Rayuwata a Duniyar Sadarwa (1)

Takaitaccen tarihina ne wannan kan irin gwagwarmayar da na sha a fannin bincike kan kimiyya da fasahar sadarwa na zamani. Wannan kashi na daya kenan. A sha karatu lafiya.

661

Kashi 90 cikin 100 na mutanen da suka sanni a matsayin marubuci ko mai sharhi a fannin kimiyya da fasahar sadarwa, sun sanni ne da lakabin “Baban Sadik.”   Cikin wannan mako nake sanar da Maman Sadik cewa da yawa cikin mutane har yanzu basu san hakikanin suna na ba; “Baban Sadik” kawai suka sani.  Kai kace wannan shi ne lakabin da na faro rayuwata a duniyar kimiyya da fasahar sadarwa dashi.  Ko kadan!  Suna na “Abdullahi Salihu Abubakar” ne.  Sunan “Salihu” dake tsakiyar sunan,  sunan kakana ne.  Sunan mahaifina shi ne Abubakar Garba Salihu.  Allah gafarta masa, ya jikan dukkan musulmi da suka riga mu baki daya, amin.  To duk meye ma’anar wannan zance?

Manufar wannan maudu’i na yau shi ne nuna godiya ga Ubangiji Allah mafi baiwar masu baiwa, ba wai alfahari ko son riya ba.  Allah ya tsare mu da yin riya, amin.  Sai kuma sanar da ‘yan uwa hanyoyin da nabi, cikin kaddarar Ubangiji (wadanda ba tsara wa kaina nayi ba), har na shahara.

Mafari da Sanadi

Shekaru 14 da suka wuce ban san komai kan harkar sadarwar kwamfuta ko wayar salula ba.  Tsoron taba kwamfuta ma nake, duk da cewa ina aiki a hukumar da ake amfani da kwamfuta.  Wayar salula kam bata yadu ba, a takaice ma sai cikin shekarar 2000 aka baiwa kamfanonin lasisi; sannan ina Masinja.  Babban abin da ya fara hada ni da kwamfuta ko Intanet ita ce fasahar Imel; sadda na bukaci a aika mini wani sako zuwa gidan rediyon BBC (shirin koyon harshen Turanci mai suna: “The Learning Zone”), a shekarar 2001.  Sanadiyyar wulakancin da aka mini, tunda alfarma naje nema, sai raina ya baci.  Mako guda bayan wannan lamari sai na roki wani ya bude mini adireshin Imel.  A ranar na fara taba allon shigar da bayanai (Keyboard), a ranar na fara mu’amala da fasahar Intanet, ta hanyar Hotmail (www.hotmail.com).

Tun daga wannan rana nake ta kokarin fahimtar yadda kwamfuta ke aiki, da yadda ake sarrafa ta, da yadda ake aika sako ta cikinta, da kuma yadda ake mu’amala da bayanai cikin sauki.  Na yi ta shige-shige cikin shafukan Intanet da dama; wasu ma ba na iya tuna su ko kadan.  Wasu lokuta nakan saci hanya ne daga ofishinmu zuwa matattarar kwamfutoci da ke ma’aikatar (Computer Room, kamar yadda ake kiran ofishin), don kawai inyi mu’amala da kwamfuta.  Bazan taba mancewa ba, Oga na a lokacin idan aka zo mitin yakan ce:

- Adv -

“My problem with Abdullahi is that he has two offices; one is Treasury, the other one is Computer Room.  You better choose one office.” 

Sai a kwashe da dariya.  Ba ya jin dadin hakan, domin akan neme ni wasu lokuta a rasa; da an zo “Computer Room” sai a same ni ina kwankwashe-kwankwashen allon shigar da bayanai (Keyboard).  Amma a karshe hakan ya zama alheri gare shi, da kuma ofishin da nake baki daya.  Domin da zarar Sakatare ta yi tafiya ko tana hutu, da ni ake dogaro wajen rubuce-rubuce da sarrafa bayanai.

Wata Sabuwar Duniya

Ban san yadda aka yi ba rannan kwatsam sai kawai na ga an mini rajista a daya daga cikin Majalisun Tattaunawa na Yahoo!, wato Yahoo! Groups kenan.  Ban san waye ya mini wannan rajista ba, kuma ban taba damuwa da sanin ko waye ba.  Majalisar kuwa ita ce: Majalisar Fina-finan Hausa, wacce Farfesa Abdallah Uba Adamu dake Tsangayar Ilimi (a yanzu shi ne babban Darakta na Cibiyar Sadarwar jami’ar – Director MIS) ya kafa kuma yake shugabanta.  Na karu matuka da irin abubuwan da ake tattaunawa.

Bayan wannan majalisa, akwai majalisar Marubuta, da majalisar Hausa, da majalisar Hausa da Hausawa (duk na Farfesa Abdallah), da majalisar Matasa (Malam Bashir Nuhu Mabai), da Majlisar Nurul-Islam (Malam Magaji Galadima) da sauransu.  Wadannan “Majalisu,” kamar yadda muke kiransu, su suka fara wurga ni tsundum zuwa duniyar Intanet.

Zan ci gaba a kashi na biyu.

- Adv -

You might also like
2 Comments
  1. Nuhu Abdullahi Adamu says

    Allah yakara kaifin basira

  2. Muryar Hausa24 Online Media says

    Masha Allah

Leave A Reply

Your email address will not be published.