NIGCOMSAT-1 Ya Samu Matsala A Cikin Falaki

Idan ba mance ba dai cikin lokutan baya ne hukumar Najeriya ta kaddamar da tauraron dan adam na musamman mai suna: NigComSat-1″, wanda aka tanade shi don samar da bayanai kan yanayi da sauransu. To a halin yanzu labari ya tabbatar da cewa wannan tauraron dan adam ya samu matsala cikin falaki.

169

Tauraron dan Adam da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta harba cikin falaki shekara da wasu watanni da suka gabata mai suna NIGCOMSAT-1, ya samu matsala a halin shawaginsa cikin falaki.  Hukumar da ke lura da tauraron, wato Nigerian Communication Satellite, ta bayyana haka cikin makon da ya gabata.  Hukumar tace ta gane hakan ne sanadiyyar yakewar sadarwa tsakanin tauraron na NIGCOMSAT-1, da kuma cibiyar da ke lura da shawaginsa a falaki, wanda hakan ke nuna cewa ya daina aiki sanadiyyar wasu matsaloli da ya ci karo dasu a cikin falakin da yake sulmiya.  Wannan, a cewar Hukumar, “shi yasa aka dakatar dashi.”

A farkon al’amari dai akwai jita-jita da ake ta yadawa cewa tauraron ya bace ne, ba a ma san inda yake ba cikin falaki.  Wannan tasa jama’a suka yi ta mamakin wannan zance mara kan-gado: “ta yaya za a ce ya bace, bayan harba shi aka yi, kuma ana lura dashi?”, a cewar wani bawan Allah mai suna Malam Murtala Baba Aminu Kalgo.  Amma daga baya sai Hukumar ta tabbatar da cewa ba bacewa yayi ba, ya samu matsala ne da fika-fikansa masu taskance masa makamashin hasken rana, wato solar panels, wanda hakan ke taimaka masa wajen cajin batirin da yake dauke da shi.  Wannan tasa injinsa ya tsaya, don batirin yayi rauni, baya iya juya injin da ke gudanar da tauraron gaba daya.  Ga al’ada kowane tauraron dan Adam na da hanyoyin samun wutar lantarki ne kashi biyu; akwai batir mai taimaka masa yin rayuwa cikin dare ko duk lokacin da wannan duniya tamu tayi masa shamaki daga hasken rana, da kuma fika-fikai biyu masu kallon rana.  Aikinsu shi ne taskance makamashin hasken rana, wanda tauraron ke amfani dashi kai tsaye, tare da taimaka wa batirin yin caji lokacin yini.

- Adv -

A karshe dai Hukumar ta baiwa kamfanonin da wannan matsala ta shafa hakuri, da kuma cewa kada su damu, za a sada su da wani kamfanin da zai ci gaba da basu bayanan da suke bukata, kafin gwamnatin Nijeriya ta samu wani tauraron daga kamfanin da ya kera NIGCOMSAT-1.  Wannan ke nuna cewa NIGCOMSAT-1 ya kwanta dama kenan.  Hakan ya haddasa kace-nace a tsakanin ‘yan Nijeriya masu lura da abin da ke kai ya kawo.  Shin wannan na nufin cibiyar da ke lura da wannan tauraro ba ta ganin shawagin da yake yi kenan a aikace cikin falaki, sai dai kawai ta samu sakonni daga gareshi?  Kenan ba don sun kasa samun sakonni daga tauraron ba, da shikenan, sai ya zama sharar cikin falaki (space junk), ba wanda ya damu.  Amma sai dai kuma sabanin yadda mutane ke zato, bah aka lamarin yake ba.  Kamfanin da ke lura da wannan tauraro dai ta dakatar dashi cikin falaki, cikin wani irin yanayin da kanikawansa zasu iya duba shi don gano cikakken dalilin da ya haddasa masa wannan tsayawa cikin kankanin lokacin.

Gwamnatin Nijeriya dai ta mallaki tauraron NIGCOMSAT-1 ne cikin shekarar 2007 ta hannun wani kamfanin sadarwa na kasar SIN (China), a kan kudin da kimarsa ta kai Naira Biliyon Arba’in (N40B).  Manufar mallakar wannan tauraro shi ne don taskance bayanan da suka shafi yanayi (Weather Forecast), da kuma taimaka wa kamfanonin sadarwa wajen yada bayanai.  Har wa yau, akwai gidajen rediyo na FM da ke amfani da wannann tauraro wajen yada shirye-shiryensu.  Wadannan kamfanonin sadarwa na biyan gwamnatin tarayya kudaden wannan aiki ne a duk farkon watanni hudu.  Yanzu haka akwai kamfanonin da suka biya kudi ba tare da sun amfana da ko harafi guda ba, sai tauraron ya kwanta dama.  Wannan tasa dole a hada su da kamfanin da zai basu bayanan da suke bukata, kafin a samu wani tauraron dabam.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.