Rayuwar Matasanmu a Dandalin Abota (2)

Ga kashi na biyu cikin jerin kasidunmu kan fadakarwa ga matasa. Wannan karon mun dubi yadda suke rayuwa a Dandalin Facebook ne musamman a cikin watan Ramala mai alfarma.

297

Babban Baƙo

A yau makonni hudu kenan cif-cif da shigan wannan wata na Ramalana mai alfarma, kuma mai tarin albarka.  Babu wanda ke da shakku kan muhimmancin wannan wata a duniyar Musulunci bakiɗaya.  Daga cikin masu nuna farin cikinsu, da sauya rayuwarsu don dacewa da yanayin watan, tare da neman ɗimbin tabarrakin da ke cikinsa, har da matasanmu, waɗanda ke kaikomo da’iman a duniyar kayayyakin fasahar sadarwar zamani; daga fasahar Intanet zuwa wayoyin salula; daga manhajar sadarwar Imel, da na Dandalin yin abota da sadar da zumunci, zuwa manhajar saƙonnin tes na wayar salula, da shahararriyar manhajar hirar ga-ni-ga-ka ta wayar BlackBerry, wato BB Chat.

A yau za mu dubi irin rayuwar da matasanmu suka yi ne daga kamawar wannan wata zuwa yau da ake sa ran ƙarewarsa ko gobe, in Allah ya yarda.  Don daɗa fahimtar yadda waɗannan kayayyakin sadarwar zamani ke tasiri a rayuwarmu baki ɗaya; shin, mu ne ke tasiri wajen sauya ma’amalarmu a cikinsu ko kuwa su ne ke yin tasiri wajen yin hakan?  Idan su ne, shin, mummunar tasiri ce ko kyakkyawa?  Sai a biyo mu kamar yadda aka saba.

Fasahar Intanet

Wajen ma’amala da fasahar Intanet a matsayin fasaha mai tasiri cikin hanyoyin sadarwar da ake tinƙaho da su a wannan zamani, matasanmu sun tsunduma tsundum wajen faɗakar da juna ne.  Idan muka koma kan tattaunawar da matasa ke yi a Majalisun Tattaunawa (Internet Groups) na ƙauyukan Intanet (Cyber Communities), za mu fahimci haka ƙarara.  Wasu kan aiko da saƙonnin faɗakarwa kan shigan wata, wasu kan falalar watan, wasu kan nau’ukan ibadar da ake yi ne a watan, wasu kuma kan ɗimbin ladan da aka tanada wa masu aikata alheri ne a watan.  Ana yin hakan ne ta hanyar kawo hujjoji daga ayoyin Ƙur’ani mai girma ko Hadisan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) ingantattu.  A wasu lokuta wasu hadisan da ake kafa hujja da su ba ingantattu bane.  To amma dai, duk ana yin hakan ne don faɗakar da juna, da neman tsira wajen Allah.  Kowa “Malam” ne a wannan wata, kowa “Mai wa’azi” a wannan wata, kowa ya zama mutumin kirki.

A majalisun tattaunawa na musamman irin su Majalisar Marubuta, da Majalisar Fina-finan Hausa, da Majalisar Hausa da Hausawa, da sauran makamantansu, duk jama’a kan ajiye wasu daga cikin maudu’in da aka kafa majalisar dominsa, su ɓuge da faɗakarwa na musamman kan wannan wata.  Masu lura da waɗannan majalisu basu cika tsaurara doka ba kan kauce wa maudu’i, duk saboda wannan wata mai alfarma.

Dandalin Abota da Zumunci

Haka lamarin yake a dandalin abota da zumunci na Intanet, musamman a Dandalin Facebook.  Kowa ya zama mai wa’azi. Akwai masu farkar da jama’a a duk talatainin dare, don su sahuru, kada su makara.  Akwai masu tashi “ƙiyamullaili” (sallar dare), ta hanyar Facebook.  Kana iya gane hakan ne daga saƙonnin da suke aikawa a shafinsu, cewa: “Anybody awake?”  Ma’ana, “Akwai wanda ke farke yanzu?”  Akwai masu sanar da faɗuwar rana, don a yi buɗe baki, ko shan ruwa, kamar yadda muka saba faɗa.  Bayan haka, akwai masu taimaka wa masu azumi da hadisi ɗaya a dukkan rana. Sukan aiko da hadisi kan wani aiki na ibada mahimmi da aka shar’anta a cikin wannan wata mai ƙarewa a yau ko gobe.  Bayan su, akwai majalisun tattaunawa da koyar da tarbiyyar rayuwar musulunci da kyawawan al’adun Bahaushe, inda ake gabatar da tafsirin watan Ramalana, duk a Dandalin Facebook.  A ire-iren waɗannan majalisu akwai malamai masu karantar da mambobin majalisar.  A duk wayewar gari sukan aiko ayoyin Ƙur’ani gundarinsu, sannan su yi sharhi kansu, don faɗakar da jama’a.  Duk mai neman ƙarin bayani kan yi tambaya kan abin da bai fahimta ba, don a masa bayani sosai ya gane.

A wasu majalisun kuma ana faɗakarwa ne ta hanyar gasar kacici-kacici, amma a fannin shara’ar musulunci, don fahimtar da jama’adunƙulallun nau’ukan ilimin da suka faku gare su.  Wasu lokuta kuma a kawo wasu labarai na abubuwan da suka faru haƙiƙatan, ko dai a Najeriya ko a wasu ƙasashe, don ƙarin faɗakarwa ga mambobin majalisar.

- Adv -

A yayin da wasu ke ƙoƙarin faɗakarwa, wasu kuma suna can suna ta raha.  Sukan gayyaci abokanansu zuwa shan ruwa amma ta shafin Dandalin Facebook.  Wasu kan aiko da hotunan nau’ukan abincin da za su ci ko suke ci, wasu kuma su aiko da hotunan wasu nau’ukan abinci mai daɗi daga wasu ƙasashe.  Wasu kan aiko da hotunan kayayyakin marmari don zolayar abokanansu.  Wata ne mai alfarma da galibi ake cikin raha hatta a Dandalin abota da zumunci, musamman Dandalin Facebook.

Akwai kuma waɗanda a kullum ba su da wani aiki, ba su da wani zance, illa cillo ayoyin Ƙur’ani zuwa shafukansu don amfanin kansu da na abokanansu.  waɗannan ayoyin Ƙur’ani dai daga wasu gidajen yanar sadarwar Intanet ne suke karɓo su, sanadiyyar rajista da suka yi a can.  Duk wayewar gari ko duk sadda suka ga dama, za su shiga shafin gidan yanar, su cillo ayar da suke buƙata zuwa shafinsu ba tare da wata matsala ba.  Yin hakan ya ƙaru matuƙa da shigan watan Ramalana.

A ɗaya ɓangaren kuma an samu raguwar yawaitan hotunar batsa da ashararanci, da zantuka marasa amfani, da kalmomi na rashin ladabi da a baya suka zama ruwan dare a tsakanin matasanmu da ke shawagi a shafin Dandalin Facebook.  Duk sadda wani ya ɗan yi fushi kan abin da aka masa, nan take sai a bashi haƙuri, idan ya ƙi amincewa, sai a tuna masa cewa a “Watan Rahama” fa ake, sai ya saduda nan take.  Hotunan ‘yan mata sun ragu, haka ma waɗanda samari ke aikowa.  Hotunan da suka fi shahara a tsakanin matasa su ne masu ɗauke da sunan watan Ramalana, ko dai cikin harshen Larabci ko cikin harshen Turanci, da hotuna masu nasaba da watan, da kuma wasu guraren ibada, kamar masallacin harami da ke Makka, da masallacin Madina, da dai sauransu alamu masu dangantaka da Musulunci.  A taƙaice dai, tsarin ‘yan uwantaka ya daɗa ƙulluwa a tsakanin matasa.  Kowa na ƙoƙarin kamewa wajen aikata wani abin assha a fili, saboda alfarmar wannan wata na Ramalana.  Da haka rayuwa za ta ci gaba da kasancewa da’iman, musamman a ɓangaren matasanmu, da al’amura sun gyaru matuƙa.  Amma ko a yanzu ma dai tubarkalla.

Wayoyin Salula

A ɓangaren sadarwar wayar salula ma an samu ci gaba sosai. Matasa sun shagaltu da nau’ukan ayyukan ibada wajen yaɗa sanayya kan hukunce-hukuncen da suka shafi wannan wata na Ramalana.  Ana sanar da shigan watan nan take saƙonnin tes suka fara shawagi a tsakanin matasa.  Bayan yinin farko yayi wafati, sai saƙonnin hadisai masu alaƙa da watan, don faɗakarwa.  Sai dai saboda bambancin tsari da yanayi da kuma mahalli, saƙonnin Dandalin zumunci da abota sun fi yawan maimaituwa, da yawa, da kuma gamewa.  Su kuma saƙonnin tes sun fi sauƙin ma’amala, da sauƙin samu, da sauƙin aikawa, ba tare da matsala ba.

Masarrafar BB Chat

Bayan masarrafar saƙonnin tes da ke wayar salula, akwai shahararriyar manhajar hirar ga-ni-ga-ka da ke nau’in wayarBlackBerry, wato BB Chat.  Wannan masarrafa ce ta musamman wacce ke taimakawa wajen aiwatar da hirar yanzu-yanzu, amma ta hanyar wayar BlackBerry. Galibin samari kan kusan kwana suna zance da ‘yan matansu ta hanyar wannan manhaja, idan su ma suna da wayar BlackBerry.  Ba komai ya sa haka ba sai don sauƙin ma’amalarsa, da cewa ko ba ka da ko sisi a wayarka, kana iya hira da duk wanda kake son hira da shi babu matsala.  A cikin wannan wata an samu ƙaruwar faɗakarwa ta wannan hanya sosai. Kowa ya zama mai wa’azi, mai faɗakarwa na musamman. Kuma tasirin hakan ya zama mai gamewa, saboda a kowane hali kake kana iya aiwatar da sadarwa, tunda ta wayar salula ne, kuma ba ka buƙatar sai da kuɗi a wayarka; a kwance kake a ɗaki, ko a tsaye kake a tashar mota, ko a zaune kake a falo, duk kana iya aiwatar da sadarwa cikin sauƙi.

Kammalawa

Daga bayanan da suka gabata, a tabbace yake cewa wannan wata mai alfarma da ke mana bankwana yayi tasiri matuka wajen sauya wa matasanmu rayuwarsu, kuma hakan ya fito fili cikin ayyukansu na bayyane (Allah kaɗai ya keɓanta da sanin abin da ke ɓoye). Wannan abin sha’awa ne, kuma da samari za su ci gaba da kasancewa haka, ko kwatanta rabin wannan sauyi da ya bayyana daga rayuwarsu cikin wannan wata, da rayuwa ta ƙara inganci, nesa ba kusa ba.  Muna roƙon Allah ya bamu dacewa cikin al’amuranmu baki ɗaya, ya karɓi dukkan ayyukan da muka gabatar cikin wannan wata da sauran watannin da suka gabata, da waɗanda ke tafe, ya kuma sa su zama tafarkin tsari a gare mu ranar Ƙiyama, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.