana, su ne suka samar wa duniya tsarin Mulki da Kasuwanci da ake ta kokarin kakaba wa kasashen Musulmi ko kasashe masu tasowa, cewa dole su yi riko da su a matsayin tafarkin rayuwa.  Wadannan tsare-tsare kuwa su ne tafarkin kasuwanci da tattalin arzikin kasa na Jari-hujja, wato Capitalism.  Wanda tsari ne da bai san talaka ba, sannan ya ginu ne a kan manufar tara dukiya, da kokarin taskance su.  Daya tsarin kuma, wanda ke kokarin mika hakkin hukunci da tsarin gudanar da rayuwa ko shugabanci ga mutane kadai – duk da nakasarsu wajen tunani da sanin maslahar kansu – shi ne tsarin Dimukiradiyya, wato Democracy.  Wanda duk abin da jama’a ta raja’a akai shi za a bi, ko da ya saba wa mahalicci da maslahar rayuwarsu wacce ba su iya hangowa a sadda suke yanke hukunci.

- Adv -

Wadannan tsare-tsare biyu, wato tsarin Jari-hujja a bangaren kasuwanci, da tsarin Dimukiradiyya a bangaren shugabanci, su ne manyan matsalolin duniya a halin yanzu. Domin suna gadar da son duniya, da tsoron mutuwa, da kwadayi, da son mulki, da danniya, da mamaya, da dai sauran abubuwan da a halin yanzu muke gani.  A bayyane yake cewa manyan kasashen duniya suna fama da matsalar tattalin arziki, da basussukan da suka musu katutu, wanda kuma hakan ya samo asali ne daga mummunar sakamakon tsarin Jari-hujja, musamman dabi’ar son tarawa, da cin mummunar riba, da barin ‘yan kasuwa su yi yadda suka ga dama. Wanda wadannan kuma, kamar yadda masu karatu za su shede ni, su ne manyan dirkokin tsarin Jari-hujja. A bangaren Dimukiradiyya kuwa ba sai na fadi abin da ke faruwa ba.

Kasashen da ke gaba-gaba wajen tallata wannan tsari suna iya kokarin kiyaye dokokinta a kasashensu, amma a wasu kasashen, sai wanda suka ga daman ya zama shugaba yake zama.  Akwai kasashen da sunyi kokarin bin tsarin, amma saboda mahangarsu ta rayuwa ta sha bamban da mahangar kasashen yamma da ke tallata tsarin, sai suka taimaka aka ruguza su.  Gajeren misali na cikin abin da ya faru a kasar Aljeriya a shekarar 1994.  Muna neman tsarin Allah daga faruwar irinsa a kasar Misra.  A takaice dai, hobbasa da ke haifar da samuwar ire-iren makaman yaki da suka sha karfin tunanin dan adam a yau, ta hanyar tallafin fannin Kimiyya da Fasahar Sadarwa da Kere-kere, na samun goyon bayan tsarin jari-hujja ne da tsarin shugabancin mamaya da danniya.  Ba ilmin bane aibu.  Ba abin da ake kerawan bane aibu a sake, sai dai manufar da ke karkashin hakan, wacce ke bayyana bayan tsawon zamani.  Jama’a ku gafarce ni, na buge da wani abin daban.

Ma’ana da Asali

Jirage masu sarrafa kansu, ko Drone, ko Unmanned Air Vehicle, ko Pilotless Aircraft kamar yadda ake kiransu a harshen Turanci, nau’ukan jirage ne marasa matuki, marasa direba, wadanda ake sarrafa su daga cibiyar sadarwa da ke kasa.  Wadannan jirage sun sha bamban da makamin mizail ko makami mai linzami.  Duk da cewa makaman mizail su ma ana harba su ne kamar yadda ake harba wadannan jirage masu sarrafa kansu, amma sabanin mizail, su jirage masu sarrafa kansu na iya daukan makamai ne su jefa a wuri, ko su dauki hoton wurin da abokan gaba suke, ko su dauko kaya, ko su gano inda masu rauni suke daga filin daga.  Su mizail makamai ne gaba dayansu.  Da zarar an harba su sukan isa wurin da aka aika su ne kai tsaye, shikenan sun gama aikinsu.  Sannan ana iya darkake makaman mizail kafin su isa inda aka jefa su ko a hanyar da suke tafiya, amma jirage masu sarrafa kansu na iya kubuta daga wannan, domin akwai wadanda ke iya bacewa cikin sararin samaniya, iya gwargwadon kwarewar makerinsu.  Bayan haka, mizail kamar mutum-mutumi ne su, inda aka tura su nan za su.  Amma jirage masu sarrafa kansu suna da dabi’un fahimtar abubuwa, da gani, da kuma kauciya ko gociya kamar yadda bayanai za su nuna nan gaba.

Tunani kan sarrafa jirgi ba tare da matuki ba ya samo asali ne tun shekarar 1898, a watan Mayu, lokacin bajekolin kayayyakin fasahar kere-kere da aka yi a Dandalin Madison (wato Madison Square) da ke birnin New York na kasar Amurka.  A wannan biki na bajekolin kayayyakin fasahar lantarki ne Nikolas Tesla, wani masanin kimiyyar lantarki, ya gabatar da wani jirgin ruwa da ake sarrafa shi ta amfani da siginar rediyo, daga waje.  A wurin ne yayi gwajin wannan jirgin ruwa, da yadda ake sarrafa shi ba tare da direba ba, daga waje, ta amfani da siginar rediyo.

Wannan bikin bajekoli dai an shirya shi ne wata guda bayan sojojin yakin kasar Andalus (Spain) sun nutsar da wani jirgin ruwan yakin kasar Amurka a gabar tekun Havana (Havana Harbour).  Watanni uku bayan wannan bikin bajekoli sai Nikolas Tesla ya rubuta kasida ta musamman kan yadda za a iya sarrafa jirgin yaki mara direba, don darkake abokan gaba a lokacin yaki, da yadda za a iya kai hari da irin wadannan jirage.  Daga nan sai ya tura wa mujallar Electric Engineer don ta buga.  Amma sai suka ki karban kasidar, domin a cewarsu, wannan wani abu ne da bazai taba iya faruwa ba, balle a yi tunanin shigar dashi cikin kundin ilmin kimiyya.  A takaice dai suka ce wannan wani nau’in binciken ilmi ne da ba za a iya dabbaka shi a aikace ba.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.