Matsalolin Katin ATM a Najeriya (2)

Wannan shi ne kashi na biyu kuma na karshe, cikin jerin kasidun da muka fara a makon jiya, kan matsalolin kati ko tsarin ATM a Najeriya. A wannan karon mun dubi dalilan da suka haddasa wadannan matsaloli ne, da irin hanyoyin da bata gari ke amfani dasu. A sha karatu lafiya.

171

Musabbabai

Dole akwai matsala, to amma me ke haddasa matsalar?  Wannan shine abin da galibin masu ajiya a bankuna ke damuwa a kai.  Wannan tasa da yawa suka daina amfani da katin; wasu kuma suka ki karba ma gaba daya.  Domin a cewarsu, kada su buda wa wani dan iska kafa; suna aiki shi kuma yana kwashe musu kudade a wofi!  Akwai dalilai da dama da ke haddasa wannan mummunan ta’ada ta sace wa mutane kudade ta irin wannan hanya mai ban mamaki.  Da farko dai, masu yin wannan aiki ‘yan dandatsa ne, watau ATM Hackers.  Sunan wannan mummunar sana’a tasu kuma shine ATM Skimming, a Turance.  Kamar yadda ake da ‘yan dandatsa a harkar kwamfuta, to haka ake da su a bangaren tsarin ATM.  Masu wannan aiki kuma sun samo fasahar yin hakan ne ta hanyoyi biyu; ko dai ta amfani da kwarewa irin ta kwakwalwarsu kan harkar sata, ko kuma ta hanyar koyon ilimin yin hakan daga kasashen Turai inda wannan aiki yayi kaurin suna, ta hanyar Intanet.

Hanyar farko da suke bi ita ce ta hanyar kera katinan ATM makamantan wadanda bankuna ke bayarwa, amma na bogi.  Sai dai kuma duk dabararka ba za ka iya gane bambanckin da ke tsakaninsu ba.  Daman katin holoko ne.  Idan kamfanin INTERSWITCH ya aika wa bankuna, sai su kuma su kirkiri lambobi da kuma kalomomin iznin shiga (PIN Cord) na wuin gadi da suke baiwa kwastomominsu.  Shi yasa idan kaje karbar katin, sai a ce ka jira (a wasu bankunan kenan).  Za a je ne a darsana wa katin wasu sinadarai masu dauke da wadannan lambobi da bankin ke bayarwa, ta hanyar wata na’ura da suke amfani da ita, kamar dai yadda kamfanonin wayar salula ke darsana wa katin SIM lambobin wayar da suke sayarwa.  Asalin katin ai holoko ne.  Sai an darsana masa wadannan sinadarai sannan za ka iya amfani da shi.

Don haka idan suka kera wadannan katuna, abu daya kawai ya rage musu.  Wannan abu kuwa shine na’urar da ake amfani da ita wajen darsana wadannan bayanai masu dauke da lambobin taskar masu ajiya.  A nan ne fa gizo ke sakar.  Su kadai suka san hanyoyin da suke bi wajen satar bayanan taskokin ajiyar mutane.  Suna iya samun haka ta hanyar satar katin wasu, su tace bayanan da ke ciki ta hanyar kwamfuta, sannan su ci gaba da tatsar mai taskar, ko da kuwa an bashi wani katin.  A wasu lokuta kuma suna amfani ne da dabarun satar bayanan sirrin mutane, ta hanyar lekenka a yayin da kake kokarin cire kudi.  Suna iya tsayawa a bayanka, gab da kai, ta yadda suna iya ganin wasu kalmomi ko haruffa ka danna don cire kudinka.  Idan suka san wadannan, sun gama komai. Ba sai sun saci katinka ba, a a.  Suna iya amfani da wani katin holoko, don aiwatar da wannan aiki cikin sauki.  A wasu lokuta kuma, suna iya samun bayanai daga jikin ‘yan rasitin da ake watsarwa a farfajiyar bankin.  Da dama cikin mutane basu san tasirin barin rasitin taskarsu ba a yayin da suka cire kudi, duk da cewa sun baiwa mashin din umarni da ya ciro musu bayanai kan abinda ya rage a cikin taskarsu bayan kudin da suka cire.  Har wa yau, a wasu lokuta masu wannan ta’ada na iya dasa wata ‘yar karamar na’ura mai satar bayanan sirri a daidai wurin da ake shigar da katin.  Da zarar ka gama cire kudadenka, wannan na’ura za ta taskance bayanan da kayi amfani dasu.  Su kuma sai su zagayo daga baya su cire, don tace bayanan da ke ciki.  Sun fi yin wannan a wuraren da babu cikakkiyar tsaro.

Sabuwar hanyar da suka sake bullowa da ita kwanan nan kuma ita ce rudar mutane (musamman ‘yan Nijeriya masu akwatin wasikar sadarwa ta Imel) ta hanyar Intanet.  Suna yin hakan ne ta hanyar sakonnin bogi, watau Spam Mails.  Sakonnin sata da zamba cikin aminci, wadanda ake aiko wa mutane ba tare da su suka bukace su ba.  Kwanakin baya akwai labarai da suke ta kai komo cikin biranen Abuja da Legas cewa wasu ‘yan Dandatsa sun afka wa kwamfutoci da kuma na’urorin kamfanin INTERSWITCH, inda suka saci bayanan sirrin mutane, suka yi ta ta’addanci wajen wawashe musu kudade.  Wannan ya tilasta wa da yawa cikin bankunan da ke wadannan birane biyu sauya tsarinsu na ATM, inda suka caccanza wa dukkan masu rike da katinan ATM dinsu kalmomin iznin shigarsu (PIN Cord).  Daidai lokacin da wannan abu ke faruwa naje don cire kudi na ta amfani da katin da daya cikin bankunan da nake mu’amala dasu ya bani.  Nan take na kasa shiga.  Aka ce mini wai kalmomin da na shigar ba daidai suke ba.  Don haka sai na shiga ciki, inda na samu jami’in da ke lura da wannan fanni, shine yake min bayani makamantan rade-radin da nai ta ji a baya.  To sai masu wannan ta’ada ta Intanet suka dauki wannan dalili don rudar mutane ta hanyar sace musu kalmomin iznin shiga da kuma bayanan taskarsu, cikin sauki.

- Adv -

Yadda abin ya faru kuwa shine, na shiga akwatin wasikar hanyar sadarwata ta Imel ranar litinin, 15 ga watan Janairun 2009, sai na ga sakon Imel wai daga kamfanin INTERSWITCH zuwa gare ni.  Abin ya bani mamaki.  Yaushe na fara alaka da kamfanin kai tsaye, balle har ya san adireshin Imel di na?  Sai dai na bude.  Nan take na samu sanarwa cewa wai kamfanin na kara inganta hanyoyin mu’amalarsa da kwastomominsa ne, don haka ake sanar dani don amfanin kai na, da in yi maza-maza wajen bayar da wasu bayanai da suka shafi katin ATM dina don tsira daga ‘yan Dandatsa.  A kasan bayanan naci karo da rariyar likau, wacce aka ce in bi don ta kai ni shafin da zan bayar da bayanan da ake bukatar in bayar.  Ina ganin haka sai mamaki ya kama ni.  Da na duba kirjin sakon (watau Header), sai na gane sakon bogi ne.  Wasu ne kawai ke son satan bayanan sirri na cikin sauki, don su rika yashe min taska ta ba tare da wani gumi ba.  A saman sakon babu adireshin Imel dina a matsayi na na wanda aka aiko wa sako, sannan babu adireshin kamfanin INTERSWITCH, a matsayinsu na masu aikowa.  Sai dai na bi rariyar, inda ta kai ni shafi mai dauke da wuraren shigar da bayanai: suna na, da lambobin iznin shiga na, da adireshin Imel dina, da lambar tarho dina, da kuma lambar da ke dauke a jikin kati na.  Ina shiga wannan shafi, sai manhajar da ke lura da kwayoyin cutar kwamfuta da ke kwamfutata ta sanar dani nan take, cewa ta cafke wani kwayan cutar kwamfuta (watau Computer Virus) guda daya, ta kone shi har lahira. Nan dai na tabbatar da cewa sakon bogi ne, kuma barayin Intanet ne ‘yan Nijeriya ke amfani dashi wajen yaudarar mutane don sace musu kudade cikin sauki.  Sai na zarce zuwa gidan yanar sadarwar kamfanin INTERSWITCH don tabbatar da gaskiyar wannan sako ko rashinsa.  Ina zuwa zauren gidan, sai aka min barka da shigowa da wata sanarwa ta gargadi kan barayin Intanet masu yaudarar mutane, da kuma cewa idan na sake na basu bayanan kati na, to ni na sano.  Daga nan na ci gaba da samun ire-iren wadannan sakonni a sigogi dabam-daban.  Sai na samu natsuwa kan hukuncin da na yanke.

Me Ya Kamata Mu Yi?

To me ya kamata mai ajiya a banki, mai kuma amfani da katin ATM ya kamata yayi a irin wannan yanayi da lokaci mai cike da rudani makamancin wanda muka karanta a baya?  Akwai abin yi da dama; daga wanda zaka iya yi a matsayinka na mai amfani da katin, zuwa matsayin da bankuna zasu dauka, tare da na Hukumomin Gwamnatin Tarayya masu lura da wadannan bankuna.  Da farko dai idan kana rike da wannan kati kuma kana son ci gaba da amfani dashi, to dole ne ka rika adana shi sosai.  Kada ka bari wani ya san kalmomin iznin shiganka sai wanda ka amince masa.  Sannan idan kazo zaban kalmomin iznin shiga da zaka rika amfani dasu wajen aiwatar da cire kudade ko wani abu dabam, to ka guji yin amfani da lambobin ranar haihuwarka.

Da dama cikin mutane kan yi amfani ne da kwanar watan ranar haihuwarsu (date of birth), wanda kuma hakan shi yafi saukin ganewa wajen wadannan ‘yan ta’adda.  Bayan haka, idan kana da katin sai ya bace, to maza ka garzaya zuwa ofishin ‘yan sanda ka sanar, don a baka takardar sheda kan haka, sannan kaje kotu da kuma bankin da kake ajiya dasu, don sanar dasu halin da katin ya shiga.  Idan ka bata lokaci, duk wanda ya sace katin ko ya tsinta, akwai yiwuwan iya amfani dashi dari-bisa-dari.  Amma idan ka kai kara nan take, za a canza maka wani, a kuma bata dukkan bayanan da ke wancan dayan don ya zama kai kadai kawai ke da damar shiga taskar.  Idan ka zo cire kudi, ka rika lura da yanayin mutane. Idan ka ga mutum ya like maka a layi wajen cire kudi, to dole ne ka canza wuri, ko kuma a kalla ka bashi damar ya yi abinda ya zo yi, in ya gama, sai ka cire kudinka.  A kul ka amince wani na like da kai a kafadarka, lokacin da kake danne-dannen cire kudi.  Sai ya sha ka musilla baka sani ba.

Haka kuma, ka lakanci siffar mashin din da kake cire kudi daga gareta, idan wuri daya kake zuwa a kullum.  Duk ranar da ka ga yanayin ta ya canza musamman wajen sanya katin nan, to kayi hattara.  Bayan haka, idan ka san baka bukatar rasiti, to kada ka umarci mashin din da ya fitar maka.  A karshe idan ka daina amfani da katin, to ko dai ba mayar da shi ne zuwa ga bankin da ya baka, ko kuma ka kona ko binne shi gaba daya.  A daya bangaren kuma, idan hankalinka bai kwanta ba, to kada ka karbi katin.  Ka hakura da zuwa bankin don cire kudinka kawai.  Idan kuma kana da taskokin  ajiya guda biyu a banki daya, to a kul ka kuskura ka hada su cikin kati guda.  Ka bar daya mai kati, dayan kuma haka kawai. Wannan zai sa duk lokacin da kaji al’amura sun rikice na sace-sace, sai kawai ka kwashe kudadenka daga taskar da ke da kati zuwa wacce bata da shi.  Ka kuma tsare katinka sosai, idan kana da yawan mantuwa ka samu wani wuri na musamman don boye shi, kada ka yar dashi a halin kai-komonka.  Idan kana mu’amala da fasahar Intanet, duk wanda ya aiko maka da sakon Imel cewa ana son ka bayar da bayanai kan katinka, to dole ka yi hattara da ire-iren wadannan sakonni.  Idan a kwamfutarka kake karanta sakon, kada ma ka bude.  In kuwa ba haka ba, to akwai yiwuwar kwamfutar za ta kamu da kwayoyin cutar kwamfuta masu hallaka ruhin ko haukatar da ita.  Don haka a yi hattara ta kowane fanni.

A bangaren bankuna kuma, tabbas an san ba lallai bane su dauki dawainiyar hasarar da mutane suka yi musamman wanda ya shafi sakaci wajen adana kati da bayanan da suka shafi hakan, wanda kuma hakan ke haddasa irin wannan ta’ada mummuna, amma kuma dole ne su dauki dawainiyar ilimantar da kwastomominsu kan muhimmancin tsaro.  Duk sanda suka samu labara kan wata badakala da wasu ke yi wajen sace-sace a wannan tsari, dole su sanar dasu.  Domin a yanzu dai kam babu wannan hanya ta ilmantarwa ko kadan.  Wannan bai kamata ba.  Sannan dole ne su sanya tsaro sosai wajen wadannan mashina na ATM, su rika lura da wadanda ke lazimtar wajen a kullum ba don zuwa cire kudi ba, sai dai kawai su zauna a gefe suna lura da jujjuyawar mutane.  Wannan bai kamata ba ko kadan.  Hukumar babban bankin Nijeriya ma tana da nata hakkin da ya kamata ta rika lura dashi.  Shine ta tilasta wa wadannan bankuna, tare da kamfanin INTERSWITCH ganin suna amfani da hanya mafi inganci wajen tsare dukiya da bayanan mutane a dukkan na’urorinsu.  Hukumar EFCC ma tana da nata hakkin, wajen ganin ta samo hanyar cafke masu rudar mutane ta hanyar Intanet.  Da wannan, sai kayi amfani da katin ATM dinka lafiya.  Amma idan ba haka ba, to da sauran rina a kaba!  Allah Ya tsare mu, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.