Ma’ana da Nau’ukan Makamashi

A bangaren kimiyyar makamashi, yau za mu fara bayani kan makamashi da ma’anarsa, da kuma nau’ukansa. A sha karatu lafiya.

143

Gabatarwa

Don samun natsuwa da sauki a dukkan marhalan rayuwarsa ta duniya, dan Adam na bukatar makamashi kusan fiye da kowane irin halitta da ke rayuwa a doron wannan kasa.  Domin sai da makamashi zai iya gyatta abincinsa; sai da makamashi zai iya dumama jikinsa don samun cikakkiyar lafiya a yanayin sanyi da hunturu; sai da makamashi zai iya kera wasu cikin kayayyakin da yake matukar bukatarsu wajen tafiyar da rayuwa; sai da makamashi dan Adam, a wannan zamani da muke ciki, zai iya tasarrufi daga wannan gari zuwa wancan, ko wannan kauye zuwa wancan  ko kuma wannan unguwa zuwa wancan. In tafiya tayi nisa ma, hatta sadarwa bazai iya yi ba sai ta hanyar wasu daga cikin nau’ukan makamashin da muke da su a yau.  Kai a takaice ma dai, wasu cikin manyan al’amuran Ibada basu yiwuwa ta dadi sai da makamashi a wannan duniya tamu ta yau.  To me ake nufi da makamashi?

Makamashi ba ya bukatar wata doguwar ta’arifi, domin kowa ya san abin da ake kira da suna makamashi.  Amma don tunatarwa, makamashi shi ne dukkan wani abin da zai sawwake wa dan Adam hanyoyin tafiyar da rayuwa wajen abin da ya shafi dumamawa, gasawa, dafawa, haskakawa, Konawa, sanyayawa, tasarrufi da sadarwa da dai sauran abin da zai iya bukata masu alaka da makamashin.  A takaice, dan Adam na bukatar wuta, da hasken lantarki, da hasken rana (da dukkan nau’ukansa), da man fetur da gaz da dizil da dai sauran abubuwa masu nasaba da su.  Wadannan dukkansu ana kiransu makamashi da Hausa, ko kuma kace Energy, a turancin kimiyyar muhalli.  Muhallin dan Adam gaba daya a cike yake da dukkan nau’ukan makamashin da yake bukata; ya sani ko bai sani ba.  Daga hasken ranar da ke ziyartarsa a dukkan rana, zuwa tururin zafin karkashin teku, da matattun halittu ko tsiri da ke daskare a karkashin kasa, zuwa dunkulallun bakaken duwatsu da ke kawwanuwa ta sanadiyyar tarkacen da ke karkashin kasa, duk suna samar wa dan Adam dukkan makamashin da yake bukata.  Wasu daga cikin wadannan nau’uka na makamashi a zahiri suke kowa na iya ganinsu.  Wasu kuma basu ganuwa sai dai kawai a samu natijarsu a matsayin makamashi.  Hakan ya baiwa dan Adam yakinin yarda da samuwarsu.  Har zuwa wannan lokaci, dan Adam bai gama  gano dimbin makamashin da ke dankare tsakanin sama da kasa ba, balle ya taskance su don amfaninsa.  Sai dai kawai yayi iya yinsa, sauran ya bar wa na baya.

Nau’ukan Makamashi

Kamar yadda bayani ya gabata, akwai nau’ukan makamashi da dama da Allah Ya hore wa dan Adam amfani dasu tsakanin sama da kasa.  Yana kuma ganowa ko amfanuwa das u ne iya gwargwadon ilimi da kuma binciken da yayi wajen gano su.  Hatta wadanda yake gani ko jinsu a fili, amfanin da yake dasu ya ta’allaka ne da iya gwargwadon bincikensa.  Idan muka dubi littafan tarihi, za mu ga cewa dukkan al’ummomin da suka shude suna da nau’ukan makamashinsu.  Zai iya yiwuwa muna amfani da irin nasu a yanzu, amma saboda tasirin bincike da aka yi ko ake kan yi a yanzu, mun sake samun wasu nau’ukan dabam, ko da kuwa hanyoyin samuwarsu iri daya ne da na al’ummar da suka gabace mu.  A halin yanzu akwai nau’uka da dama, amma za mu takaita bayani ne kan kadan daga cikinsu, wadanda suka shahara.  Wadannan shahararru dai su ne: makamashin da ake samu daga tataccen hasken rana, wato Solar Energy kenan a Turance.

- Adv -

Akwai wasu nau’ukan makamashin da ke wannan duniya wadanda ake samu daga gundarin hasken rana da ke darsuwa a wannan duniya tamu; wanda jikin dan Adam ko kwayar idonsa basa iya jure ji ko riskarsa, ba wai irin nau’in hasken ranar da yake iya gani ba a kullum. Wadannan nau’ukan haske su ake kira Electromagnetic Radiation, kuma suna dauke ne da makamashi mai dimbin yawa, masu taimaka wa dan Adam wajen bincike da sauran abubuwan ci gaba. Sai makamashin tururin zafin karkashin teku, wanda ake kira Geothermal Energy.  Akwai kuma makamashin wutar lantarki, wato Electricity kenan.  Bayan wadannan akwai makamashin nukiliya, wato Nuclear Energy.  Sai makamashin da ake tsuwurwirtarsa daga karfin iskar da ke bugawa a cikin wannan duniya tamu, wato Wind Energy.  A karshe kuma za mu ji bayani kan makamashin karkashin kasa, wanda ke samuwa sanadiyyar rubabbun tarkacen da ke daskare shekaru aru-aru, wato Fossil Fuel ko kuma Geological Energy.  Wani abin sha’awa shi ne, galibin nau’ukan makamashin da aka zayyana, wasu masu zaman kansu ne, wasu kuma su ke samar da wasu.  Za mu ji bayani dai filla-filla nan gaba.

Makamashin Hasken Rana (Solar Energy)

Hasken rana da ke mamaye duniya yayin fitowarta shi ke dumama duniya da dukkan abin da ke cikinta, da zarar ya hasko.  Kuma wannan dumi ko zafi na samuwa ne iya gwargwadon yadda halittu ke bukatarsa wajen tafiyar da rayuwa.  Idan ya gaza yadda yake fitowa, za a samu matsala wajen rayuwarsu.  Haka idan zafin ya tsananta fiye da kadarin da rai ke bukata, dukkan halittu na iya konewa gaba daya da dukkan ilahirin muhallinsu.  Allah Buwayi gagara misali!    Wannan haske na samuwa ne da zarar rana ta bullo, ta hanyar wasu sinadarai masu suna Photons.  Su sinadaran Photons wasu balgace ne ko buraguzan makamashi masu haske da ke samuwa ta sanadiyyar zarrar maddar maganadisu masu hadewa da juna don haifar da walkiyar haske a sararin samaniya (wato electromagnetic charges).  Idan rana ta hudo daga inda take fitowa, takan hasko ne kai tsaye da haske da zafin da ke dauke cikin hasken.

A dukkan minti guda, rana takan darkako da haskenta cikin dukkan murabba’in mita guda na fadin kasa a wannan duniya da zafin hasken da ya kai Megawatt dubu daya da dari hudu.  Wannan zafi ne mai dimbin yawa wanda halittu baza su iya rayuwa a karkashinsa ba.  Don haka kashi hamsin cikin dari na zafi da hasken kadai ke riskar wannan kasa da muke kai.  Sauran kashi hamsin din da ya saura, ya bi cikin hazo da gagarumar iskar da ke bugawa a saman wannan duniya da muke kai.  Bayan haka, shi kansa kashi hamsin da ke darsuwa a wannan duniya tamu, zafinsa ya danganci lokaci da ranar da ake ciki da kuma bigiren da rana take fitowa a wannan lokaci ko yanayi na shekara.

Amma a yini guda, wannan haske na rana kan kure zafinsa ne idan tazo tsakiyar duniya, daidai karfe goma shabiyun rana kenan.  Da zarar ranar ta karkata, sai zafin ya fara raguwa.  Amma duk yadda zafin ya kai cikin yini ko shekara, ba ya wuce kashi hamsin da digo biyu (50.02%), idan ya tsananta kenan.  Ko kuma kashi arba’in da tara da digo casa’in da takwas (49.98%), idan yayi kasa kenan.  Idan yayi kasa fiye da haka, halittu na iya samun matsala wajen tafiyar da rayuwa.  Haka idan ya haura sama da yadda ya kamata, halittu na iya konewa ko narkewa ma gaba daya.  Wannan yayi daidai da fadin Allah Madaukakin Sarki a cikin Kur’ani, inda yake nuna cewa taskar duk wani arziki a wurinsa yake, kuma ba ya saukar dashi sai iya gwargwadon bukatar halittu.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Hassana says

    Hayyakallah baban sadik fatan Alkhairi gareka da Kuma aminci. Tambayata anan shine shin wannan taska har yanzu tana fitar da sabbin mukaloli ko Kuwa?

Leave A Reply

Your email address will not be published.