Sakonnin Masu Karatu (2007) (1)

Ga wasu daga cikin wasikun masu karatu nan da suka aiko a lokuta daban-daban.  A sha karatu lafiya.

69

Wannan shafi ya samu tambayoyi guda uku daga wajen Malam Sanusi Sagir Tudun Murtala (elnusy111@yahoo.com), daya daga cikin masu karatu, kuma ga abin da yake cewa:

Don Allah wasu tambayoyi nake so ayi mun bayani a kan su tambayoyin sune:  Kamar yanda a internet cafe a ke sa lokaci kafin a iya amfani da kwamfuta, haka yake ma ga mai ita a gida?   Sannan don Allah ya ake zuba bayanai a yanar gizo-gizo….Bayan haka, wai akwai security da ake sa wa  bayanan?  Na gode


Da farko dai, idan masu karatu basu mance ba, a kasidar “Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake (Cyber Café), mun sanar da cewa galibin kwamfutocin da ake amfani da su wajen shiga Intanet, a kulle su ke.  Wannan kariya ne wajen tabbatar da cewa duk wanda ya sayi sa’a daya, to lallai sa’a dayan yayi.  Da zarar ka samu dakiku sittin, kwamfutar za ta rufe kanta.  Wannan shi ake kira “Cyber Lock” a turancin Intanet.  To amma idan kwamfutar gida ce, sai in ka saya ka sanya mata da kanka, domin manhaja ne mai zaman kan sa, ba wai sayan kwamfutar ake yi da shi ba.  In kana bukata sai ka saya ka sanya.  Amma ni ina ganin tunda ba kasuwanci kake da kwamfutar ba, naka ne, ka iya barin ta haka.

- Adv -

Sai Magana kan yadda ake zuba bayanai a yanar gizo-gizo, wato gidan yanar sadarwa kenan, wanda wasu ke iya shiga don karantawa, in na fahimce ka.  Zuba bayanai ya kasu kashi-kashi; akwai wanda za ka iya zubawa a matsayin dakunan gidan yanar sadarwa (Web Pages), a matsayinka na wanda ya mallaki wannan gidan yanar sadarwa.  Sai kuma Mudawwana.  Idan kana da Mudawwanar Intanet (Blog) nan ma za ka iya zuba ra’ayoyin ka wasu su karanta.  Ko kuma ka aika da kasidu ko ra’ayoyin ka zuwa wasu gidajen yanar sadarwa irin su Gamji.com don su buga a gidan yanar sadarwan wasu su karanta.  Duk wadannan hanyoyi ne na zuba bayanai a giza-gizan sadarwa na Intanet.

Sai tambayar karshe, wacce yake son sanin ko akwai wani Security da ake sa ma bayanan.  Kalmar “Security”, wacce ke nufin hanyar tsaro ko wata kariya da ake sanya ma bayanai a giza-gizan sadarwa na duniya na bukatar bayani ne mai tsawo.  A takaice abin da zan iya cewa shi ne “eh akwai kariya da ake sanya ma bayanai saboda kare su daga kwafowa ba tare da izni ba, ko kuma hana kwafansu ma gaba daya, ko da kuwa za ka ga bayanan, har ka karanta.

A wasu lokutan kuma, ba za ka san da bayanan ba, idan ba ka da iznin ganin su.”  Bayani kan wannan abu ne da zai cinye shafuka a nan.  Zan dakata sai in munasaba ta sake kawo mu.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.