Munanan Tasirin Makamin Nukiliya a Duniya

Makamin nukiliya yana da hadari matuka, saboda irin sinadaran da yake dauke dasu masu guba. A wannan mako mun gudanar da bincike ne kan tasirin wadannan sinadarai masu guba.

434

Munanan Tasirin Makamin Nukilya

Makamin nukiliya, kamar yadda bayanai suka gabata a sama, na tattare ne da sinadaran kimiyya masu matukar illa ga rayuwa, musamman lokacin fashewar makamanin a wani wuri da aka harba ko jefa shi.  Wannan ke wajabtar da samuwar illoli da dama ga rayuka da muhallin da makamin ya fashe.  Muhalli ya shafi iskar da ake shaka a bigiren, da duwatsu ko tsaunukan da ke wannan muhalli da kuma teku ko koguna ko rafuka.  Duk idan makamin ya fashe, zai shafe su mummunar shafa, tare da yada illolinsa ga duk wani abin da ya ta’allaka dasu; dabba ce mai rai ko wani abu dabam.

Da zarar an harba ko jefa makamin nukiliya a wani wuri, gari ne ko dajin Allah ta’ala, akwai abubuwa guda hudu da ke haddasuwa da zarar makamin ya fashe.  Abu na farko shi ne kara mai tsananin firgitarwa, wato Blast a turance.  Wannan kara mai tsananin firgitarwa shi ya kumshi kashi arba’in zuwa hamsin (40% – 50%) na bala’in da ke tattare da wannan makami mai narkar da rayuwa da muhalli.  Har wa yau, yawa ko karfin wannan kara mai firgitarwa ya ta’allaka ne da yanayin makamin wajen kerawa. Makamin da ke cike da sinadaran makamashin nukiliya mai dimbin yawa yafi haifar da kara mafi girma da firgitarwa.  Babban abin da ke haddasa wannan kara mai firgitarwa yayin fashewar makamin nukiliya su ne wasu dimbin makamashin sinadaran kimiyya masu dauke da maddar kimiyya masu tsananin hadari ga rayuwa da muhalli.  Idan fashewa ya auku, zai haifar da wannan kara, wanda ke kumshe da iska mai bala’in tunkudowa don raunana dukkan wani abin da ta riska, tare da tarwatsa shi nan take babu kakkautawa.  Wannan kara mai dauke da wannan iska mai bala’in tunkuda na haddasuwa ne cikin ‘yan dakiku (seconds), amma tasirinsu wajen tarwatsa muhalli da abin da suka darkake, ya zarce na dukkan wata mahaukaciyar guguwa mai dauke da iska (hurricane) da aka taba samu a duniya.  An kiyasta cewa karfin wannan kara mai firgitarwa na iya kwantar da dukkan gidajen da ke bigiren da fashewar ta auku.  Haka idan akwai hanyar dogo (jirgin kasa) a wajen, karar na iya daukan taragon jirgin ta jefar dashi wata duniya dabam.

Abu na biyu cikin abubuwan da fashewar makamin nukiliya ke haifarwa shi ne wani haske mai dauke da tururin guba ko sinadaran kimiyya masu illa ga muhalli da rayuwa.  Wannan shi ake kira Thermal Radiation a turance, kuma yana fitowa ne da zarar wancan kara mai firgitarwa ya haifar da makamashin maddar kimiyya zuwa muhalli, wanda ke dabaibaye dukkan ilahirin wuri ko bigiren da fashewar ta auku cikin kasa da dakika guda.  Wannan nau’in makamashin haske mai dumi da ake kira Thermal Radiation shi ne ya kumshi kashi talatin zuwa hamsin (30% – 50%) na makamashin da fashewar makamin nukiliya ke haifarwa.  Kuma wannan tururin haske ya kumshi nau’ukan haske ne guda uku; na farko shi ne asalin haske irin na rana da ido ke iya jure ganinsa, wanda muke dashi a nan duniya kenan (wato Visible Light), sai kuma nau’in hasken da ido baya iya jure kallonsa, saboda gundarin haske ne mai cike da makamashi mai dimbin yawa (wato Ultraviolet Light), na karshe kuma shi ne nau’in haske mai dauke da makamashin Infra-red, wato hasken da ke kasa da ganin dan Adam, amma yana nan kuma yana da tasiri matuka ga muhallinsa da kuma jikinsa.

- Adv -

Wadannan nau’ukan haske na cikakken tasiri wajen haddasa makantar wucin-gadi (na tsawon mintuna arba’in), ko tabbatacciyar makanta.  Hakan ya danganta da kusancin mai idon da kuma wajen da aka samu fashewar makamin ne.  Domin haske ne da ke shiga jiki ko duk abin da yayi karo dashi, tare da mannewa ko tabbata a jikin, bayan tasirin kuna mai tsanani da ya mallaka.  Bayan dukkan wannan, tururin hasken Thermal na iya gurbata dukkan iskar da ake shaka da zarar ya fito, tare da haddasa maganadisun lantarki cikin iskar (Electromagnetic Shockwave), mai cikakken tasiri ga dukkan wani jiki, kamar yadda mayen-karfe (magnet) yake da sauran karafa!  Da iskar da ke muhallin, da rafi ko kogi ko tekun da ke muhallin duk zai gurbata su.  Kai hatta dutse ko wani tsauni dake wannan wuri yana iya samun nasa rabon.  Idan ya samu damar saduwa da jikin dan Adam, ya kan raunana dukkan gabobinsa, ya haifar da mummunar illa ga kasusuwa da bargonsa, sannan ya karya wa jijiyoyinsa dukkan lagonsu, bayan haka, yabi mabudan hanji ko tumbi, da huhu da kuma gangar kunne, duk ya bata su ta hanyar rubar da su nan take!  Abu na karshe da wannan tururin haske ya mallaka shi ne haddasa gagarumar gobara a muhallin da fashewar ta auku.

Abu na uku da ke haifuwa sanadiyyar fashewar makamin nukiliya shi ne tururin hayaki mai haifar da sinadaran kimiyya nau’in ayon, ko kuma ionization a turance.  Wannan tururin haske aikinsa shi ne ya haifar da sinadaran madda masu tattare da maganadisun lantarki (Electromagnetism), masu taimaka wa tururin hasken Thermal da bayaninsa ya gabata, don gurbata yanayin gaba daya, da hana dukkan wani abin halitta sararawa.  Wannan nau’in tururin haske na ayon shi ne kashi biyar (5%) na makamashin da makamin nukiliya ke fitarwa da zarar ya fashe.  Wadannan nau’ukan tururi guda biyu, da zarar sun watsu cikin muhalli sanadiyyar fashewa da aka samu na makamashin nukiliya a wurin, to garin baya iya zaunuwa har abada.   Wannan shi ne abin da ya faru da mutanen birnin Pripyat da ke kasar Yukiren (Ukraine), lokacin da wata masana’anta ko cibiyar nukiliya ta fashe, dole suka bar garin, don bazai zaunu ba.  Saboda dukkan iska da ake shaka, da ruwa da ake sha da kuma muhallin shi kansa, duk sun gurbace matukar gurbacewa; wata halitta mai rai bata iya jure zaman wurin, balle ta amfana da abin da ke muhallin wajen gaba daya.  Dole garin, duk da girma da kuma kayan alatun da ke cikinsa, ya zama fako, kowa ya gudu.

Ire-iren wadannan garuruwa da ke samun kansu cikin wannan hali ana kiransu Nuclear Ghost Town a turanceNau’in abin da ke samuwa daga fashewar makamin nukiliya na karshe shi ne hayaki mai dauke da haske, wanda ke tudadowa don mamaye ilahirin muhalli ko bigiren da fashewar ta auku.  Wannan hayaki, wanda dan Adam na iya ganinsa, yana fitowa ne tare da masifaffen karar fashewar makamin, a matsayin wata gagarumar da’ira ta hayaki, wacce ke haurawa sama don yada dukkan sinadaran tururin hasken da bayaninsu ya gabata a baya.  Da zarar wannan hayaki yayi ziri zuwa sama, sai ya warware yayi lema, don tarwatsawa da yada wadannan sinadaran guba, wadanda ke gurbata muhalli gaba daya.  Wannan tarin hayaki shi ne ke daukan kashi biyar zuwa goma (5% – 10%) na yawan makamashin da makamin nukiliya ke fitarwa yayin fashewarsa.  To me ye kimar hasarar da ke iya shafan rayuka ko ababen da ke kusa da wajen wannan fashewa?

Duk lokacin makamin nukiliya nau’in Atomic Bomb ya fashe a wuri, duk wani abin halitta – ko gida ko dutse ko tsauni ko wani teku – da ke kusa da wurin fashewar da gwargwadon nisan mil guda, zai hallaka gaba daya.  Babu abin da za a samu mai amfani tattare dashi.  Idan kuma nau’in Hydrogen Bomb ne, duk abin da ke gwargwadon mil biyar ko nisan kilomita takwas zai hallaka nan take.  Domin Hydrogen Bomb yafi Atomic Bomb masifa wajen hasarar rayuka da muhalli.  Bayan nan, idan kuma nisan da ke tsakanin wata halitta ko gine-gine ya kai mil daya da digo biyu, ko gwargwadon kilomita biyu kenan, to zai samu mummunar illa wanda zai sa a gwammace rasa shi ma gaba daya.  Idan kuwa nau’in Hydrogen Bomb ne, duk wanda ke iya nisan kilomita bakwai da fashewar na iya samun wannan mummunan illa.

Idan, a daya bangaren kuma, fashewar ta uku a nisan kilomita uku ne, to duk wanda ke kusa da wajen iya takin wannan nisa na samun illa mummana wacce bata kai mutu-kwakwai-rai-kwakwai ba.  Irin wannan illar na iya samun wanda ke nisan kilomita goma shabiyar tsakaninsa da fashewar Hydrogen Bomb.  A karshe, halitta na iya samun takaitattun raunuka ko ‘yar karamar dameji, idan gine-gine ne, muddin aka samu tazarar kilomita biyar tsakaninta da wajen fashewar makamin nukiliya nau’in Atomic Bomb, ko kuma nisan kilomita ashirin da bakwai idan nau’in Hydrogen Bomb ne.  Wadannan, a takaice, su ne kadan cikin bala’i ko masifar da ke dauke cikin makamin nukiliya.  Kuma duk da yake kusan kowace kasa na burin kera wannan makami, amma Majalisar Dinkin Duniya tace kowa ya mayar da wukarsa cikin kube, ta haramta kerawa balle yada wannan makami.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.