Ka’idojin Mu’amala da “Password” (11)

Ga kashi na 11 cikin jerin kasidun dake nazari kan “Kalmar Sirri”, wato “Password” da mahimmancinsa ga mai mu’amala a shafin Intanet. A sha karatu lafiya.

161

Idan Na Mance “Password” Din Kwamfuta ta

Bayan bayani kan inda ake adana “Password” a manyan manhajojin kwamfuta, abu ne sananne cewa mantuwa dabi’a ce ta dan adam; idan mutum ya mance “Password” din kwamfutarsa, ta yaya zai gano ko kuma goge wancan na farkon tare da shigar mata da sabo ba tare da ya rasa bayanansa ba a takaice, ko tunanin goge babbar manhajar ma ba idan abu ya faskara?  Lokuta da dama (ga wadanda basu sani ba) idan mutum ya mance “Password” din kwamfutarsa, ba tare da ya tanadi hanyar maido ta ba ta amfani da wani mazubi (Windows Password Reset Disc), to, ba abin da ake cewa sai dai a goge babbar manhajar don zuba mata sabo, wato: “Formatting” Kenan.

Wannan kuskure ne mai girman gaske, kuma hakan kan bayu zuwa ga rasa dukkan bayanan da mai kwamfutar ya mallaka gaba daya.  Wannan gazawa ce ga masanin kwamfuta ya dauki wannan hanya wai don kawai an mance “Password” din.  To meye abin yi?

Akwai hanyoyi da dama da masana suka tanada don ceto “Password” din kwamfuta da mai ita ya mance, ko kuma a kalla goge waccan tsohuwar da aka mance don shigar da sabuwa, ba tare da an rasa bayanan kwamfutar ba ko kuma goge babbar manhajarta.  Wannan abu ne mai sauki, wai cire wando ta ka!

A farkon lamari ma dai, an tanadi hanyar da za ka iya taskance “Password” din da ka shigar wa kwamfutarka ta hanyar amfani da kananan ma’adanar bayanai na zamani – irin su USB Flash Disk, da faifan CD, ko kuma faifan DVD idan abin ya kai makura.  A zamunnan baya akan yi amfani da ma’adanar Floppy Disk ce, amma a halin yanzu an daina yayinta.  Akwai inda aka tanada maka a bangaren tsare-tsaren kwamfutar, wato: “Control Panel,” sai ka zarce “User Accounts,” a bangaren hagu daga kasa za ka ga inda aka rubuta “Create Password Reset Disk,” sai ka makala wa kwamfutarka wannan ma’adana, don bata damar taskance maka “Password” dinka cikin yaren da take iya fahimta.  Da zarar ta gama za ta sanar da kai, sai ka cire, ka adana wannan ma’adana.  Duk sadda ka mance “Password” dinka sai ka dauko ta ka jona wa kwamfutar, nan take za ta fahimci bayanan dake ciki sai a baka damar shiga.

To amma idan tun a farko baka tanadi wannan hanya ba fa?  Yaya kenan?  Abu ne mai sauki, amma ga wanda Allah ya sawwake masa.

Akwai nau’ukan dabaru da kuma masarrafai na musamman da aka tanada masu taimaka wa mutum wajen dawo da “Password” dinsa dake kwamfutar.  Wadannan hanyoyi su ake kira: “Password Recovery Tools.”  Sannan akwai wadanda za su taimaka maka ne wajen goge wancan tsohuwar “Password” din, don baka damar shigar da sabuwa.  Sai dai dole ne a duk sadda ka samu kanka cikin bukatuwar ire-iren wadannan hanyoyi ka fahimci cewa wadannan abubuwa ko hanyoyi an samar dasu ne don amfanin kai da amfanar da mutane, ba hanyoyi bane da aka kirkira don baiwa ‘yan ta’adda saukin isa ga bayanan mutane ba.  Samun wannan tunani a kwakwalwarka zai taimaka maka wajen fa’idantuwa dasu ba tare da samun wasuwasin juyar da manufarka don aikata ta’addanci ba.

Daga cikin dabaru akwai wadda za ka iya yi ba tare da kashe ko sisinka ba wajen warware matsalar.  Misali, mu kaddara kana da kwamfuta nau’in Windows 7 ko Windows Vista, sai ka mance “Password” dinta.  Ka kasa tunawa gaba daya.  Kuma kana da bayanai masu matukar mahimmancin da baza ka so a ce an goge babbar manhajar ba gaba daya.  Abu ne mai sauki.  Sai kawai ka kashe kwamfutar ka sake kunnawa, kafin ta gama kunnuwa sai ka sake matsa maballin kashewa (Power Key) nan take.  Idan ta fara kunnuwa za a kaika inda aka rubuta: “Start Windows Normally,” da “Repair Windows (recommended)” sai ka zabi na biyun.

- Adv -

A takaice dai masana kanyi amfani da wannan hanya ne wajen isa ga dukkan bayanan babbar manhajar kwamfutar (Operating System Files), tare da kwafa da canza sunayen wasu manhajoji guda biyu (“sethc” da “cmd”) don yin amfani dasu wajen goge wancan tsohuwar “Password” din da ka mance, tare da shigar mata da wani sabo.  Karkashin wannan dabara, za ka iya ganin dukkan sunayen masu hurumi a kwamfutar (User Accounts).  Wannan hanya ce mai sauki.  Da zarar ka samu biyan bukata sai ka sake amfani da wannan hanya wajen goge sunayen manhojin da ka kwafa da wadda ka canza mata suna zuwa asalinta.  Wannan daya ne daga cikin hanyoyin.  Duk da cewa ba bayani nayi filla-filla ba saboda dalilan tsaro.

Ta bangaren manhajoji kuma akwai irin su “OphCrack” wacce za ka iya amfani da ita wajen gano “Password” din dake kwamfutarka ko da guda nawa ne, iya gwargwadon tsauri ko saukinsu.  Kana iya saukar da manhajar daga gidan yanar sadarwar masu manhajar, sai ka kona ta cikin faifan CD, ko cikin ma’adanar Flash.  Sai ka kashe kwamfutar, ka tsofa ma’adanar a jikin kwamfutar, ka sake kunna ta.  Kafin ta fara kunnuwa sai ka matsa “F10” ko “escape” daga allon shigar da bayananka (ya danganci nau’in kwamfutarka da kamfanin da ya kera. Abin nufi dai za ka shiga “Boot Options” ne) don baiwa kwamfutar umarni ta kunna kanta daga manhajar dake cikin ma’adanar Flash da ka Makala mata ko na CD.  Da zarar ta fara haka, shafi zai budo wanda zai baka damar gano duk “Password” din dake kwamfutar, cikin sauki.

Bayan manhajar “OphCrack” kuma akwai “PC Login,” wadda ke iya taimaka maka wajen goge tsohuwar “Password” din da ka mance, don shigar da wata sabuwa.  Kamar wadda ta gabace ta, ita ma saukarwa ake daga gidan yanar sadarwar mai manhajar, sannan a tsofa wa kwamfuta ta loda manhajar daga gare ta kai tsaye, don baka damar gogewa ko hana kwamfutar bukatar shigar da “Password” ma a duk sadda ta gama kunnuwa.

Idan manhajar “PC Login” bata gamsar da bukatarka ba, akwai manhajar “Kon Boot,” wacce ke gudanar da aiki irin nata.  Sai dai wannan manhajar ta kudi ce.  Ba a samunta kyauta.  Amma aiki kam ko agogo bai kai ta ba.  Kana iya loda manhajar a cikin ma’adanar filash, sai ka sake kunna kwamfutar tare da bata umarnin ta loda manhajar kai tsaye yayin da take kunnuwa.  Wannan zai kai ka cikin manhajar, inda za ka iya goge dukkan “Password” din dake cikin kwamfutar.  Da zarar ka sake kunnawa za ta mike garau, ba tare da an bukaci ka shigar da “Password” din ba.  Sai ka sake sanya wa huruminka (User Account) wata sabuwar “Password” don kariya.

Wadannan kadan ne cikin hanyoyin da mai karatu zai iya bi wajen magance ire-iren wadannan matsaloli dake tasowa sanadiyyar dabi’ar mantuwa da shagala, ko kuma kuskure da ba a rasawa a yayin tafiyar da rayuwa wajen mu’amala da na’urar kwamfuta.

Rayuwar “Password” a Gidajen Yanar Sadarwa

Bayan mai karatu ya fahimci yadda kwamfutoci ke adanawa tare da layance “Password” din da mai kwamfutar ke shigar musu, don bashi damar shiga da aiwatar da abubuwan da yake bukata, a halin yanzu za mu jirga bangaren gidajen yanar sadarwa na Intanet, don fahimtar yadda su kuma suke adana “Password” din da muke shigarwa idan mun tashi shiga shafukansu don aiwatar da abin da muke son aiwatarwa.  Abin da wannan zance ke nu shi ne, shafinka na Dandalin Facebook, idan ka tashi shiga kana shigar da “Password” dinka bayan suna ko?  In eh, a ina masu shafin Facebook ke adana wannan “Password” din naka, ta yadda a duk sadda ka tashi shiga suke iya shaida ka ta hanyar abin da kake shigarwa?  Kana shiga akwatin Imel dinka ko?  In eh, idan ka shigar da suna (username) da kalmar sirrinka (password) a karon farko, a ina masu gidan yanar suke adana bayanan, ta yadda idan ka tashi shiga suke iya shaida ka da wanda ka shigar?

Duk wani shafi da kake iya shigansa ta hanyar bayar da suna (username) da kalmar sirri (password) a Intanet, to, akwai inda masu shafin kea dana bayanan, ko makwafinsa.  Sai dai hanyoyin adanawar da kuma kwafan bayanan ne suka sha bamban.  Ya danganci tsarin da kowane gidan yanar sadarwa ke amfani dashi.  Akwai hanyoyi guda biyar ko shida masu shafukan yanar sadarwa ke amfani dasu wajen adanawa tare da kwafan bayanan masu ziyarar gidajen yanar sadarwarsu ta hanyar suna (username) da kalmar sirri (password).  Wadannan hanyoyi ne zamu yi bayani kansu daya-bayan-daya a mako mai zuwa.  A ci gaba da kasancewa tare damu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.