Manhajar Lilo (Web Browser) (2)

Wannan kashi na biyu ne na kasidar da ta gabata a makon jiya. Mun kawo samfurin manhajar Intanet Explorer na kamfanin Microsoft ne. A sha karatu lafiya

180

Siffofin Internet Explorer 6.0

Hausawa suka ce alkawari kaya ne.  Idan mai karatu bai mance ba, makonni biyu da suka gabata ne muka fara koro bayanai kan Rariyar Lilo da Tsallake-tsallake wato Web Browser, a turance.  Mun fadi ma’ana da kuma tarihin yadda wannan manhaja mai muhimmanci ya fara bayyana.  Daga karshe, bayan mun gabatar da sunayen wasu daga ciki, muka sanar da mai karatu cewa wadanda suka fi shahara a halin yanzu su ne: Internet Explorer (na kamfanin Microsoft), Firefox (na kamfanin Mozilla), da kuma Netscape Navigator (na kamfanin Netscape).  Daga karshe kuma muka yi alkawarin cewa a mako mai zuwa za mu kawo bayanai kan siffofin Rariyar Lilo da Tsallake-tsallake na kamfanin Microsoft, wato Microsof Internet Explorer 6, tun da ita ce ta fi shahara a wannan bangaren da muke. Bamu samu yin hakan ba cikin makon da ya gabata saboda wasu dalilai da suka sha karfi na.  da fatan za a gafarce ni.

Da zarar ka budo wannan masarrafa ta Internet Explorer wacce ka saba amfani da ita, za ka samu a kalla bangarori shida ne, wadanda ke taimaka ma dukkan mai amfani da ita.  Wadannan bangarori dai su ne: Title Bar, Menu Bar, Tool Bar, Address Bar, Display Page, da kuma Process Bar.  Wadannan bangarori dukkansu kowanne aikinsa daban ne da na dan uwansa; kamar yadda maginin Rariyar ya gina ko tsara su.  Kuma duk da yake a wuri daya suke, wani a saman wani, kowannensu manhaja ne mai zaman kansa a can cikin tumbin kwamfutar da kake amfani da ita.  Duk lokacin da ka kira daya daga cikinsu, sai kwamfuta ta zakulo maka shi cikin kiftawa da bisimilla, don ya gabatar maka da aikin da kake bukata, sannan ya koma mazauninsa.  A halin yanzu ga bayanin kowanne daga cikinsu, a fayyace:

Title Bar

Wannan shi ne shudin layi ko gurun da ke saman shafin masarrafar gaba daya.  An kuma kira shi da wannan suna ne saboda shi ne ke bayyana maka sunan masarrafa, da kuma sunan shafin gidan yanan sadarwan da kake ciki.  Da zarar ka budo shafin gidan yanan sadarwa da Internet Explorer, kana daga kanka sama daga hannun hagu, za ka ga an rubuta “Yahoo! – Microsoft Internet Explorer”, idan gidan yanan sadarwan Yahoo! ka shiga, misali.  Idan kuma ka dubi can kuryan dama, za ka samu wasu alamu guda uku, wadanda ke taimaka kara fadin shafin da kake ciki, ko rage zuwa kasa, don budo wani shafi, ko kuma ma ka rufe shafin gaba daya.  Na farko ne zai taimaka ma sauko da shafin kasa (minimize), na biye da shi kuma ya taimaka maka kara fadin shafin (maximize), shi kuma na karshen aikinsa shi ne rufe shafin gaba daya (close).  Har way au, idan kana bukatan kara fadin shafin, za ka iya yi ba tare ka je “minimize” ba, a a, sai kawai ka saman Title Bar din sau biyu a lokaci daya (double-click).  Shafin zai karu gaba daya, iya fadinsa na asali.  Wannan aikin Title Bar kenan.

Menu Bar

Shi kuma Menu Bar shi ne layin da ke kasan Title Bar, yana daga cikin bangarori masu muhimmanci ga duk mai amfani da masarrafar lilo da tsallake-tsallake.  Menu Bar na dauke ne da hanyoyi guda bakwai da zasu taimaka maka aiwatar da wasu ayyuka masu muhimmanci yayin da kake yawace-yawacenka a gidajen yanan sadarwa ta Intanet.  Wadannan bangarori ko hanyoyi sune: File (mai dauke da hanyoyin budo wani sabon shafi, ko binciko bayanan da ka ajiye cikin kwamfutarka don loda su a shafin yana, ko adana wasu bayanan da ka samo daga Intanet, zuwa kwamfutarka, ko kuma ya taimaka maka buga  – print – bayanan da ka samo masu muhimmanci), Edit (mai taimaka wajen yanko wani bayani da ka gani zuwa kwamfutarka, ko kwafo shafin gaba daya), View (wanda zai kai inda za ka iya kara yawan makaman aikin da ke Tool Bar, ko kuma taimaka maka wajen ganin fasahan da aka gina shafin da kake ciki da shi, wato View Source), Favourites (wanda zai taimaka maka wajen adana adireshin shafin yanan da kake ciki, idan ya kayatar da kai, ko kuma yadda za ka tsara wasu adiresan da ka adana a baya), Tools (zai taimaka maka wajen tsara saitin kwakwalwan rariyarka.  Yana daga cikin bangarori masu muhimmanci a masarrafar lilo da tsallake-tsallake.  Za ka samu inda za ka tsara makale-makalen da ke tattare da wannan masarrafa, masu taimaka mata aiwatar da wasu ayyuka – Manage Add-ons- sai kuma inda za ka je don tsara yadda masarrafar za ta rika budo maka shafukan yanan gizo, da irin gidajen yanan da za ta rika shiga.

Akwai kuma inda ma za ka iya shigar da gidan yanan sadarwan da baka son a rika ganinsu a kwamfutar gaba daya.  Duk wadannan za ka iya gabatar da su ne a Internet Options, mai dauke da bangarorin: General, Security, Privacy, Content, Connections, Programs, Advanced.), sai Help (mai dauke da hanyoyin samun taimako kan dukkan matsalar da ka samu a yayin da kake amfani da wannan masarrafa ta Internet Explorer.  Dukkan wadannan hanyoyi, zasu riskar da kai ne zuwa jerin bayanai kan irin aikin da kake so masarrafar tayi maka.  Da ka matsa, zasu budo jerin bayanai, sai ka zabi abin da kake so.  Shi yasa ake kiran su da suna Menu, kamar yadda za ka je gidan abinci, a kawo maka jerin sunayen abincin da ake dasu, sai ka zabi wanda kake so a kawo maka.  Bangare na karshe a Menu kuma wata alama ce da ke can kuryan hannun dama, mai kama da kwallon taswiran duniya (Global Map), ko kuma mai dauke da tutar kamfanin Microsoft.  Shi wannan tambari alama ne da ke nuna maka cewa akwai siginar Intanet a yayin da ka budo ko kake yawo a gidan yanan sadarwa, ko kuma babu. Idan ka ga yana jujjuyawa ba kakkautawa, to alama ne da ke nuna cewa akwai Intanet.  Amma idan ka ganshi a tsaye cak, to da matsala.

Tool Bar

Wannan shi ne bangaren da ke dauke da almun da zasu aiwatar maka da wasu ayyuka na gaggawa, ba tare da sai ka je Menu Bar ba.  Alamun na dauke ne da sunan nau’in aikin da kowannensu ke yi.  Tool Bar na kasan Menu Bar ne.  daga hagu zuwa dama, za ka fara cin karo da alamar kibiyar da tayi hagu, an kuma rubuta Back daura da ita.  Zai taimaka maka ne wajen dawowa baya daga inda kake, a shafin yanar gizo.  Sai kibiyar da yayi gaba, don taimaka komawa shafin da ka fito, idan ka yi baya da farko.  Sai alamar Stop, wacce za ta dakatar da masarrafa, idan da farko ka bata umarnin nemo maka wani shafi.  Sai Refresh, wacce idan ka ga alamar “Page Cannot Be Displayed”, ita za ka matsa, don ta farfado maka da shafin da kake nema.  Sai Home, wacce za ka isar da kai asalin adireshin da aka dabi’antar da masarrafar ka a kai (a Internet Options ake wannan).  Da dai sauran alamun da ke wajen, wanda za ka samu kowanne da sunansa ko aikin da zai maka.

- Adv -

Address Bar

Wannan a fili yake; shi ne farin layin da  ke kasa da Tool Bar, kuma aikinsa shi ne ya zakulo maka gidan yanan sadarwan da kake bukata, ta hanyar shigar masa da adireshin gidan yanar. Idan baka shigar da adireshin daidai ba, bazai gyara maka ba, don bai san manufarka ba.  Afuwan da zai iya maka kawai shi ne ya taimaka maka wajen shigar da haruffan http:// idan ya zama www.yahoo.com kawai ka shigar, a misali.  A gaba dashi za ka samu wasu rariyoyin likau da aka tanada maka, wadanda za ka iya matsa su a zarce da kai gidan yanan kai tsaye.

Display Page 

Shafin masarrafar kenan, inda zai rika budo maka dukkan shafin yanar da kake so, idan ka shigar da adireshin daidai kenan.  Idan baka shigar da adireshin daidai ba, za t ace maka: Page Cannot Be Displayed.  Za kuma ta iya nuna maka wannan alama idan ya zama siginar Intanet ta dauke daga kan kwamfutar da kake kai, saboda tsananin ruwan sama da ake tafkawa, ko kuma tsananin hazo ko yawan masu lilo a inda kake, ko kuma wayar da ke sadar da kai da uwar garke (server) ta cire.

Process Bar

Shi kuma Process Bar shi ne layin da ke kasan shafin gaba daya.  Shima ba zaman banza yake a wajen ba, a a, yana da nasa ayyukan da yake yi, ko ka kula shi ko baka kula shi ba.  Ayyukansa muhimmai guda hudu su ne; ya sanar da kai cewa ya gama budo maka shafin da kake nema, ta hanyar “done” da za ka gani a rubuce, ko ya sanar da kai cewa yana kan lalubo maka shafin da kake nema, ta hanyar “connecting to . . . .” da za ka gani a rubuce; ko sanar da kai cewa sauran kadan shafin da kake nema ya gama budowa, ta hanyar “4 items remaining”, da za ka gani a rubuce, a misali.  Wazifansa na karshe kuma shi ne ya sanar da kai cewa akwai siginar Intanet a kwamfutarka ko babu, ta hanyar tambarin taswiran duniya da za ka gani, kamar yadda yake a Menu Bar.  Idan ka ga ba ya juyawa, to da matsala.  Wadannan su ne siffofin Microsoft Internet Explorer 6.0.  Sai dai a wasu lokuta, za ka samu wasu layuka a kasan Address Bar, masu dauke da wasu karikitai wajen taimaka maka gabatar da wasu ayyuka daban, kamar yadda mai karatu zai gani a hoton masarrafar da muka gabatar a sama.  Ire-iren wadannan makale-makale ana kiransu Add-ons, ko kuma Plug-ins, a turancin kwamfuta.

Add-Ons/Plug-Ins

Wadannan karikitai su ma manhajoji ne ko masarrafa, masu taimaka ma Rariyar Lilo gabatar da wasu ayyuka, kamar su budo jakunkunan bayanan da aka tsara da wasu manhajojin da kwamfutarka bata zo da su ba, irin su PDF (Portable Document Format) dsr.  Har wa yau, su kan taimaka maka wajen sarrafa jakunkuna masu sauti (audio files), da jakunkuna masu dauke da hotuna masu motsi (video files) da dai sauran ayyuka.  Wasu kuma su kan taimaka maka ne wajen tattaro maka bayanai ko labaran duniya a takaice (RSS Feeds), don ka samu isa garesu ba tare da kaje gidan yanar sadarwan ba.   Wannan tasa manyan gidajen yanar sadarwa irinsu Yahoo! da Google suka kirkiro abin da suke kira Tool Bar (Yahoo! Tool Bar/Google Tool Bar).  A wannan sandan manhaja da suka kirikiro, za ka samu manhajoji da dama da zasu taimaka maka gabatar da ayyuka masu muhimmanci, ciki har da nemo bayanai ta hanyar Matambayi Ba Ya Bata (Search Engine).  Galibin wadannan manhajo ana samunsu ne a gidajen yanan sadarwa masu bayar da su kyauta.  Shahararriya daga cikinsu ita ce Download.com (http://www.download.com).  A ciki za ka samu manhajoji muhimmai da zasu taimaka maka gabatar da ayyuka da dama.

Kammalawa 

Daga karshe, yana da kyau mai karatu ya budo Microsoft Internet Explorer yin nazari kan dukkan ababen da aka sanar da shi, duk da yake galibin manhajojin da za ka iya dirowa (downloading) da su, na bukatar a ce kwamfutar taka ce.  Shi ilimi wani abu ne da saninsa ke da muhimmanci, ko da kuwa watakil mutum ba zai aikata shi ba, musamman kan harkokin rayuwa.  Za mu dakata a nan, sai zuwa wani lokaci in Allah.  Ina mika gaisuwata ga dukkan masu karatu, Allah Ya bar zumunci tsakaninmu, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.