Kimiyyar Lantarki a Sawwake (3)

Wannan shi ne kashi na uku cikin jerin kasidun da muke kwararowa kan kimiyyar lantarki. A sha karatu lafiya.

530

Sanayya kan Lantarki

A baya masu nayi mana mukaddima ne kan mahangar da darasinmu zai dauka kan wannan maudu’i.  Na yi bayanin kadan daga cikin tarihin wannan fanni a takaicen-takaitawa, da bangarorin da za mu dauka.  A wannan karo in Allah Yaso za mu kutsa cikin dakin karatu don bayanin ma’ana da sinadaran da suke haduwa don samar da haske ko makamashin lantarki.  Mai karatu zai ji bayanin wani iri, saboda kalmomin da zan yi amfani dasu ba kalmomi ne da aka saba ji ba; ni ne na kirkiresu, don kokarin sawwake fahimtar sakon da nake son isarwa.

Ma’anar “Lantarki”

Kalmar “Lantarki,” a yadda muke amfani ko furuta ta a harshen Hausa, kalma ce da ta samo asali daga harshen turanci, wato: “Electricity,” wacce ita kuma ta samo asali ne daga kalmar “Electron,” wato asalin sinadarin madda da Allah ya hore a mahalli ko sahar wannan duniya, don amfanin dan adam.  Malaman kimiyyar lantarki sun hadu kan cewa bayar da ma’anar wannan kalma a ilmance abu ne mai wahala, saboda gamewa da sarkakiyar dake cikin kalmar wajen ma’ana da abubuwan da ta kunsa.  Ma’anar da ake baiwa kalmar kawai it ace: “fanni ne dake lura da gudanuwar makamashin lantarki daga mabubbugarsa zuwa inda ake son amfani dashi.”

Misali, idan ka jawo wutar lantarki zuwa cikin gidanka daga magudanarsa (na’urar Transformer ko asalin magudana inda ake samar da ita), sannan ka jona kwamfuta ko talabijin ko akwatin rediyonka ta amfani da waya ta musamman, sannan ka kunna don amfanuwa da na’urar, ka aiwatar da tsarin lantarki kenan.  Wannan ke nuna cewa ma’anar kalmar “Lantarki” na damfare ne da samar dashi; daga magudana zuwa inda za ayi amfani dashi.  Wannan a bisa tsarin samarwa da sarrafa makamashin lantarki na zamani kenan, ba wanda ke samuwa a mahalli kai tsaye ba.

Sinadaran Lantarki da Dabi’unsu

Sinadarai ko makamashin lantarki, kamar yadda bayani ya gabata a baya, su ne abubuwan da ke haduwa da juna wajen samar da wutar lantarki.  Allah Ya samar da wasu maddodi (Atoms) na kimiyya a mahallin da muke rayuwa.  Wadannan maddodi na dauke ne da wasu madda nau’uka daban-daban, masu sunaye da dabi’u daban-daban.  Daga cikin wadannan nau’ukan sinadarai akwai guda uku, wadanda su ne ke da alhakin samar da, ko haddasa samuwar makamashin lantarki a mahalli.  Kashi na farko ana kiransu: “Electrons,” wadanda daga sunansu ne aka samu sunan wannan fanni da muke zance a kai.   Kashi na biyu ana kiransu da suna: “Protons.”  Sai kashi na uku da ake kira: “Neutrons.”

Kamar yadda bayani ya gabata, wadannan sinadarai ko maddodi na kimiyya kowannensu yana da dabi’a.  wadannan dabi’u su ake kira: “Atomic Properties” a harshen fannin lantarki.   Daga cikin dabi’ar lantarki akwai “caji”, ma’ana karfin tasirinsa kenan a inda aka same shi.  Wannan shi ake kira: “Charge” a harshen turancin lantarki na zamani.  Wannan dabi’a ta caji ana iya kiyasta ta, da kuma kididdige karfinta.  Wannan ne ma yasa kowace irin na’urar lantarki take da iya kimar makamashin lantarkin da za a iya jona mata.  Idan ka sayi talabijin ko akwatin rediyo, ko kwamfuta, akwai iya kimar wutar da za ta iya dauka an rubuta a jikinta.  Da zarar ka bude kundin da tazo dashi (Manual), za ka ganinshi a rubuce cikin jerin siffofin da dabi’un na’urar.  An maka haka ne don kada ka jona mata wutan da yafi karfinta ta kone.  Idan haka ta faru, ba ruwansu; baza su biyaka ba, domin babu garanti (Warranty) a wannan yanayin.

- Adv -

Caji, wanda shi ne dabi’ar lantarki, ya kasu kashi biyu; akwai caji mai kari, wato: “Positive Charge” kenan, sannan akwai caji mai ragi, ko kace: “Negative Charge” kenan.  Akwai nau’i na uku, wanda ba a cika sanya shi cikin lissafi ba, amma yana nan.  Shi ne hakikanin wanda ke kulla zumuncin dake samar da makamashin lantarki a tsakanin maddodin da bayaninsu ya gabata.  Wannan nau’i na uku na kira shi: “Holoko.”  Aikinsa shi ne daidai nau’ukan caji biyu (kari da ragi), don samar da abin da za a yi amfani dashi na makamashi.  Kuma shi ne ake kira: “Neutral” a harshen turanci.

Shi wannan sinadari na caji shi ne asali ko madarar makamashin lantarki.  Yana karuwa kuma yana raguwa.  Ya danganci yanayi ko mahallin da ake samar da shi.  Ana iya rarraba.  Ana iya takaita shi.  Ana iya kambama shi.  Ana iya sarrafa shi.  Sannan ana iya taskance shi, don amfani dashi a wani lokaci na daban.

Madaukan Caji da Titinsa

Cajin lantarki bazai samu har a iya amfani dashi ba sai anyi amfani da madaukansa.  Wadannan madaukai su ake kira: “Charge Carriers.”  Wadannan madaukai dai su ne sinadaran nan guda uku.  Da “Electron,” da “Proton,” da kuma “Neutron.”  Sinadarin “Electron” na dauke ne da caji mai ragi, wato: “Negative Charge” kenan, ko ( – ), kamar yadda yake rubuce a jikin batir.  A nasa bangare, sinadarin “Proton” na dauke ne da caji mai kari, wato: “Positive Charge” kenan ko ( + ), kamar yadda na sanar a baya.  Sai kuma sinadari na karshe wato: “Neutron,” wanda na kira “Holoko,” ko kuma (  ).  Ba wai holoko irin wanda Bahaushe ya sani ba, wannan holoko ne mai tasiri.  Domin rashinsa na haddasa rashin lantarkin ko kuma samunsa ya haifar da barna.

Alakar dake tsakanin wadannan sinadarai shi ne ke samar da caji, wanda ke samar da makamashin lantarki.  Amma kafin makamshin ya isa inda ake bukatarsa, sai an samu abin da zai ingiza shi.  Dole ana bukatar daidaito na adadi a bangaren sinadaran dake da caji mai kari da caji mai ragi, don ingiza wutar lantarki daga magudana zuwa inda ake bukatarsa.  Don haka, idan aka samu sinadarin “Proton” guda 20, amma na “Electron” guda 15, ko kasa da haka, to, ba su iya ingiza cajin lantarki ga mabukatarta.  Dole sai an samu daidaiton adadin sinadari a kowane bangare.

Wannan tsari mai dauke da tilascin daidaiton adadin sinadarai kafin ingiza cajin lantarki zuwa inda ake bukatarsa, yana dauke ne cikin ka’idar kimiyyar lantarki mai take: “Electrostatic Force.”  Abin da wannan ka’ida ke cewa kuwa shi ne: “kafin samun cajin lantarki mai inganci, sai an samu daidaito a tsakanin sinadaran caji masu akasi da juna.”  Kuma ita ka’idar da ake kira: “Coulomb’s Law.

Karkashin wannan ka’ida, an gano cewa: caji mai kari ( + ) da caji mai ragi ( – ) idan suka hadu, sukan janyo juna ne, don bayar da sinadaran makamashin lantarkin da za a iya amfani dashi.  A daya bangaren kuma, an gano cewa caji mai kari ( + ) idan ya hadu da wani caji mai kari ( + ), tunkude juna suke yi.  Haka abin yake idan caji mai ragi ( – ) ya hadu da wani caji mai ragi ( – ) dan uwansa, sukan tunkude juna ne.  Wannan ke nuna cewa a fannin kimiyyar sinadarai na lantarki, sinadarai masu kama da juna ko masu dabi’a iri daya, ba sa zama wuri daya da jinsinsu.   Sinadarai masu akasin dabi’a ne kadai ke jituwa da juna wajen samar da karfi don ingizo abin amfani.

Wannan ya sha bamban da dabi’un mutane a matsayin jinsi.  Kamar yadda hadisi yazo daga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi), wanda Imamu Muslim ya ruwaito, cewa su mutane suna jituwa ne da wadanda suke da dabi’a iri daya dasu.  Sannan suna sabani ne da wadanda dabi’arsu ta saba musu.  Hatta malam bahaushe ma a al’adarsa yana cewa: “Sai hali ya yi daidai ake abota.”  A bangaren sinadaran lantarki ba haka abin yake ba.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.