Kimiyyar Lantarki a Sawwake (2)

Wannan shi ne kashi na biyu cikin jerin kasidun da muke kwararowa kan kimiyyar lantarki. A sha karatu lafiya.

569

Tasirin Lantarki Ga Rayuwar Yau

Abu ne sananne cewa rayuwar yau sai da makamashi  ko wutar lantarki.  Idan ka kebance kasashe masu tasowa ko kasashe matalauta,  a sauran kasashen turai da amurka, kusan duk kauyuka akwai wutar lantarki, ba ma ta birane ake ba.  Wutar lantarki ba wani kayan gabas bane a wajensu.  Amma duk da haka, a kasashenmu ma kusan duk rayuwar jama’a ta ta’allaka ne da wutar lantarki.  Tabbas akwai kauyuka da ko da wutar lantarki ko babu za su iya rayuwa yadda suka saba, amma a galibin biranenmu wutar lantarki dole ce.  Meye dalili?

Duk da cewa ba duk sa’o’in yini ake samun wutar lantarki ba, da yawa cikin jama’a sun tanadi na’urar samar da wutar lantarki, wato: janareta kenan.  Idan ba ka girki da na’urar dumama abinci mai aiki da makamashin lantarki, kana bukatar jin labaru ta hanyar rediyo ko talabijin ko jaridu.  Dukkan wadannan kafofi suna bukatar wutar lantarki don gundanuwa.  Kamfanin jarida na bukatar kwamfutoci, da na’urar dab’i (Printer), da na’urar sawwara bayanai (Photocopier ko Scanner), da wutar kwayeyen da za su haskaka ginin da ma’aikatan ke aiki, da na’urar sanyaya ofishi.  Dukkan wadannan, su kuma, suna bukatar wutar lantarki don gudanar da ayyukansu.  Idan an gama kintsa shafukan jaridan gaba daya, sai an tura wa babbar na’urar da za ta dabba’a su a matsayin jarida, wanda ita ma tana bukatar wutar lantarki don gudanuwa.

Idan ka koma bangaren kafar talabijin ma haka lamarin yake, ko ma fiye.  Daga sadda aka fara daukan shiri har zuwa lokacin gabatar dashi, komai na bukatar wutar lantarki.  A bangaren rediyo ma haka abin yake.  Ba ma wadannan kadai ba, na’urar talabijin da rediyon da za ka kunna su kansu suna bukatar wutar lantarki; ko dai ta hanyar babbar kafar samar da wutar ko ta hanyar janareta ko batiri.

- Adv -

Idan muka koma bangaren samar da lafiya kuma, wannan sai dai ayi shiru.  Babu asibitin da zai iya rayuwa a yau, a Najeriya, sai da wutar lantarki.  Tabbas akwai labaru dake nuna cewa wasu asibitocin kan gudanar da tiyata ta amfani da fitila!  Wannan hadari ne mai girman gaske, idan ma da gaske hakan na faruwa.  Amma duk da hakan ma, ita kanta fitilar, musamman idan wacce ke taskance makamashi ce (Rechargeable), dole tana bukatar wutar lantarki.  Idan ka koma wajen masu gwajin jini a dakunan bincike na asibiti (Laboratory), dole sai da wutar lantaki.  Tabbas akwai nau’ukan gwajin da za ka iya yi (na Maleriya) ba tare da wutar lantarki ba.  Sai dai wannan kadan ne cikin kadan.  Kuma galibin masana na ganin ire-iren wadannan gwaje-gwaje ba lalai bane a samu natija cikakke ko madogara mai inganci.  Dakunan ajiye gawawwaki sai da wutar lantarki.  Dakunan ajiye marasa lafiyar dake cikin halin ni-‘yasu (Intensive Care Unit), sai da wutar lantarki.  Sannan, a karshe, ginin asibitin gaba dayansa yana bukatar haske don gudanar da aiki cikin lumana da tsari.  Wannan haske bai samuwa ta dadi sai da wutar lantarki.

Mu koma bangaren siyasa da shugabanci.  Ofisoshin hukuma dole sai da wutar lantarki.  Eh, kana iya cewa ai a ofishin karamar hukumarku babu wutar lantarki.  Wannan na wucin gadi ne.  Amma in da za a bi ka’ida kowa yazo aiki kamar yadda doka ta tanada; daga karamin ma’aikaci zuwa babba, duk a taru a lokaci guda, dole sai an tanadi wutar lantarki.  Domin aiki bazai gudanu ta dadi ba.  Balle mu koma bangaren ma’aikatun jiha ko na tarayya.  Wutar lantarki a wadannan wurare jazamun ne!  in baka yarda ba, ka taba tunanin a ce ba wuta a Villa, gidan shugaban kasar Najeriya?  Ka taba tunanin ba wuta a gidan ko ofishin Gwamnan jiharku?  Ko ka taba tunanin rashin wutar lantarki a ginin majalisun jihohi da na tarayya?  Idan baka taba yi ba watakila sabo da rashin yadda wuraren suke, Villa gida ne kuma ofishi ne na shugaban kasar Najeriya.  Dole sai da wutar lantarki.  “Government House”, kamar yadda ake kira a jihohi, gida ne (ga wasu gwamnonin) kuma ofishi ne ga Gwamnan jihar.  Dole sai da wutar lantaki.  Ginin majalisu na jihohi ma nan ne ake taruwa don tattaunawa kan dokokin da za a yi wa ‘yan jihar.  A bangaren majalisar tarayya kuma dake Abuja, gini ne na ofisoshin (don akwai ofisoshi sama da 100) ‘yan majalisun tarayya dake tattauna hanyoyin samar da dokoki ga ‘yan Najeriya.  Zama a wuri irin wannan sai da wutar lantarki.

Mu dawo kan daidaikun ‘yan Najeriya; wayoyin salularmu sai da caji.  Cajin nan bai samuwa sai ta amfani da wutar lantarki.  Da yawa cikinmu mun gwamnace a ce wayoyinmu akwai caji, ko da babu wuta a gidajenmu.  Za mu iya kwana cikin duhu. Ba wannan kadai ba, motarmu ma sai da wutar lantarki.  Sosai kuwa!  In baka gane ba, cire wayar dake saman batirin motar ka gwada tayar da ita ka gani ko za ta tashi.  Shiru za ka ji, wai almajiri ya ci shirwa.  To, kaddara cewa motocin dake shawagi a kan titunan kasar nan batiransu sun shanye a lokaci guda!  Ya salaam! Me zai faru?  Komai zai tsaya cak.  Saboda batirin mota na dauke ne da sinadaran lantarki.  Shi kanshi batirin yana bukatar caji, shi yasa ma bature ya masa abin da ke caja shi a yayin da motar ke tafiya ko take kunne.  Wannan na’ura kuwa ita ce na’ura mai suna: “Alternator” dake cikin injin motar.  Da zarar babu wannan na’ura, batirin motarka zai shanye, duk tsawon zamani.  Idan kuwa ya shanye, to, babu abin zai caja shi.  Ka ga kuwa ashe dole sai da wutar lantarki.

A galibin birane kanana da manya a wannan kasa tamu, ana gina rijiyoyi na zamani da ake amfani dasu a gidaje.  Wadannan rijiyoyi suna dauke ne da na’urar dake janyo zuwa cikin rumbun dake taskanceta.  Wannan na’ura tana bukatar wutar lantarki da zai motsa ta don aiwatar da wannan aiki.  Idan ka koma bangaren manomanmu na karkara musamman masu noman rani, haka lamarin yake.  Na’urar janareta ce ke janyo musu ruwa daga gulbi ko kududdufi ko korama ko kogi, don shayar da shuke-shuke.  Wannan na’ura ita ma dole tana bukatar wutar lantarki.  Ta ko ina ka duba haka lamarin yake.

Daga bayanan da suka gabata, mai karatu zai fahimci cewa lallai rayuwa a yanzu dole sai da wannan makamashi na wutar lantarki.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.