Jirage Masu Sarrafa Kansu: Wani Sabon Salon Yaki a Duniya (3)

A yau mun dubi shahararrun nau’ukan jirage masu sarrafa kansu ne da ake ji dasu a duniya. Wannan shi ne kashi na uku. A sha karatu lafiya.

541

Shahararrun Jirage Masu Sarrafa Kansu

Akwai nau’ukan jirage masu sarrafa kansu guda 12 da suka shahara. Nau’in jirgi na  farko shi ne mai suna QinetiQ Zephyr Solar Electric, wanda a halin yanzu an kiyasce cewa yayi shawagi na tsawon sa’o’i 336 da mintuna 22, wato kwatankwacin kwanaki 14 kenan tun bayan kera shi da aka yi a watan Yuli na shekarar 2010.  Akwai wani makamancinshi da aka kera a watan Yuli na shekarar 2008, shi kuma ya kwashe sa’o’i 82 ne da mintuna 37 a sararin samaniya.  Wannan sunansa daya ne da wanda ya gabace shi.  Sai kuma nau’i na gaba mai suna Boeing Condor, wanda aka kera a shekarar 1989.  Shi kuma a iya tsawon rayuwarsa yayi shawagi na tsawon sa’o’i 58 da mintuna 11 ne kacal.  A halin yanzu an masa ritaya, yana can a girke a Gidan Tarihin kayayyakin sojin sama na kasar Amurka da ke Jihar Kalfoniya.  Sai wani nau’in QinetiQ Zephyr da aka sake kerawa a shekarar 2007, wanda shi kuma aikin sa’o’i 54 kacal yayi.  Sai nau’in IAI Heron, wanda ba a tantance shekarar da aka kera shi ba, shi kuma shawagin sa’o’i 52 kacal ya kwashe a sararin samaniya.

- Adv -

Akwai kuma wani nau’i mai suna AC Propulsion Solar Electric da aka kera a watan Yuni na shekarar 2005.  Shi kuma sa’o’i 48 da mintuna 11 ya kwashe a iya shawaginsa.  Sai kuma MQ-1 Predator da ba a tantance shekarar da aka kera shi ba.  Sa’o’insa 40 ne da mintuna 5 a sararin samaniya.  Sai GNAT-750 da aka kera a shekarar 1992, yana daga cikin tsofaffin jirage.  Ya kwashe sa’o’i 40 ne kacal yana shawagi.  Akwai TAM-5 da ya bayyana a watan Agusta na shekarar 2003.  Shi kuma ya kwashe sa’o’i 38 ne da mintuna 52 a sararin samaniya.  Wannan shi ne mafi kankanta daga cikin jirage masu sarrafa kansu da kasar Amurka ta kera, wadanda za a iya cilla su sararin samaniya su yi dogon zango; TAM-5 ne mafi kankanta daga cikinsu.

Sai kuma nau’in Aerosonde da aka kera a watan Mayu na shekarar 2006.  Ya kwashe sa’o’i 38 ne kacal da mintuna 48 a shawaginsa.  Sai wani nau’i da aka kera don daukan kayan soji mai suna Vanguard Defense.  An kera shi ne a watan Fabrairu na shekarar 2011, wato shekarar da ta gabata kenan.  Shi kuma ya zuwa yanzu ya kwashe sa’o’i 2 ne da mintuna 55.  Tunda ba a jima da kera shi ba.  Sai nau’i na karshe da za mu dakata a kansu mai suna TAI Anka da aka kera a watan Disamba na shekarar 2010.  Shi kuma tafiyar kwana daya kacal yayi, wato sa’o’i 24 kenan.

Wadannan, a takaice, su ne shahararrun jirage masu sarrafa kansu da suka yi dogon zango a rayuwarsu.  Akwai wadanda ake kerawa a halin yanzu da ake sa ran su kwashe watanni ko ma shekara suna shawagi a sararin samaniya wajen tattaro bayanai ko kai hari ko kuma yin dako don gano shirye-shiryen abokan gaba.  Yanzu aka fara, wai mahaukaciya ta shiga gada sau tara.  Wannan wani zamani ne da muka shigo da kowace kasa ke kokarin kwatan kanta a bangaren tsaro ta hanyar kwarewarta a fannin kimiyya da fasahar sadarwar zamani.  Wacce bata fadaka ba kuma, ita ta jiwo, sautun mahaukaciya. Allah mana gamo da katar, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.