Ka’idojin Mu’amala da “Password” (4)

Ga kashi na hudu cikin jerin kasidun dake nazari kan “Kalmar Sirri”, wato “Password” da mahimmancinsa ga mai mu’amala a shafin Intanet. A sha karatu lafiya.

167

Yadda Muke Zaban Password

Bayan bayani kan dalilan da ke sa mutane su mallaki “Password” da mai karatu ya karanta a baya, zai dace mu ga irin yadda muke zaban “Password” a halin yanzu.  Wato, a matsayinmu na masu mu’amala da hanyoyi da kayayyakin sadarwa na zamani masu bukatar “Password”, ta yaya muke zaban “Password”?  Wannan tambaya tana da mahimmanci musamman idan muka yi la’akari da yawaita da kuma maimaituwan mu’amala da muke yi da wadannan na’urori.  Kadan ne cikin masu mu’amala dasu wadanda za a iya kebancewa da basu mallaki “Password” ba.  Amma kashi 90 cikin 100 za ka samu sun mallaka, musamman wadanda ke amfani da wayar salula wajen shiga shafukansu dake dandalin abota irin su: Facebook da Twitter da Youtube da sauransu.

Kasancewar “Password” wani abu ne da dole sai ka shigar kafin a baka damar aiwatar da abin da kake son aiwatarwa, yasa dole ga mai shi ya haddace shi.  Tunda kuwa ya shafi hardacewa ne, ba kowa ke iya hararo abin da ya haddace lokaci guda ba, musamman idan ba yawan ta’ammali yake yi dashi ba.  Misali, mutumin da ba ya amfani da “Password” dinsa sai sau daya a mako, zai fi saurin mancewa idan aka hada shi da wanda a kullum sai ya shigar da “Password” dinsa a shafi don samun shiga.  A bangare na biyu kuma, akwai dalilan mantuwa.  Wasu duk gajartan “Password” dinsu suna iya mancewa, a yayin da wasu kuma duk tsawonsa, zai yi wahala ka ga sun mance.  Wadannan dalilai ne guda biyu dake taimaka wa masu ta’ammali da “Password” wajen zabansa; mai tsawo ne ko gajere, mai saukin haddacewa ne ko mai tsauri.

Galibin masu zaban “Password” sun fi yin amfani da sunaye.  Ko dai sunansu, ko na mahaifansu, ko ‘ya’yansu, ko wasu daga cikin danginsu.  Wadannan su ne kaso mafi yawa daga cikin masu amfani da sunaye a matsayin “Password”.  Mata: ‘yan mata, da matan aure, da zawarawa musamman a Arewacin Najeriya, na cikin wannan rukuni.  Masu kokari daga cikinsu ne ke kara lamba ko lambobi a gaban sunayensu don mayar dashi “Password”.  Misali, kana iya ganin “Password” kamar haka: “jummai1” ko “hadiza21” ko “hajiya” ko “jummala” ko “talatu” ko “ibrahim00” ko “baballe” ko “ainau1” ko “zariya” ko “kanondabo” ko “katsina” ko “birninshehu”, duk a matsayin “Password.”  Bahaushe dan Dandatsa (Hacker) ba zai sha wahala ba wajen sace ire-iren wadannan “Password” din, saboda saukinsu da zamansu “gama-gari.”

- Adv -

Wasu kuma su kan yi amfani da lambobi ne zalla.  Misali, kwanan watan haihuwarsu, ko lambar wayarsu, ko lambar gidansu, ko lambar motarsu, ko su jirkita lambar wayarsu daga karshe zuwa farko, ko su cire lambobi uku na farkon lambarsu su bar sauran, da dai sauran dabaru, duk a matsayin “Password.”  A wasu lokuta kuma su kan yi amfani da lamba daya zuwa goma (1 – 10) a matsayin “Password.”  Wasu kuma suyi amfani da lamba daya zuwa shida ko bakwai ko takwas, duk dai a matsayin “Password.”

Idan muka koma bangaren harkokin rayuwa ma mutane kanyi amfani da bayanan da suka dangancesu ko suke sha’awa ko so, don mayar dasu “Password.”  Misali, a addinance, galibin daliban ilimin addini musamman, da mata, da matasa kanyi amfani da kalmomi irin su: “yaasalaam” da “assalamualaikum” da “yaaAllah” da “subhaanallah” ko “alhamdulillah” ko  wata kalma makamanciyar wadannan.  A wani bangaren kuma wasu kanyi amfani da sunayen gwarazansu a rayuwa, kamar a fagen addini ko fina-finai.  Ba abin mamaki bane ka ga matashi ko matashiya ta sa “Password” mai suna “alinuhu” ko “sanidanja” ko “safiyamusa” ko ma sunan fim na musamman, kamar: “karni2” ko “masoyanzamani” ko “katanga” ko wani suna makamancin hakan.

Wasu kuma kanyi amfani da kalmomin turanci da suka shafi muradansu a matsayin “Password.”  Wannan ya fi shahara a bangaren ‘yan mata dake soyayya da samarinsu.  Bai sayi wuri ba kaga “Password” din mace a matsayin: “myheart” ko “mylove” ko “ineedyou” ko “iwantyou” ko kuma, a mafi yawancin lokuta, kana iya cin karo da mafin girman suna: “sweetheart” ko “sweetapples” ko “mycutie” da dai sauransu.  Babban abin dariya, wasu kalmomin “Password” din ma’anarsu sai wanda ya sa su.  Kana iya cin karo da “Password” din matashi kamar su: “londonguy” ko “followme” ko “jirginmasoya” ko kuma “fezbuk”, duk akwai su.  Wani lamarin sai ya baka dariya.  Daya daga cikin kalmomin da aka fi amfani dasu a baya a duniya baki daya ita ce kalmar: “password” ita kanta.

Daga bayanan da suka gabata, za mu ga cewa galibin mutane suna zaban “Password” ne ba tare da la’akari da tsaro ba, ko mahimmancin samun “Password” mai tsauri ba.  Babban dalili shi ne, tunda dole ne sai da “Password” ake shiga shafi ko samun riskar nau’in bayanan da ake so, shi yasa mutane ke kaffa-kaffa wajen zaban abin da yake mai sauki a gare su.  Nan gaba za mu fahimci hadari ko kuskuren dake tattare da hakan, amma kafin nan, ga bayani kan ka’idojin dake dauke da siffofin “Password” musamman a cikin wannan zamani da muke ciki.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.