Sakonnin Masu Karatu (2009) (10)

Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.

107

Salamu Alaikum, ina son na kwafi bayanai daga Mudawwanar “Fasahar-Intanet” zuwa waya ta, amma da zarar na fara, sai ta nuno min: “out of memory”.  Ya lamarin yake ne?  –  Khalil Nasir Kuriwa, Kiru, Kano: 07027275459

Idan haka ta kasance, hakan ke nuna cewa ma’adanar wayar salularka bata iya daukan yawan bayanan da kake son zuwa mata daga shafin da ka kwafo su.  Don haka ka tabbata kana da wuri ko ma’adana mai yawa da zai iya karban mizanin bayanan da kake son kwafowa zuwa wayar.  “out of Memory” na nufin mizanin ma’adanar wayarka yayi kadan ga bayanan da ka kwafo.  Da fatan ka gamsu.


Assalaamu Alaikum Baban Sadik, da fatan kai da abokan aiki kuna cikin koshin lafiya, Allah sa haka, amin.  Shin da gaske ne wai kamar yadda na’ura mai kwakwalwa ke harbuwa da cuta (virus infection), haka ma wayar salula (irinsu Nokia E-Series da makamantansu) ke harbuwa da cutar?  Kuma ko mutum zai iya sa wa wayarsa kariya, wato Anti-virus?  – Uncle B. Bash, Jimeta, Yola: 07069045367

Dubun gaisuwa da fatan alheri ga Uncle Bash, da fatan ana cikin koshin lafiya.  Tabbas haka ne; wayoyin salula na kamuwa da kwayoyin cuta kamar yadda kwamfutoci ma ke kamuwa.  Domin kusan duk tsarinsu iri daya ne.  Kai ba ma su kadai ba, hatta na’urorin janyo siginar tauraron dan Adam na zamani da muke amfani dasu wajen kallon tauraron dan Adam (wato “Satellite Receivers” ko “Decorders”), duk suna iya kamuwa da kwayoyin cutar.  Babban dalili kuwa shi ne, saboda tsari da kimtsin ruhin da suke amfani dashi duk iri daya ne.  Ana iya sanya wa wayar salula manhajar kariya da goge kwayoyin cuta, wato “Anti-virus”.  Akwai manhajoji na musamman da aka gina don wannan aiki.  Wasu kyauta ake samunsu.  Wasu kuma sai da kudi. 

Yana da kyau mai karatu ya san cewa samun wadannan manhajoji kyauta a wajen masu sanya abubuwa a wayar salula da muke dasu a biranenmu, ba zai iya kare wayar daga kamuwa ba, sai ana kara wa manhajar tagomashi ta hanyar Intanet, don tabbatar da cewa ta haddace sunayen dukkan kwayoyin cutar da ke rayuwa a zamanin da take.  Wannan shi ake kira “Virus Update”, kuma kana iya yin hakan ne ta hanyar manhajar, idan akwai ka’idar Intanet a wayar. Idan kaje inda ake yin “Update” din, ka matsa, za a shige da kai ne kai tsaye zuwa shafin kamfanin da ya kirkiri manhajar, don bai wa manhajar damar haddace sabbin sunayen kwayoyin cutar da bata sansu ba.  In kuwa ba haka ba, to babu wani amfani da za a samu na kariya, wai don an sanya ma waya wannan manhaja.  Da fatan ka gamsu.


Salam, don Allah ka taimaka min da inda zan yi da kwayar cutar kwamfuta a waya ta, wato Virus.  Don suna tayar min da hankali.  Ka huta lafiya!  –  08023672341

- Adv -

Shawarar da zan bayar ita ce, aje a samu masu gyarar wayar salula don su duba wayar.  Don a nan bazan iya sanin wasu dabi’u take nunawa ba balle in san shin kwayar cutar kwamfuta ce ta kama ta ko a a.  Amma idan aka je wajen masu gyara, suna iya fahimtar hakan.  Allah sa a dace.


Assalam Baban Sadik, Allah Ya kaddare ni da karanta kasidarka mai taken: “Hanyar Sadarwa ta Rediyo a Intanet”, wadda ka rubuta a jaridar AMINIYA tun watan Agustar bara (2008), kuma nayi murna musamman ma da na ga wanda ya rubuta ta musulmi ne.  Bayan haka, nayi Difloma kan Ilmin Kwamfuta amma har yanzu ban samu kwarewa mai zurfi ba a fannin Intanet, amma wasu hanyoyi suka kamata na bi?  Wassalam  – 08063446395

Malam barka da war haka, kuma mun gode da wannan sako na neman shawara.  Ya danganci abin da kake nema ko son kwarewa a kai.  Idan so kake ka dauki fannin Intanet a matsayin fannin kwarewa da cin abinci, sai ka sake neman makarantun da ake koyar da ilmin kwamfuta, don yin nazari na musamman a kai.  Idan kuma a matsayin fannin sha’awa ne kawai da motsa kwakwalwa, sai ka lazimci ziyartar gidajen yanar sadarwa don sabawa da fasahar.  Kwarewa kan fasahar Intanet ba karatu bane tsantsa, a a, aikata abin da aka koyo ne lokacin karatu.  Wannan, a takaice shi ne abin da zan iya cewa.  Ina kuma rokon Allah ya baka juriya da kwazo da dagewa kan abin.  Da fatar ka gamsu.


Malam Abdullahi nakan ji wasu suna cewa: idan jirgin sama yazo saitin tsaunuka, ana fahimtar jirgin yana girgiza.  Me ye gaskiyar lamarin ne?  –  Khalil Nasir Kuriya, Kiru: 07069191677

Malam Khalil barka da kokari.  Wato wannan Magana haka take:  lallai jirgi kan girgiza idan yazo saman tsauni a halin tafiyarsa.  Ba ma tsauni kadai ba, ko cikin hazo ya shiga akan samu irin wannan girgiza…kaji kamar a saman duwatsu kuke tafiya.  Duk wanda ya taba hawa jirgin sama, zai tabbatar maka da hakan.  Bayan wadannan wurare har wa yau, idan jirgi yazo saman teku ma, yana iya samun wannan cikas.  Babban dalilin da ke haddasa wannan cikas da jirgi ke samu kuwa shi ne idan iskar da ke sama ta kara kiba da tumbatsa zuwa sama ko kasa ko kuma gefen dama da hagu, sanadiyyar wani abin da ya tare ta a halin tafiyarta.  Misali, idan iskar da ke can sama na tafiya daga gabas ne zuwa yamma, a guje, da zarar taci karo da wani tsauni, nan take sai iskar ta takura wuri guda, tayi toroko zuwa sama, ko kasa, ko kuma gefen dama da hagu.  To idan aka yi sa’a (ko rashin sa’a) jirgi yazo saman wannan tsauni a daidai lokacin da iskar taci karo dashi, sai ya fara girgiza, saboda sauyin yanayin iska da ya samu.

Idan a baya yana tafiya ne lafiya lau, yanzu iskar da tsaunin ya kado zuwa sama, zai kara tunkuda jirgin sama ko kasa, ko kuma zuwa wani gefe daban.  Haka abin yake idan jirgi ya shiga cikin hazo.  Domin shigansa cikin hazon na sauya masa yanayin iskar da ya baro a kasa ko can sama ne.  Wannan tsari na sauya wa jirgi yanayin tafiyarsa sanadiyyar sauyin yanayin iska da ke sama, shi ne Malaman Fiziya (Physics) ke kira “Turbulence”.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.