Masu Mu’amala da Fasahar Intanet a Duniya Sun Kai Biliyan 3 – In Ji ITU

A wannan mako dai mun dubi rahoton Hukumar Sadarwar Tarho ta Duniya ne, wato: “International Telecommunication Union” (ITU), kan adadin masu mu’amala da Intanet a duniya. A sha karatu lafiya.

190

Kamar yadda ta saba, hukumar lura da harkar sadarwa ta duniya mai suna International Telecommunication Union, ko ITU a gajarce, ta fitar da alkaluman adadin masu shawagi a giza-gizan sadarwa ta duniya ta amfani da dukkan kayayyakin sadarwa a duniyar yau.  Wannan rahoto nata, wanda shi ne kashi na farko a zangon rabin shekara, ya tabbatar da cewa a yanzu kashi 40 ne cikin 100, wato mutane biliyan biyu da miliyan dari bakwai (2.7billion) na jama’ar duniya suke mu’amala da fasahar Intanet.  A wannan rahoto da ta fitar cikin watan da ya gabata, hukumar ta sanar da cewa ya zuwa tsakiyar wannan shekara ta 2013, masu mu’amala da fasahar Intanet a duniya sun doshi biliyan 3!  Wannan adadi kuwa shi ne kashi 40 na jama’ar duniya baki daya.  Cikin wannan kaso, kasashe masu tasowa na da kashi 31, a yayin da sauran kashi 79 daga kasashe masu arziki ne.  Wannan, a cewar hukumar, ya dada fito da katafaren tazarar da ke tsakanin kasashe masu arziki da marasa galihu ne, musamman a fagen sadarwa ta duniya.  Amma akwai alamar cewa kasashe masu tasowa lallai sun fara tasowa, musamman ganin yadda suke ta hankoron tabbatar da tsarin sadarwar bayanai ta Intanet mafi inganci, wato Broadband, da inganta tsarin sadarwar wayar salula da sauran hanyoyi.

A daya bangaren kuma, hukumar ITU ta tabbatar da cewa kasashe Turai (Europe) ne suke da kaso mai girma na adadin jama’a a giza-gizan sadarwa ta Intanet.  Domin cikin duk mutum 4, to, 3 na da hanyar sadarwa ta Intanet.  Sai kasar Amurka da ta biyo baya da kashi 61, da nahiyar Afirka mai kashi 16, sai kuma nahiyar Asiya mai dauke da kashi 50 cikin 100.  A nahiyar Asiya kowane mutum daya cikin mutane uku, ya mallaki hanyar sadarwa ta Intanet.

A bangaren jinsi kuma, hukumar ta nuna cewa an samu karin adadi da kaso a bangaren mata masu mu’amala da wannan fasaha a duniya, inda kasonsu (percentage) ya karu da kashi 16.  A yanzu akwai maza sama da biliyan daya da miliyan dari biyar masu mu’amala da fasahar Intanet a duniya, da mata sama da biliyan daya da miliyan dari uku.  Wannan ya cilla kason maza zuwa kashi 41 cikin 100, su kuma mata kasonsu ya haura zuwa kashi 37 cikin 100 a duniya.  A kasashe masu tasowa mata masu mu’amala da fasahar Intanet sun kai miliyan 826, a yayin da maza suka haura zuwa miliyan 980.  A kasashe masu arziki kuma wannan adadi ya sha bamban, a yayin da adadin maza masu mu’amala da fasahar  ya tsaya a miliyan 475, adadin mata ya haura zuwa miliyan 483.

- Adv -

Dangane da ci gaban sadarwa a gidajen jama’a kuwa, hukumar ta nuna cewa daga cikin gidaje miliyan 750, kashi 41 a jone suke da fasahar Intanet.  Daga cikin wannan adadi, kaso 28 daga cikin wadannan gidaje na kasashe ne masu tasowa, a yayin da kashi 78 daga kasashe ne masu arziki.  Hukumar ta ci gaba da cewa bayan wadannan gidaje masu jone da fasahar Intanet, a duniyar yau akwai gidaje sama da biliyan daya da miliyan dari daya da har yanzu basu samu alfarmar jonuwa da fasahar Intanet ba.  Daga cikin wannan adadi, in ji wannan rahoto, kashi 90 na gidajen na kasashe ne masu tasowa, a yayin da sauran ke kasashe masu arziki.  Nahiyar Turai ce ke da gidaje masu jone da fasahar Intanet sama da kowace nahiya ta duniya.  Domin, a cewarta, kashi 77 na gidajen da ke Turai duk a jone suke. A yayin nahiyarmu ta gado Afirka ke dauke da kashi 7 kacal cikin gidajen da ke jone da fasahar Intanet.  A nahiyar Afirka kuwa, bincike ya nuna cewa tsakanin shekarar 2009 zuwa 2013, gidaje masu jone da fasahar Intanet sun karu da kashi 27, a nahiyar Asiya kuma da kashi 15, haka ma a kasashen Larabawa.

A bangaren kudancin Amurka kuwa, wato Latin America, kashi 61 suna mu’amala da fasahar Intanet.  Idan muka koma kasashen Larabawa kuma, rahoton ya nuna cewa a cikin duk mutum uku, daya na mu’amala da fasahar Intanet.  Kamfanin binciken ci gaban kimiyyar sadarwar zamani mai suna McKinsey & Co, yayi hasashen karuwar masu mu’amala da fasahar Intanet a Indiya daga miliyan 160 zuwa miliyan 330 ya zuwa shekara ta 2015.  A nata bangaren kuma hukumar ITU ta yi hasashen karuwar masu amfani da tsarin Broadband duk dai a kasar ta Indiya daga miliyan 175 zuwa miliyan 600 nan da shekara ta 2020.

Masana a tsarin sadarwar zamani sun nuna cewa daga cikin manyan dalilan da ke haddasa habbakar masu mu’amala da fasahar Intanet a kasashe masu tasowa musamman, akwai yaduwar wayoyin salula masu dauke da tsarin sadarwa ta GSM.  Sukan buga misali da Najeriya, inda a shekarar 2000, daidai sadda aka baiwa kamfanonin wayar salula lasisi, masu amfani da wayoyin salula basu shige dubu dari biyar ba.  Amma ya zuwa wannan shekara akwai masu amfani da layin wayar salula da kamfanonin wayar kasar suka bayar, kusan miliyan 100! A daya bangaren kuma, akwai karancin yaduwar fasahar Intanet a gidajen mutane a nahiyar Afirka musamman, ba don komai ba sai don dalilin farko.  Galibin jama’a sun gwammace su yi mu’amala da fasahar Intanet ta hanyar wayar salula ko na’urorin mu’amala da bayanai na zamani, irinsu iPad, da Samsung Galaxy Note, a misali.  Maimakon sayan kwamfutoci, mutane sun gwammace, kuma ya fi musu sauki su gudanar da ayyukansu ta amfani da wadannan na’urori.

- Adv -

You might also like
2 Comments
  1. Muryar Hausa24 Online Media says

    NIGERIA KENAN!

    FATANA HAUSAWAN MU SUMA SU SHIGO A DAMA DA SU.

    DOMIN IDAN MUKA HADA HANNU DA HANNU ZAMU KAI KASAR GA GACI AMMA NAFISON HAUSAWAN MU SU MAYAR DA HANKALI AKAN HARSHEN HAUSA SABODA A YAU YAFI KARANCI A SHAFUKAN YANAR GIZO, WANDA DUKKAN MU ZAMU IYA TAIMAKAWA WAJEN BUNKASAR SHI , SAI DAI MAFI YAWANCIN MU A WANNAN ZAMANIN MUNFI MAI DA HANKALI AKAN YAREN ENGLISH A MAIMAKON NAMU YAREN.

    SHAFIN KA YANA DAYA DAGA CIKIN YAREN DA YAKE KARA MIN GWIWA DON GANIN NI MA NA BAYAR DA GUDUNMAWATA AKAN HARSHEN.

    MATSALAR KAWAI IDAN MUTUM YANASON YAYI ABUBUWA YADDA YA KAMATA DOLE SAI DA ISASSUN KUDADE.

    1. Muryar Hausa24 Online Media says

      Na manta zance…

      Yana daya daga cikin shafukan da suke karamin kwarin gwiwa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.