Kamfanin Nokia Ya Sayi Babbar Manhajar “Symbian”

Shahararren kamfanin nan mai tsarawa da kuma kera babban manhajar wayar salula da ke landan, wato Symbian zai koma hannun kamfanin NOKIA nan bad a dadewa ba.  Kamfanin NOKIA ya mallaki wannan kamfani ne sanadiyyar sayan ragowar kashi sittin da biyar na hannun jarin kamfanin, kuma masu lura da harkokin wayar salula da manhajarta na ganin wannan ba karamin yunkuri kamfanin NOKIA yayi ba, wajen mallake kasuwar wayoyin salula a duniya.

 

Wannan kamfani na Symbian dai aikinsa shi ne gina manhajojin wayoyin salula masu inganci, kuma kafin wannan mamaya da kamfanin NOKIA ya kai masa, shi ne kamfanin da yayi fice wajen samar da kayatattun babban manhajar wayar salula, wato Mobile Phone Operating System a duniya.  Domin manyan kamfanonin kera wayar salula irinsu SonyErricsson da Motorola da kamfanin Nokia, duk suna sanya babban manhajarsa cikin wasu daga cikin wayoyin salularsu.  Wani abin dawannan kamfani na Symbian ya shahara dashi har way au shi ne, kusan dukkan manyan wayoyin salula na musamman nau’in Black-berry da ire-irensa, duk suna amfani ne da babban manhajarsa.

 

Wasu daga cikin kayatattun siffofin wannan manhaja ta kamfanin Symbian sun e: samuwar hanyoyin mu’amala da fasahar Intanet, da wasikun Imel da hanyar sadarwa ta Rediyo da Talabijin da hanyoyin taskance hotuna da wakoki da kuma murya, sai tsarin aikawa da kuma karbar sakonni na text, da fasahar sadarwa ta GPRS.  Wasu kebantattun hanyoyin mu’amala da wayar salula da wannan manhaja take takama dasu basu faduwa sai mai karatu ya gansu a aikace.

 

Wannan tasa da dama cikin masu lura da bunkasar wayar salula a duniya ke ganin cewa kamfanin NOKIA na dosar mamaye kasuwar ce gaba daya.  Don a yanzu ma dai shi ne a gaba wajen kera ingantattun wayoyin salula a duniya, kuma gashi ya saye kamfani mafi girma, mai gina babban manhajar wayar salular ma gaba daya.

Baban Sadik

Baban Sadik marubuci ne, kuma mai bincike a fannin kimiyya da fasahar sadarwar zamani da tasirinsu ga al'umma a kasashen Afrika, musamman Najeriya. Ya tanadi wannan shafi ne don taskance dukkan kasidun da yake gabatarwa a shafinsa na jaridar AMINIYA mai take: "Kimiyya da Kere-kere," wanda ya faro tun shekarar 2006; shekaru goma kenan a takaice. Bayan kasidun shafin jarida, wannan shafi har wa yau yana dauke da wasu kasidun da ya gabatar a tarurruka da aka gayyace shi, ko wasu hirarraki da gidan rediyon BBC Hausa yayi dashi a lokuta daban-daban. Baban Sadik na zaune ne a birnin tarayyar Najeriya, wato Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *