Rayuwata a Duniyar Sadarwa (3)

Takaitaccen tarihina ne wannan kan irin gwagwarmayar da na sha a fannin bincike kan kimiyya da fasahar sadarwa na zamani. Wannan kashi na uku kenan. A sha karatu lafiya.

357

Daga cikin abubuwan da suka taimaka mini matuka a rayuwata cikin wannan fanni na kimiyya da fasahar sadarwa akwai yawan karance-karance, da kuma samun shawarwari daga masana, da karanta tarihin magabata a fannin – irin su Bill Gates, da Paul Allen, da Steve Jobs, da David Filo, da Jerry Yang, da Larry Page, da Sargey Brin, da Tim Bernes-Lee, da Vincent Diof dsr.  Wasu lokuta nakan lullube kaina cikin dakin karatu inta kwamacala; inta gudanar da bincike kan abubuwa da dama ba tare da tsari ba.  Da zarar na fahimci na shiga rudu, sai in nemi shawara wajen masana.

Mashawarta…

Mutane uku ne ke halarto ni a zuciyata a duk sadda na shiga rudu.  Mutum na farko shi ne Farfesa Abdallah Uba Adamu.  Mutum na biyu kuma Malam Magaji Galadima, wanda shi ya dauki nauyin bitar littafin da na rubuta mai take: FASAHAR INTANET A SAWWAKE, tun shekarar 2009, amma har yanzu na kasa fitarwa.  Sai mutum na uku, wato Abdulrasheed Dan-Abu, wanda babban jami’i ne a sashen na’urorin sadarwa da ke ofishinmu.  Aboki ne.  Babban yaya ne.  Malami ne.  Sannan abokin shawara ne.  Farfesa Abdallah Uba Adam kan ce min, a duk sadda na tambaye shi: “Wasu ka’idoji zan bi don iya gudanar da bincike na ilimi?:

“Malam, babu wasu ka’idoji; abin da za ka kiyaye kawai shi ne, sakamakon bincikenka ya zama wani abu ne sabo, wanda a baya wani bai taba ganowa ba.”

Tabbas wannan shawara ta wadatar dani matuka a rayuwata.

Shirin “Google Localization”

- Adv -

Sadda na fara gane bakin zare na a duniyar Intanet, daidai lokacin kamfanin Google ya fara kokarin fadada manhajarsa zuwa harshen gida, wato: “Google Localization.”  Wannan ya faru ne bayan kaddamar da manhajar Imel mai suna “Gmail” da kamfanin yayi a shekarar 2005.  Wannan aiki na “Google Localization” ya kunshi mayar da dukkan manhajoji da masarrafan Google ne zuwa harsunan duniya, ciki har da harshen Hausa.  Sun yi shela ga duk wanda zai iya ba tare da sun bashi ko sisin kwabo ba, wato: Volunteers kenan.  Da na duba sai na ga zan iya.  Daman ina cikin wadanda suka fara gwajin manhajar Gmail a farkon fitowarta, sadda aka raba wa wasu daidaiku kuma kwararrun masana, sai kawai na dukufa.

Na dauki tsawon shekaru 3 ina wannan aiki a bangarena.  Bayan fassara kalmomin da ake son su rika bayyana a harshen Hausa (wato “Placeholders), na kuma bi fassararorin da wasu suka yi, na gyaggyara.  Wannan aiki ya taimaka mini fahimtar abubuwa da dama, da kuma bani damar gudanar da wani aiki makamancinsa a shekarar 2011.  Wannan aiki kuwa shi ne fassara kalmomi 3,200 da suka shafi babbar manhajar wayar salula (Mobile Phone Operating System) da wani kamfanin kera wayoyin salula ya bukaci muyi.

A bangaren Malam Abdulrasheed kuwa, shawarar da ya taba bani wacce bazan taba mancewa ba, ita ce:

“A duk sadda kake mu’amala da na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani, ka sa abubuwa guda biyu a ranka; farko, hakuri.  Na biyu kuma, ka shirya wa kundunbala wajen hasarar bayanai ko rikicewar na’ura a sadda ba ka tsammani.”

Lallai wannan zance haka yake.   Ban fahimci hakan a aikace ba sai cikin shekarar 2007, sadda wata baiwar Allah, marubuciyar Hausa dake karatu a Jami’ar Azhar dake kasar Masar ta nemi in agaza mata da bayanai cikin harshen hausa, kan wani aikin gida (Assignment) da aka basu mai take: “Bunkasar Adabin Hausa da Alakarsa da Adabin Larabci.”  Da naji haka sai na yanke shawarar gudanar da bincike na musamman da rubuta mata kasida cikakke kan haka.

Na kwashe makonni biyu ina bincike, tsakanin littattafan Hausa, da jaridu, da mujallu, har a karshe na zauna na rubuta kasida mai shafuka 14!  Sai da na gama rubuce wannan kasida a kwamfuta tsaf, zan aika, sai ma’adanar da na sa kasidar a ciki (Floppy Disk) ta gurbace.  Ya salaam!  Hankalina ya tashi, na fara gumi, duk sanyin A/C da ke ofis; na rasa yadda zanyi, kuma a ranar ake son kasidar, don wayewar gari za a gabatar.  Da kyar wani sakatare ya agaza mini, yayi amfani da wata dabara ya kwafe min kasidar daga cikin ma’adanar, sannan na aika mata.

Zan ci gana a kashi na hudu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.