Kimiyyar Lantarki a Sawwake (1)

A yau za mu fara bincike na musamman kan abin da ya shafi kimiyyar lantarki da yadda makamashin lantarki ke samuwa, duk a mahangar kimiyya. Wannan shi ne kashi na daya mai dauke da mukaddima. A sha karatu lafiya.

756

Mabudin Kunnuwa

Bayan kwashe makonni sama da goma shabiyar muna amsa tambayoyi da yin bayani kan tsokacin masu karatu, a wannan mako dai na lura cewa idan muka ci gaba da amsa tambayoyi kadai, shafin na iya gudanuwa na tsawon lokaci ba tare da an tattauna wani abu ba; domin a duk mako tambayoyi na dada karuwa ne.  Don haka naga dacewar dakatar da amsa tambayoyi.  A yanzu sabon tsarinmu shi ne, za mu rika amsa tambayoyi ne bayan gama maudu’in da muka dauka; ko da kuwa zai kai mu makonni goma ne.  Illa dai tabbacin da zan iya baiwa masu karatu shi ne, zan rika amsa tambayoyi ko bukatun masu neman kasida ko karin bayani na gaggawa  ne ta Imel.  Amma abin da ya shafi tsokaci, sai mun gama maudu’in da muka dauka sannan zan hada da sakonnin masu neman kasidu in buga.

Don haka, duk mai neman wata kasida ta musamman, yana iya aiko da bukatarsa ta adireshinmu na Imel.  Akwai wadanda suka aiko da sakon bukata ta tes, ba tare da adireshin Imel ba.  Zai yi wahala a wannan yanayi in iya aika maka kasida wadda mafi karancinta shafi uku ne, ta hanyar tes a wayar salula.  Dole sai ta Imel.  Sai a kiyaye.

A yau cikin yardar Allah ga mu dauke da maudu’i na musamman kan fannin kimiyyar lantarki; wani fannin da bamu taba yin bincike a cikinsa ba, duk da mahimmancinsa ga rayuwar al’umma da tattalin arzikinsu.  Rubutu kan wannan fanni na lantarki zai dauke mu wasu makonni nan gaba.  A yau zamu yi bayani ne kan mahimmancin wannan fanni, bayan takaitaccen bayani daga asalinsa.  Sannan muyi bayani kan madaukan lantarki; ma’ana: mahallin da lantarki ke gudanuwa kenan.  A gaba mu kawo bayanai kan nau’ukan sinadaran lantarki.  Sai kuma bayani kan yadda sinadarin maganadisun lantarki ke gudana a mahallinsa.  Daga cikin bincikenmu har wa yau, mai karatu zai ci karo da bayani kan farantin makamashin lantarki, wanda a harshen Turanci ake kira: “Electrical Circuit.”   Wannan faranti shi ne hakikanin abin da idan ka fahimce shi a ilimin lantarki, ka kusan kure fannin.  Domin duk wata na’urar dake dauke da sinadarai ko makamashin lantarki a wannan zamani, tana dauke ne da wannan faranti.  Kada in cika ku.

Daga cikin bincikenmu za mu kawo bayanai kan abubuwan da ake sarrafa su don samar da wutar lantarki a duniyar yau.  Wannan zai zo ne bayan ‘yar takaitacciyar karatun tarihi da za mu yi kan asalin lantarki na zamanin da; tsakanin wanda ke samuwa daga sararin samaniya da wanda ke samuwa daga halittun dake rayuwa a teku.  Za mu ci karo har wa yau da bayani kan tarihin lantarkin zamani; su wa da wa suka assasa wannan fanni a duniyar yau?  Kasidar ba za ta kare ba sai masu karatu sun san yadda ake kididdige kima da yawan wuta ko makamashin lantarki dake gudanuwa a na’urorin sadarwa na zamani masu amfani da wutar lantarki.  Wannan zai kaimu ga bayani kan ka’idojin ilimin kimiyya da wasu masana suka assasa don karantawa da nazarin wannan fanni a kimiyyance (Scientific Laws), irin su Ohm, da Fradays’ Laws.  A karshe, masu karatu za su samu bayanai kan asalin kwan lantarki ko kayayyakin da ake amfani dasu wajen haska wutar lantarki a dakuna da gidaje da ma’aikatu ko masana’antu.  Su waye suka samar dasu a asali?

Wadannan, a takaice su ne kadan daga cikin abubuwan da wannan maudu’i namu zai kunsa in Allah ya so.  A daya bangaren kuma, bazan yi magana a kan matsalolin wutar lantarki a Najeriya ba.  Don haka, kada a rubuto mini tambaya kan wannan maudu’i.  Kasidar za ta mayar da hankali ne kan fannin a ilimance, da nazarce.  Manufar hakan kuwa ita ce ne don yada ilimi, ba muhawara cikin siyasar samar da wutar lantarki ba a Najeriya.  Da fatan za a kiyaye wajen aiko tambayoyi ko tsokaci.

- Adv -

Asali da Samuwa a Takaice

Wutar lantarki ko makamashin lantarki na daga cikin nau’ukan makamashi da Allah ya samar don moriyar dan adam a wannan duniya.  Kamar yadda na tabbata mai karatu ya ji wa’azi daga malaman addini, cewa Allah bai halicci wata halitta ba face sai da ya tanada mata arzikinta kafin lokacin halittarta.  Daga cikin wannan arziki akwai samuwar duk wani abin da zai taimaka wa dan adam yin rayuwa mai inganci a wannan duniya.  Duk wannan gata Allah ya masa ne, don dan adam ya samu natsuwa har ya bauta wa Allah hankalinsa a kwance.

Daga cikin makamashin da Allah ya tanada wa dan adam a wannan duniya, gabanin bayyanar ilimin kimiyya ko masana kimiyya su gano irin na zamanin yau.  Daga cikinsu akwai sinadaran lantarki dake samuwa daga walkiya (hasken dake bayyana kafin samuwar cida) dake darsuwa a sararin samaniya.  Akwai kuma sinadarai na musamman da Allah ya samar a mahallin duniyar nan da muke rayuwa.  Wadannan sinadarai na madda (Atoms) su ne suke haduwa da juna a bisa kaddara da tsari da kintsin Ubangiji, don samar da caji ko wutar lantarki a mahallinmu.  Sinadaran kuwa su ne: “Protons,” da “Neutrons,” da kuma “Electrons.”  Hadakar wadannan sinadarai ne ke samar da makamashi ko wutar lantarki.  A zamanin da al’ummomi kan hada abubuwa daban-daban don samar da wannan nau’in makamashi.

Bayan wadannan har wa yau, tarihi ya nuna cewa al’ummomin da suka gabata musamman na kasar Masar da daular Girka na cikin wadanda suka fara gano samuwar makamashin lantarki daga jikin wasu daga cikin dabbobin dake cikin ruwa, musamman kifaye.  Akwai nau’in kifi da ake kira: “Electric Fish,” wanda ke dauke da sinadaran lantarki a jikinsa.  Irin wannan kifi idan ka taba shi nan take zai ja ka, kamar yadda wutar lantarki ke jan wanda ya taba shi ba tare da wani shamaki ba.  Irin wannan nau’i na kifi shi ake kira: “Electrogenic Fish.”  A daya bangaren kuma akwai wadanda su ba sa dauke da wannan caji na lantarki a jikinsu, sai dai kuma duk inda akwai cajin lantarki ko sinadaran lantarki, suna iya fahimtarsa.  Wadannan su ake kira: “Electro-receptive Fish.”  Masana kimiyyar lantarki suka ce ire-iren kifayen da ke dauke da sinadaran lantarki suna da yawa, sannan an kiyasta karfin cajin lantarkin dake jikinsu na tsakanin 60 zuwa 600 ne a ma’aunin lantarki na “Volts” (60 – 600volts).

Bayan dabbobin ruwa da sinadaran mahalli dake haddasa samuwar makamashin lantarki, jikin dan adam ma yana dauke da sinadaran lantarki.  Wannan bangare kuwa shi ne kwakwalwarsa.  Idan mai karatu bai mance ba, a doguwar kasidarmu mai take: “Asalin Tunani: Tsakanin Kwakwalwa da Zuciya,” mun nuna cewa kwakwalwar dan adam na dauke ne da nau’ukan jijiyoyi daban-daban.   Daga cikinsu akwai jijiyoyin dake dauke da sinadaran lantarki masu suna: “Neurons.”  Wadannan jijiyoyi masu dauke da tubalin halitta (Neural Cells), su ne ke aikin sadar da bayanai tsakanin bangarorin kwakwalwar dan adam da sauran sasannin jikinsa.  Malaman kimiyyar kwakwalwa na wannan zamani sun tabbatar da cewa akwai ire-iren wadannan jijiyoyi masu dauke da sinadaran lantarki sama da biliyan dari (100,000,000,000) a jikin kowane dan adam mai rai.

A wannan zamani kuma da muke rayuwa, fannin lantarkin da muke amfana dashi ya samo asali ne daga gaggan masana guda uku.  Wadannan masana kuwa su ne: Benjamin Franklin, daya daga cikin masana fannin kimiyya a kasar Amurka, wanda ya fara kwatanta cewa: walkiya dake samuwa daga sararin samaniya yayin da ake ciba, yana dauke ne da sinadaran lantarki.  Ya gudanar da bincike na musamman a kan haka, don tabbatar da ikirarinsa.  Sai kuma Thomas Edison, wanda aka fi danganta wannan fanni gare shi, shi ne babban sanadi wajen samar da kwan lantarki, don janyo makamashin lantarki da amfana dashi a gidaje.  Sai mutum na uku, wanda ya samar da tsarin samar da makamanin lantarki da yada shi ko rarraba shi.  Wannan masani kuwa shi ne Nikola Tesla.  Ya rayu ne a karni na 19.  Bayan wadannan mutane, akwai daruruwan jama’a da suka yi ruwa suka yi tsaki wajen ganin fannin ya habbaka kamar yadda yake a halin yanzu.  Cikin dacewar Ubangiji, za mu rika kawo sunayensu da abin da suka yi, lokaci zuwa lokaci, idan bukata ta kama.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. NAZIFI A.A BAHIRAWA says

    SLM MLM INA SO KABANI DAMA IN DAN SAMUN WASU ILIMAI DAGA GAREKA.

Leave A Reply

Your email address will not be published.