Ma’ana da Asalin Kwayar Cutar Kwamfuta (Virus)

Daga wannan mako in Allah Ya yarda, za mu fara bayanai kan manyan matsalolin da ke damun kwamfuta da masu amfani da ita a wannan zamani da muke musamman.  Kamar dai yadda dan Adam yake ne; yana da damuwoyi da dama da ke masa kaidi wajen tafiyar da rayuwa ingantacciya kuma cikin sauki.  Haka na’urar kwamfuta take; akwai matsaloli da ke mata karan-tsaye wajen gudanar da ayyukan da aka kera ta don yin su, cikin sauki.  Wadannan matsaloli suna da yawa, amma za mu dauki wadanda suka shafi lafiyarta da kwakwalwarta ne kadai, don su ne manyan matsalolin da suka fi kowanne tasiri wajen dama mata lissafi, musamman cikin wannan zamani da aka samu kwararru kan ilimin ta, birjik a duniya.

394

Gabatarwa

Kamar yadda taken wannan kasida ya nuna, za mu yi bayani ne kan kwayoyin cututtukan da ke damun na’urar kwamfuta a yau; daga ina suke; ta yaya suke shiga jikin ta har su kai ga kwakwalwa;  mene alamun da ke nuna cewa kwamfuta ta kamu da irin wadannan cututtuka masu sanya ta zazzabi mai tsanani, a wasu lokuta ma su hana ta sakat har su kai ta ga sumewa?  Abin da muka tanada kenan a yau.  Mako mai zuwa za mu kawo bayanai kan wadanda ke da alhakin kirkiran wadannan cututtuka da kuma manufofin su.  Mu kuma ji bayanai kan hanyoyin da su suke bi wajen yada wadannan cututtuka.  Daga karshe kuma masu karatu su samu bayanai kan hanyoyin magance ire-iren wadannan matsaloli.  A kasance tare da mu.

Computer Virus: Ma’ana da Asali

Idan aka ce Computer Virus, a turance, ana nufin kwayoyin cutar da ke haddasa ma kwamfuta matsaloli ne na rashin lafiya; ko su rika aikin leken asiri a cikinta, tare da aika ma marubucinsu bayanai, ko su sauya mata bayanan da take dauke dasu, ko su goge su, ko kuma a wasu lokutan ma, su sumar da  ita.  Su wadannan kwayoyin cuta ba wasu abubuwa bane face bayanai da ke kumshe da haruffa ko lambobi da aka rubuta su ta amfani da kwarewar gina manhajar kwamfuta, wato Programming Language.  Wadannan jakunkunan bayanai na dauke ne da umarni da marubucinsu ke ba kwamfuta.  Don haka da zarar sun shigi kwamfuta, to ba abin da ya rage mata sai bin umarnin da ke cikin su.  Suna samuwa ne ta hanyoyi uku; ko dai ya zama bayanai ne zalla da aka taskance su cikin jakar adana bayanai.  A turancin kwamfuta ana kiran su Virus Text Files.  Irin wadannan nau’ukan kwayoyin cuta idan suka shigi kwamfuta ba a ganin su kai tsaye, don lungu suke samu su buya, iya kwatancin umarnin da ke cikin su, daga marubuci ko makirkirin su.

Sai nau’i na biyu da ke zuwa a matsayin masarrafa.  Wato jakar bayanai da za a iya shigar ma kwamfuta, a iya budo shi ana amfani da shi.  Su kuma ana kiransu Virus Executable Files.  Idan har ka matsa su don shigar ma kwamfuta, to ka nemo mata rigima.  Hanya ta uku ita ce ta jakunkunan bayanan da ke dauke da hotuna masu irin wadannan kwayoyin cuta.  Galibi hotuna ne masu dauke da tallace-tallace; na batsa ko kuma na harkan caca.   Watakila mai karatu yayi ta mamaki: yaya daga shigar da jakan bayanai a cikin kwamfuta kuma sai ta rikice ko sume?  Ai ba a nan take ba, wai an danne bodari a ka. Idan kana son gane yadda lamarin yake, ka kwatanta da jikin dan Adam.  Idan kwayar cuta ta shiga jikin sa, to dole ne sai an samu sauyin yanayin lafiya a tattare da shi.  Don me?  Saboda kwayar cutar ta sha banban da dabi’ar jikin sa.  To haka ma irin wadannan bayanai da ke shiga kwamfuta;  umarni ne a cikin su da maginin su ke baiwa kwamfutar, kuma a matsayinsa na wanda ya san yadda gini ko zubin tsarin manhajar ta yake, ya san hanyoyin da zasu iya zama matsala a gareta.  Don haka da zarar sun shigo, sai ta rikice.

Hanyoyin Kamuwa da Yaduwa

Wadannan cututtuka sun fara samuwa ne tun kirkiran kwamfuta da manhajojin ta, kuma akwai manyan hanyoyi guda biyu da kwamfuta ke iya kamuwa da su.  Hanyar farko ita ce ta amfani da hanyoyin shigarwa ko fitar da bayanai ta kwamfuta, wato Storage Devices, a Turance.  Ma’adanai ne da ake amfani da su wajen shigar ma kwamfuta bayanai na haruffa da taswiro ko hotuna da dai sauran su.  Sun hada da Floppy Disk, mai cin mizani miliyan daya da rabi, da kuma Zip Diskette, mai cin mizanin bayanai sama da miliyan goma, da kuma Flash Disk, wanda a yanzu aka fi amfani dashi.  Shi Flash Disk dabaka-dabaka ne; akwai mai cin miliyan dari da ashirin da takwas, da mai cin miliyan dari biyar da goma sha biyu, da kuma mai cin biliyan daya har dai zuwa sama.  Dukkan wadannan ma’adanai ne da ake amfani da su wajen shigar da bayanai ko debo su daga kwamfuta.  Idan suna dauke da kwayoyin cutar kwamfuta, ka shigar dasu cikin kwamfutarka, to nan take zasu nemi wuri a cikin ta su labe.  Hanya ta biyu ita ce ta hanyar Intanet.  Nan ma kana iya jefa kwamfutarka cikin hadari.  Idan ka sauko (Download) ma kwamfutarka da masarrafa (Software) mai dauke da kwayoyin cuta, yanzu za ta kamu.  Haka idan ka cika ziyartan gidajen yanar sadarwa na caca da batsa, kana matsa duk hoton da ka gani, kana iya kamuwa da wadannan cututtuka.

Haka kuma idan ka cika sauko (Download) da duk jakar bayanai da ka ga an aiko maka ta Imel dinka, ba tare da ka san mai aikowa ba, nan ma kana iya kamuwa da wannan cuta.  Galibin sakonnin da ake aiko mana cikin Imel din mu wadanda bamu san mai aiko su ba, wato Spam Mails, duk za ka samu suna dauke da makalutun bayanai (Attachments), kuma sau tari za ka samu akwai kwayar cutar kwamfuta cikin su.  Wadannan, a takaice, su ne shahararrun hanyoyin da ake bi a kamu da cutar kwamfuta.

Alamun Kamuwa

- Adv -

Idan kwamfuta ta kamu da cuta, ba kowa ke iya ganewa ba, sai wanda ya saba mu’amala da ita a kullum.  Ko shi ma, ba kowanne zai iya ganewa ba.  Kwamfuta na iya kamuwa da cuta, amma kuma ba a gane ba.  Kai a takaice dai, akwai alamun da za a iya ganewa ba tare da sai an sha wahala ba.  Akwai kuma wadanda sai kwararre ke iya gane su.  Nau’ukan farko sun shafi shahararrun alamu masu bayyana, wadanda ko da baka san cewa kamuwa tayi ba, ka san cewa akwai matsala.  Sun hada da yawan saibi.  Idan ka bata umarni, sai ta dauki lokaci kafin ta karbi umarnin ka.  Muddin kaga haka yaci gaba, lokaci mai tsawo, to akwai matsala.  Haka idan kaga tana yawan sumewa da kamewa alhalin kana aiki da ita.  Wannan shi ake kira Hanging a turancin kwamfuta.  Muddin ta ci gaba da haka, kuma ba a jone kake da Intanet ba, to akwai matsala.   Haka idan ka nemi wasu jakunkunan bayanan ka ka rasa, ko kuma ka samu wasu, ka rasa wasu, ko kuma ka budo jakunkunan, ka samu wasu bakin bayanai da baka san dasu ba, masu dauke da wasu irin sunaye marasa kan gado, to da matsala.

Haka idan ka kasa bude jakunkunan bayanan ka gaba daya, ko kuma idan ka budo guda daya, sai su yi da budowa ba tare da ka budo su da kanka ba, to duk alama ne da ke nuna cewa kwamfutar ka ta kamu.  A wasu lokuta kuma za ka samu kwamfuta na mutuwa da kunna kanta, ba tare ka kashe ta ba, haka kawai!   Duk wannan alama ne da ke nuna kamuwa.  Idan kuma cutan ya ga dama, yana iya gurbata maka bayanan ka gaba daya; duk wanda ka budo sai dai ka yi ta ganin wasu shirmen sunaye ko haruffa.  Duk aikin su ne.  A wasu lokuta kuma kwamfutar na iya kamuwa, amma ba za ka taba sani ba.  Galibin lokuta sai an sanya manhajar goge cutar kwamfuta, wato Antivirus Software, sannan ake iya ganowa da cire su.  Idan kuma cutar mai tsanani ce, illolin ta na iya haddasa ma kwamfuta hadari mai girma, ta yadda sai an sanya mata wani sabon ruhi ko babban manhaja sannan za ta iya ci gaba da aiki.  Wannan manhajar ba ya iya magance mata matsalolin ta.

Nau’ukan Kwayoyin Cutar Kwamfuta

Suna nan da yawa!  Da farko dai shahararren sunan da aka fi sanin su dashi shi ne Computer Virus, a turance.  Amma a karkashin wannan suna akwai rukuni wajen hudu, iya gwargwadon girma/tsanani ko kuma yanayin illa ko aikin da cutar ke iya yi a cikin kwamfuta.  Da farko akwai kwayoyin cututtukan da ake tsofa su cikin masarrafan kwamfuta da galibi ake samu kyauta a Intanet.  Su ana kiran su Spyware, kuma aikin su shi ne yin leken asiri ga uban gidan su, wato wanda ya gina manhajar kenan.  Akan sanya su ne cikin masarrafan, don duk lokacin da ka jona kwamfutar ka da Intanet, wannan masarrafa da ka samo kake amfani da ita kyauta, ta rika aika ma mai shi da bayanai kan tsarin abin da kake yi.  Yai haka ne don wata manufa mummuna ko kyakkyawa.  Galibi na yin haka ne don sanin yawan wadanda suke amfani da wannan manhaja nasu.  Amma a ka’ida bai dace ba.

Sai kuma rukuni na biyu, wato Malware, wadanda su ma a cikin manhajojin kwamfuta da ake samu ta Intanet ake sanya su.  Sai dai sabanin na farko, su wadannan aikin su na cutarwa ne kai tsaye.  Idan ka sake suka shiga kwamfutarka, nan da nan za ka fara ganin alamun rashin lafiya tattare da ita.  A kataice dai cuta ce ta kwamfuta mai halakarwa.  Sai rukuni na uku, wadanda ake kira Adware.  Su kuma galibi idan kana yawan mu’amala hotunan tallace-tallace ne za ka iya kamuwa da su.  Cututtuka ne na kwamfuta, masu dauke cikin hotuna masu motsi ko marasa motsi.  Idan ka matsa (Click) hotunan da suke dauke dasu, da zarar shafin hoton ya budo, to kwamfutarka ta shiga kenan, muddin ka ci gaba da ta’ammali da wannan shafi.

Wadannan cutattuka an fi samun su a gidajen yanar sadarwa na caca da batsa da kuma katuttukan gaishe-gaishe (Greetings Cards).  Sai rukuni na karshe, wato Trojan Horse.  Idan irin wannan cuta ya shiga kwamfutarka, to gaskiya hanya mafi sauki shi ne kayi mata juyen ruhi kawai, wato Formatting.  Domin yana mallake ta ne gaba daya, ya bi ta ya mamaye; ya hana ka aiki da komai a kwamfutar gaba daya.  Idan Trojan Horse ya auri kwamfutarka, sai makabarta, Yalla!  Domin zai mallake manyan ma’adanta ne, wato Disk Drives, ya hana ka budo komai, ya rikita kwamfutar gaba daya.   Wasu lokuta idan ya ga dama, sai ya dasa wani shafi guda daya, wanda zai rufe fuskar kwamfutar ma gaba daya; baka iya komai. Idan kwamfutar ka a jone take da Intanet, ya fuskanci kana niyyar budowa ko kuma sauko da manhajar goge cutar kwamfuta, sai ya kashe kwamfutar gaba daya, ya sake kunna maka ita.  Amma idan ba can ka nufa ba, shikenan.

A takaice dai, cuta ne mai lura da dukkan abin da kake yi. Idan aikin ka ya shafi jakunkunan bayanai ne zalla, sai ya barka (iya gwargwadon umarnin da uban gidan sa ya bashi).  Amma idan ya ga ka nufi Intanet da rariyar lilo da tsallake-tsallaken ka, wato Browser, sai ya kashe kwamfutar kawai.  Wannan ya taba faruwa da ni shekaru kusan uku da suka gabata.  Sai da na sauya ma kwamfutar wani sabon ruhi na zauna lafiya.

Kammalawa

A bayyane yake cewa babban matsalar da ke damun kwamfutoci a halin yanzu shi ne cututtukan da ke mata illa wajen hana ta aiwatar da ayyukan ta cikin sauki.  A mako mai zuwa za mu kawo bayanai kan wadanda ke da alhaki wajen samar da wadannan cututtuka da kuma manufofin su.  Har wa yau za mu kawo nau’ukan hanyoyin da suke bi wajen yada ire-iren wadannan cututtuka.  Idan akwai tambayoyi a rubuto ko bugo waya  ta 08034592444, ko kuma a aiko sakon Imel ga fasaha2007@yahoo.com.   Idan da hali, sai a ziyarci mudawwanar da muka tanada don wannan shafi: http://fasahar-intanet.blogspot.comA ci gaba da kasancewa tare da mu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.