Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (3)

Wannan shi ne kashi na uku cikin jerin kasidun da muke bincike na musamman kan alakar dake tsakanin kimiyyar Kur’ani da ta Zamani. A sha karatu lafiya.

540

 SIFFAR DUNIYA 

——————————

Bamu gushe ba muna ta bincike kan abubuwan da malaman kimiyya suka fada dangane da halittar duniya baki daya, da kuma gwama abin da suka fada da wanda yazo daga Al-Kur’ani mai girma, kamar yadda daya cikin masu karatu ya bukata makonni hudu da suka gabata.  A sashen da ya gabata mai karatu ya samu bayanai kan yadda wannan duniyar da muke ciki da sauran duniyoyi da halittun da ke sararin samaniya suka samo asali, da kuma hujjoji masu nuna hakan daga binciken malaman kimiyyar zamani da kuma tabbaci daga Al-Kur’ani mai girma.  A yanzu zamu ci gaba, inda zamu mayar da hankali kan siffar wannan duniya tamu; yaya take?  Shin a shinfide take sambai, da gaba ko iyaka a kowane gefe, ko kuwa ya abin yake?  Sannan, wannan rana da wata da muke hange ko gani a kullum, yaya alakarsu take da wannan duniya da muke ciki?  Kuma mai karatu zai san ko suna da ajali da aka yanke musu, ko kuma haka kawai zasu ci gaba da kasancewa.  Dukkan wannan zasu zo ne ta hanyar hujjoji daga binciken malaman kimiyyar zamani, da kuma tabbaci daga Al-Kur’ani kan haka.  Mu je zuwa!

Duniya A Mulmule Take

Al’ummomi da dama da suka shude basu gushe ba kan tunanin cewa wannan duniya tamu a shimfide take kamar faifai; ta inda duk ka dosa, zaka samu makura ko gaba.  Kamar dai yadda saman tebur yake, ko saman kamfai ko saman duk wani shimfidadden abu.  Wasu ma har tsoron zuwa yawo suke da nisa, don tsoron kada su “afka” karkashin kasa, a cewarsu.  A kan wannan  tunani da akida ake, sai cikin shekarar 1597, lokacin da wani malamin kimiyya mai suna Francis Drake ya yi kokarin zagaye duniyar ta teku, sannan ya tabbatar da cewa lallai duniyar ba kamar yadda ake tunani bane; a mulmule take, kamar kwai.  Shi yasa wasu lokuta idan kaje karshen gari, ko bakin teku, sai kaga kamar sama ta hade da teku ne.  Drake yayi wannan bincike ne cikin shekarar 1597, wato shekaru 412 kenan a yau.  Dangane da Kur’ani kuwa, sai mu ga cewa hakan yazo ne bayan saukarsa da shekaru dubu daya da goma shatakwas (1,018).  Kuma har yanzu, kamar yadda kowa ya sani, a kan sakamakon wannan “sabuwar” bincike ake.  To me Kur’anin ya fada kafin wannan bincike?

Tabbaci Daga Kur’ani

A cikin Surorin Kur’ani da yawa, Allah Ya nuna mana cewa lallai wannan duniya tamu a mulmule take, kamar kwai.  Zamu fahimci hakan ne daga tsarin alakar da ke tsakanin shigan dare da shigan yini (ko rana, kamar yadda muka saba fada). Ga wasu daga cikin hujjoji nan:

“Ashe ba ku gani ba, lalle Allah Yana shigar da dare a cikin yini, kuma Yana shigar da yini a cikin dare…?” (Luqman:29)

Cewa ana shigar da dare a cikin yini, da kuma yini a cikin dare, kamar yadda muka sani, hakan na faruwa ne a hankali – kadan kadan –  ba wai lokaci daya ba.  Kuma wannan ke nuna mana cewa duniyar ba a shimfide sambai take ba.  Da haka ne, to da lokaci daya zamu rika shiga yini, haka lokaci guda zamu rika shiga dare.  Ma’ana da kowanne zai zo ne da haske ko duhunsa lokaci guda, kamar yadda kake samun haske da zarar ka kunna tocila, ko kashe ta.  A wata ayar Allah yayi amfani da Kalmar “nannadewa”, inda yace:

“Ya halitta sammai da kasa da gaskiya. Yana nannade dare a kan rana (yini), kuma yana nannade rana (yini) a kan dare…” (Zumar:5)

Duk da cewa wasu na amfani da Kalmar “shigarwa” a ma’anar kalmar “kawwara”.  Suna hakan ne wajen isar da ma’ana.  Amma asalin ma’anarta na nufin “nannadewa” ne.  Duk kuwa abin da aka ce ana nannade shi, to a siffar da’ira yake, ko kuri, ko kuma mulmule yake.  Idan kuma aka ce an nannade wani abu a tare dashi, to an shigar dashi ciki kenan.  Kamar dai yadda mai sanya rawani ke nannade rawaninsa, wani sashe a saman wani.  Haka kuwa bazai faru ba dangane da rana da dare, sai muhallin da haske ko duhunsu ke riska ya zama mulmulalle ne ko curarre, mai siffa irin ta kwai.

Rana Da Wata Na Juyawa

Kafin kwarewar turawan Turai yayi nisa cikin binciken kimiyya, akidarsu dangane da rana ita ce, a tsaye take cak!  Duk sauran halittun da ke makwabtaka da ita kuma suna jujjuyawa ne a cikin falakinsu, don kewaye ta.  Har a karni na biyu haka ake tafiya a yammacin duniya. A cikin shekarar 1512 ne wani malamin kimiyya mai suna Nicholas Copernicus ya samar da wannan ka’ida ta ilimi mai suna Heliocentric Theory of Planetary Motion, wanda ke nuna cewa dukkan sauran halittun da ke sararin samaniyar duniya baki daya suna jujjuyawa ne a cikin falakinsu da ke gewaye da rana. Amma ita rana a tsaye take cak, ba ta motsawa.  Haka ma binciken da Yohannus Keppler ya tabbatar, cikin shekarar 1609.

Wadannan sakamakon bincike ne suka fara wayar wa turawa da kai, suka dada samun fahimta kan yadda manyan halittun da ke sararin samaniya ke juyawa, suka kuma basu damar fahimtar “juyin-wainar” da dare da yini ke yi a cikin falakinsu. Na tabbata idan ba yanzu ba, da dama cikinmu (wadanda suka yi sakandare shekarun baya), an karantar da mu wannan ka’ida ta ilmin kimiyya da ke nuna cewa “dukkan sauran halittun da ke sararin samaniya na kewaye da rana ne, a halin kewayar da suke yi.”  Amma a yanzu kam, malaman kimiyyar sararin samaniya, wato Astronomers, sun warware wancan ka’ida ta Nicholas da Keppler, inda suka tabbatar da cewa lallai rana ma na jujjuyawa a nata falakin, ba a tsaye cak take ba guri guda.  To me Kur’ani ya fada?

Tabbaci Daga Kur’ani

Idan muka koma cikin Suratu Ambiya’, zamu samu tabbaci da ke nuna cewa da rana da wata, duk kowanne daga cikinsu na da nashi falaki (ko hanya, ko magudana) da yake bi, da yanayin gudu ko saurinsa.  Ga abin da Allah yace:

- Adv -

“Kuma Shi ne wanda Ya halitta dare da rana (yini), da rana da wata, dukkansu a cikin wani sarari suke iyo.” (Ambiya’:33)

Wannan ke nuna cewa lallai akwai falaki ko tafarki da kowannensu ke bi a halin iyonsa.  An ambaci dare da yini a nan don nasaba da ke tsakaninsu da rana da kuma wata.  Har wa yau, tsarin tafiya ko juyawa da suke yi a cikin wannan falaki nasu ya sha bamban.  Kowanne da irin saurin da ya kamace shi yake tafiya.  Dangane da haka Allah Ya sake cewa:

“Rana ba ya kamata a gareta, ta riski wata. Kuma dare ba ya kamata a gareshi ya zaman mai tsere wa yini. Kuma dukkansu a cikin sarari (falaki) guda suke iyo.” (Yasin:40)

Kalmar “iyo” ko “sulmuya” da Allah yayi amfani dashi (wato “Yasbahoon”) zai sa wani yayi tunanin ko akwai ruwa ne a sararin samaniya da har rana da wata suke yin iyon a cikinsa.  A a, ba haka lamarin yake ba.  Kalma ce mai fadin sha’ani, ya kuma danganci yadda aka yi amfani da ita a jimla. Idan aka yi amfani da ita kan mutum a cikin ruwa, yana nufin yana iyo kenan.  Idan a kasa yake, ana nufin yana tafiya kenan.  Haka rana da wata, su ma tafiya suke yi, a cikin muhallinsu a sararin samaniya.  Sai dai kowanne daga cikin su da tafarkinsa daban.  Kuma malaman kimiyyar sararin samaniya a yanzu sun tabbatar da cewa rana kan gama kewayenta ne – daga tashar farawa zuwa tashar tikewa (ko “axis”, a turance) – cikin kwanaki ashirin da biyar, a kowane wata.  Kenan, cikin kwanaki ashirin da biyar take yin kewaye daya.  Shi kuma wata yana kewaye wannan duniya tamu ne cikin kwanaki ashirin da tara da rabin kwana (29½).  Dangane da haka Allah yace:

“Kuma da wata, mun kaddara masa manziloli, har ya koma kamar tsumagiyar murlin dabino, wadda ta tsufa.” (Yasin:39)

Wadannan “manziloli” da Allah ya fada, su ne masaukai da yake sauka a cikinsu a kullum, har ya gama zagayensa cikin wadancan kwanaki da suka gabata.

Nan Gaba Rana Zata Bice

Malaman kimiyyar zamani suka ce rana na dauke ne da wasu sinadarai (wato hidirojin da hiliyum), wadanda ke gudanuwa a cikinta, kuma suke baiwa halittu sinadarai masu amfani cikin hasken da suke narke cikinsa idan ranar da bullo.  Suka kuma ce wadannan sinadarai na kumshe cikin rana ne tun shekaru wajen biliyan biyar da suka wuce.  Wannan ke nuna mana cewa, tunda asali babu wannan halitta ta rana, to a tabbace yake cewa nan gaba haskenta zai bice, ta daina haske, har a rasa ta.  Wannan tabbaci ya fito daga bakin malaman kimiyyar zamani, kamar yadda Mark Garlick ya fada cikin littafinsa mai suna The Story of the Solar System.  To me Allah ya ce kan haka?

“Kuma rana tana gudana ne zuwa ga wata matabbata nata. Wannan kaddarawar Mabuwayi ne, Masani.” (Yasin:38)

Cewa rana tana gudana zuwa wata matabbata, ishara ne ga lokacin da Allah Ya haddade mata.  Kamar yadda yake tabbatace cikin binciken da mujallar Scientific American ta fitar a shekarar 2004, da ke nuna cewa taurari da dama sun kwanta dama, wasu sun tsufa, wasu kuma yanzu suke fara rayuwarsu.  Mujallar tace hatta rana ma, akwai tabbacin kwanakin ta na tafe.  Domin ta tsufa tukuf.  Amma saboda masu binciken ba su kawo tashin kiyama a zuciyarsu ko imaninsu, suka ce idan rana ta kare kwanakinta, wata za a samu ta maye gurbinta.  Amma ga kowane musulmi mai imani, wannan shirmen banza ne.  Wannan matabbata da Allah ya fada ba wani abu bane illa adadin kwanakin da aka haddade mata.  Ko kuma, a daya bangaren – kamar yadda yazo cikin Hadisin Bukhaari, wanda Abu Dharril ya ruwaito – karkashin al’arshin Ubangiji.  Zuwa karkashin al’arshin Allah da rana ke yi a duk faduwanta ne, amma kwanakinta na karshe suna zuwa ne da zarar kiyama ta tsaya.  Da zarar wannan rana ta daina fitowa, ko mun daina ganinta, to alama ce da ke nuna cewa lallai duniya tazo karshe.

Wannan shi ne abin da malaman Tafsirin Kur’ani irinsu Ibn Kasir da Aliyyus Saabooni suka fada cikin sharhin ma’anar wannan aya.  Sabooni yace:

“Ai da wata aya kuma garesu, ita ce rana da ke tafiya da kudurar Allah, a cikin wani falaki da baza ta taba wuce shi ba, ko ketare shi, cikin wani zamani da za ta tabbata a cikinsa (tana wannan tafiya). Kuma da wani lokaci da za ta tike a cikinsa. Shi ne ranar tashin kiyama, lokacin da tafiyarta zai yanke sanadiyyar rushewar duniya baki daya.” 

Haka Al-Iman Ibn Kasir ma yace:

Lallai abin nufi da ‘matabbatar ta’, shi ne lokacin tikewar tafiyarta, kuma shi ne ranar kiyama. Lokacin da (tsarin) tafiyarta zai rushe, ta daina motsi, a kuma nannade ta; wannan duniyar kuma ta zo karshe.”

Don haka, rana tana da kayyadadden lokaci da aka ajiye mata, wanda idan ya kai, za ta bice, haskenta ya shafe, a nannade ta, kamar yadda Kur’ani ya sanar.

Allah Ya mana jagora!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.