Nau’ukan Fasahar Sadarwa a Intanet (2)

 Mun fara kawo mukaddima a makon da ya gabata kan nau’ukan fasahar sadarwa da ke giza-gizan sadarwa na Intanet.  Inda muka fara da irin dalilan da suka haddasa yaduwar nau’ukan wadannan hanyoyin sadarwa a Intanet, duk da cewa suna da nasu muhallin da su ke ta taka rawa shekaru kusan hamsin da suka gabata.  A yau muka ce za mu ci gaba da koro bayanai kan ire-iren wadannan nau’ukan hanyoyin sadarwa, da tsarin da suke gudanuwa a kai da kuma yadda mai karatu zai iya amfana da wadannan hanyoyi ba tare da ya mallaki nau’urorin da ake sauraro ko saduwa da su ba.  Bisimillah, wai an hada Malamai kokawa:

275

Hanyar Sadarwa ta Rediyo

 Nau’in fasaha ko hanyar sadarwa da za mu fara bayani a kai ita ce hanyar sadarwa ta rediyo, wacce ke daga cikin tsoffin hanyoyin sadarwa a duniya.  Alal hakika kowa ya san cewa dole ne a mallaki akwatin rediyo don sauraron shirye-shirye irin su labarum duniya da sauransu.  Amma wani zai yi mamaki matuka idan ka ce masa akwai wani tsari a duniya in da zai iya sauraron shirye-shiryen gidajen rediyo ba tare da ya mallaki akwatin rediyo ba, musamman idan bai taba jin labarin fasahar sadarwa ta Intanet ba da irin yadda take gudanuwa.  Akwai hanyoyi da dama da suke bi wajen yada labarai da shirye-shiryen yau da kullum.  Kafin nan, gidajen rediyo masu yada shirye-shiryensu a Intanet sun kasu kashi-kashi.  Kashin farko su ne gidajen rediyo masu tsarin FM, wadanda kuma galibi wake-wake su ke sanyawa ga dukkan masu sauraronsu.  A gidajen yanar sadarwan su idan ka je, za ka samu hanyoyin sauraron wakoki iri biyu; na kyauta da kuma wadanda sai ka biya za ka samu isa zuwa gare su.

Wadannan galibi basu cika damuwa da gabatar da wasu shirye-shirye ba, kuma wakokin na su duk taskantattun wakoki ne; ma’ana an riga an tanade su a gidan yanar sadarwan, ba wai kai tsaye (Live) ake watso su ba.  Sai kuma bangaren masu yada labarai da sauran shirye-shirye a tsarin matsakaici da kuma gajeren zango, wato MW da kuma SW, wato manyan zangon yada shirye-shirye mafiya girma da shahara a duniya.  A ire-iren wadannan gidajen yanar sadarwa na rediyo, nau’ukan shirye-shirye kala biyu suke da su; akwai wadanda za ka saurare su ne kai tsaye, kamar yadda masu saurare daga akwatunan rediyon su suke sauraro su ma.  Ire-iren wadannan shirye-shirye galibi labarun duniya ne da kuma shirye-shirye masu kebantattun ranaku da suka shafi hira da baki da ake gayyata zuwa gidajen rediyon.   Sai kuma kalan shirye-shirye na biyu, wadanda taskantattu ne.  Su wadannan sun hada da wakoki da wasu shirye-shirye maimatattu.  A wasu lokuta kuma za ka samu dukkan shirye-shiryen da aka yi na baya an taskance su (archived) don masu ziyara.  Wadannan su ne nau’ukan gidajen rediyon da ake da su a giza-gizan sadarwa ta Intanet.

Abu na karshe da ya kamata mai karatu ya sani shi ne, wasu daga cikin shirye-shiryen da ke wadannan gidajen yanar sadarwa na rediyo za ka samu na saidawa ne (musamman a kasashen Turai da Amerika).  Idan ka je ka biya sai a budo maka su ka saurara ko ka ma diro da su a kwamfutarka, don sauraro a wasu lokutan.  Galibin gidajen yanar sadarwa na FM da ke Intanet duk sayar da wakokin su suke.  Kamfanin Apple da ke Amurka ce gaba-gaba wajen wannan sana’a.  Su wadannan gidajen rediyo ana kiran su Music On Demand Stations.  Ma’ana, tashoshin rediyon sayar da wakoki.  Akwai na kyauta tabbas, musamman gidajen rediyon BBC da VOA da DW Radio masu sashen harsunan kasashen waje, da kuma wasu gidajen yanar sadarwa na addinin musulunci masu zuba shirye-shiryen da’awa da ake watsawa a wasu gidajen rediyon Turai da sauran kasashen duniya, duk kyauta suke watsa shirye-shiryen su.  Kafin mu kai ga ambato adireshin wasu daga cikin ire-iren wadannan gidajen rediyo da ke Intanet, zai dace mai karatu ya san tsarin da suke bi wajen yada shirye-shiryen su, da yadda zai iya mu’amala da gidajen yanar sadarwan su idan ya samu kan sa a can.

Tsarin Gabatar da Shirye-shirye

 Idan ka shiga gidajen yanar sadarwa na gidan rediyo, akwai abubuwa da dama da watakil ba za ka gan su a fili ba, amma suna nan.  Abubuwa ne da ke da nasaba da fasahar tsara gidajen yanar sadarwa.  Da farko dai akwai jakunkunan bayanai na sauti, wato Sound Files, wadanda ke dauke da shirye-shiryen da ake taskancewa.  Wannan ya fi zama ruwan dare a gidajen rediyon sayar da wakoki.  Domin sun riga sun tanadi dukkan wakokin da suke saidawa.  Za kuma ka samu hanyar sauraron wadannan wakoki daga irin alamun da ke makale a gidan yanar, cikin sauki.  Wadannan jakunkunan bayanai an gina su ne a tsarin mp3 ko midi ko mov ko mpeg da dai sauran hanyoyin taskance bayanai masu sauti a Intanet.  Bayan haka, a kan girke su a rumbun adana bayanai na gidan yanar, wato web database.  Duk lokacin da ka shigo, ka bukaci sauraron shirye-shirye, Uwar Garken za ta miko maka su.  Idan kuma gidajen rediyon na watsa shirye-shiryen su ne kai tsaye, to akwai manhaja ko masarrafa da suke amfani da ita, wacce ke baiwa kwamfutarka daman miko maka bayanan iya gwargwadon yadda take karban su daga Uwar Garken gidan rediyon.  Shi yasa wasu lokuta za ka ji Mannir Dan Ali ko Alhaji Dauda Kulibali ko Aishatu Musa da ke sashen Hausa na Rediyon BBC suna cewa “. . .a yanzu za ku iya sauraron mu a mita na 41, da 26, da 49.  Ko kuma kai tsaye  ta hanyar sadarwa ta Intanet. . .”.  Duk da wannan tsari su ke amfani.

Tsari da Yanayin Sauraro

- Adv -

 Ga duk mai bukatar sauraron shirye-shiryen gidajen rediyon da ke Intanet, yana bukatar wasu makale-makale a kwamfutar da yake amfani da ita, idan ba haka ba, bazai iya sauraro ba.  Da farko kana bukatar diro da wasu manhajoji na musamman wadanda za su taimaka maka wajen sauraron shirye-shiryen.  Duk da yake dukkan kwamfuta kan zo da irin wannan manhaja, amma galibin gidajen yanar sadarwa basu cika damuwa da na kamfanin Microsoft ba.  Akwai irin wadannan manhaja da dama, wadanda a turancin Intanet a ke kiran su da suna Plug-Ins.  Akwai su Real Player (www.real.co.uk), wanda galibi a gidajen yanar sadarwa shi aka fi amfani da shi.  Sai kuma irin su Quick Time (www.apple.com).  Shi wanda ke zuwa cikin manhajar Windows, wato Media Player, shi ma yana da kyau, amma sau tari idan kaje wasu tashoshin za a ce maka sai kana da Real Player a kwamfutarka za ka iya sauraro.  Idan haka ta kasance, sai kaje gidan yanarsa da ke http://www.real.co.uk, don ka diro da shi, kyauta.  Idan ka samu wannan, sai kuma abin jin Magana, wato Speaker ko kuma Headphone.  Duk wanda ka ke da shi yayi.  Duk lokacin da ka matsa alama ko shirin da ka ke son sauraro, wannan manhaja za ta karbo maka shi ta kuma jiyar da kai dukkan abin da ke kumshe cikin sa.

Su wadannan manhajoji na Plug-Ins, musamman aka gina su don jiyar da sauti da hotuna masu motsi na Video ko Animations a kwamfuta.  Idan manhajar ta jawo jakar bayanin, za ta fara bugawa (playing), sai kuma “jami’an” da aka tanade su don sadar da ruhin jikin kwamfuta da gangar-jikinta (Drivers), su hada manhajar da abin jin magananka, wato Speakers ko Headphone da ka jona ma kwamfutar.  Haka za ka yi ta sauraro har sai shirin ya kare, ko kuma adadin mintuna ko sa’o’in da aka diba ma jakar sautin ya kai.  Idan ka sake ya katse, to dayan biyu; ko dai wayar kebul din ka ta cire, ko kuma yanayi ya sauya, ma’ana an fara ruwa ko kuma hadari ya hadu.  Idan duk babu dayan biyun nan, to watakil jakar da ke dauke da shirin ta lalace, kuma wannan manhaja da ke da hakkin jiyar da kai shirin, zai sanar da kai irin matsalar.

Gidajen Rediyon Harshen Hausa a Intanet

 Na tabbata galibin masu karatu a yanzu sun san cewa gidajen rediyo irin su BBC, Muryar Amurka (VOA), Muryar Jamus, da gidajen rediyo na kasar Sin da Faransa, duk ana iya sauraron su ta Intanet.  Wannan na daga cikin ci gaban da aka samu a wannan bangaren fasahar sadarwa na zamani.  Idan kana son sauraron labaru da shirye-shiryen Sashen Hausa na BBC ko Muryar Amurka, ko Muryar Jamus, abu ne mai sauki, muddin ka cika ka’idojin da aka zayyana a sama.  Za ka iya sauraron shirye-shiryen baya, da kuma wanda ake yi a lokacin da ake ciki (in har lokacin yin ne).  Sai dai, kamar yadda bayani ya gabata a sama, idan siginar Intanet ta dauke, za ka ji shirin ya yi tsit. Wannan wata dama ce ga wadanda ba su iya samun sauraron shirye-shiryen a kan lokaci.  Bayan haka, za ka iya sauraron wasu tashoshin BBC na turanci a wannan adireshi http://www.bbc.co.uk/radioIdan kuma na Sashen Hausa ka ke son sauraro, ka shiga nan: http://www.bbc.co.uk/hausa, sai ka nemi alamar da za ta sadar da kai da shafin shirye-shiryen a sauti.  Haka idan kana son sauraron na Muryar Amurka, wato Voice of America,  za ka samesu a nan: http://www.voanews.com/hausaNan ma sai ka nemi alamar da za ta sadar da kai da shirye-shiryen cikin sauti.  Har wa yau, za a samu na Muryar Jamus, wato Deustchewelle, shi kuma a wannan adireshin: http://www2.dw-world.de/hausaWadannan su ne shahararru cikin gidajen rediyon da ke shafin yana a Intanet cikin harshen Hausa.  Idan mai karatu ya ziyarce su, zai samu bayanai kan yadda zai yi mu’amala da jakunkunan da ke dauke da dukkan shirye-shiryen.

Neman Tashoshi  a Intanet

 A halin yanzu akwai gidan yanar sadarwa na Matambayi Ba Ya Bata da ke taimaka ma mai neman tashoshin rediyo don sauraren shirye-shirye da dama.  Duk da yake gidan yanar sadarwan Yahoo! na da na ta (za a same shi a nan: http://music.yahoo.com), amma idan kana son samun tashoshi daga dukkan kasashen duniya, za ka iya samu in har akwai tashoshin da suka bude shafin yana na watsa shirye-shirye a kasar.  Wannan shi ne ma hanya mafi sauki wajen neman tashoshi, kuma zai taimaka wajen neman wata tasha wacce ka san kasar da ta ke, amma kuma kuma baka san adireshin gidan yanar sadarwan ta ba.  Wannan gidan yana na neman tashoshin rediyo shi ake kira Radio Locator, kuma za a samu shafin gidan yanar a nan: http://www.radio-locator.comDuk tashar da ka ke so, a kowace kasa take, muddin ta bude shafin yana tana watsa shirye-shiryen ta, za ka samu har ka saurari shirye-shiryen su.

Kammalawa

 Daga karshe, yaduwar hanyoyin kayatar da gidajen yanar sadarwa wajen yada bayanai da sadar da su, shi ya haddasa samuwar nau’ukan fasahar sadarwa a Intanet, duk da cewa suna da na su muhallin tabbatacce.  Wannan har wa yau ke nuna irin tasirin da wannna fasaha ta Intanet ke da shi, wanda ya shanye na sauran nau’ukan hanyoyin sadarwan.  A mako mai zuwa in Allah Ya yarda, za mu ci gaba da kawo bayanai kan gidajen yanar sadarwa masu dauke da talabijin, ya Allah na cikin gida ne (local channels) ko kuma wadanda ake watsawa ta tauraron dan Adam, wato Satellite Channels.  Ina mika godiyar wannan shafi ga dukkan masu rubuto sakonnin gaisuwa da ban gajiya ko kuma bugo waya don yin hakan.  Allah Ya bar zumunci, amin summa amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.