Sakonnin Masu Karatu (2009) (8)

A yau ma ga mu dauke da wasu cikin wasikun masu karatu. Kamar yadda muka sha fada kwanakin baya, cewa za mu daina amsa maimaitattun tambayoyi, don kauce wa tsawaitawa.  Duk wanda ke son yin tambaya, in da hali, zai dace ya binciki kasidun baya da ke mudawwanar wannan shafi a http://fasahar-intanet.blogspot.com, don samun gamsuwa.  A halin yanzu ga wadanda kuka aiko mana nan makonnin baya:

93

Assalaamu Alaikum!  Ina matukar jin dadin wannan fili na Kimiyya da Fasaha, wanda shi ne kashi sittin cikin dari da ke ja na ina karanta wannan mujalla mai farin jinni.  Baya ga haka, dan Allah ina da tambayoyi guda biyu:  na farko, ina so inyi ajiya a Intanet di na, yadda kowa in ya shiga zai iya karantawa ya amfana.  Na biyu,  yaya zan dawo da duba imail di na a cikin waya, da kuma aika sako?  Da fatan za ka agaza Malaminmu, ka bani hasken da ka saba baiwa dalibanka.  Daga: Jamilu Nafsen (Marubucin ‘Yar’Auta), nafsiniya@yahoo.com – 08083503380

Malam Jamilu mun gode, kuma Allah saka da alheri.  Dangane da abin da ya shafi yin ajiya a Intanet, in na fahimce ka sosai, kana nufin samun gidan yanar sadarwa ne na kanka ko kuma Mudawwana (Blog) don yin hakan.  Dangane da gidan yanar sadarwa, kana bukatar wanda zai gina maka, sannan zaka iya loda dukkan kasidu ko bayanan da kake dasu, don wasu su karanta.  Idan kuma Mudawwana kake so, sai kaje gidan yanar sadarwa na Google da ke www.blogger.com/start, don yin rajista da bude naka Mudawwanar. Yin hakan kyauta ne, kuma kana iya yin rajista cikin minti ashirin ko ma kasa da haka.   Tambaya ta biyu kuma mun sha maimaita amsarta a wannan shafi, don haka in da hali, sai ka ziyarci shafin mu da ke http://fasahar-intanet.blogspot.com don samun kasidar.  Kana iya karantawa, tare da bugawa (printing).  Ko kuma in kana so sai in aiko maka da kasidar ta akwatin Imel dinka.  Sai naji daga gareka kenan.  Da fatan ka gamsu.


Assalaamu Alaikum Malam Abdullahi, da fatan kana lafiya, amin.  Hakika ni mai karanta filinka  ne; a duk mako ba ya wuce ni.  Kuma ina jin dadin bayananka sosai, don ina karuwa dasu.  Ba abin da zan ce sai dai “Allah Ya saka da alherinsa”.  Ina da wata tambaya da nake son Karin haske a kai, tambayar ita ce: a halin yanzu na fahimci cewa duniyar nan tamu kamar kwai take, a sararin samaniya.  Misali, idan aka tona kasa har zuwa karshenta: aka wuce duwarwatsu da sauransu, teku za a samu ko me?  Nine Aminu TYT, Kanon Dabo: 08078719722

Malam Aminu barka da wannan sako naka, kuma mun gode da gaisuwarka ta yabo da gamsuwa.  Abin da yake tabbace na binciken Kimiyya kan wannan kasa da muke rayuwa akai dai bai wuce bayani kan bangarorin da wannan duniya ke dauke dasu ba, tare da sinadaran da ke cikinsu.  Na farko shi ne sararin samaniya; watau sararin da ke dauke da haske da kuma iskar da muke shaka, daga doron kasa zuwa samaniya. Wannan bangare ne ke dauke da iska da haske da sanyi da zafin ranar da ke haskowa daga muhallinta.  Sai kuma doron kasar da muke takawa, wanda ke dauke da bangarori guda uku:  na farko shi ne muhallin da ke mamaye da ruwa na teku ne ko rafuka ko kuma gulabe, da duk dai inda ruwa yake makare dashi a doron wannan kasa, shi ke kumshe da bangaren farko. 

Na biyu kuma shi ne gundarin kasa, inda dan Adam zai iya takawa, ya noma, ko ya tona.  Wannan bangare ya hada da duwatsu dake saman kasar da kuma muhallin da ke karkashin teku na gundarin kasa (watau “Ocean Floor” kenan a Turance).  Wannan shi ne bangare na biyu. Na uku kuma shi ne duk wani muhalli mai iya daukar halitta mai rai:  a sararin samaniya yake (watau bangaren farko kenan) ko a cikin teku muhallin yake da gundarin kasar da muke takawa?  In dai halitta na iya rayuwa a ciki, to shi ne bangaren wannan duniya na uku. 

Sai kuma bangaren cikin kasa, can ciki kenan.  Shi ma ya kasu kashi uku.  Sai dai dukkan bangarorin na kunshe ne da sinadaran duwatsu, da sauran sinadaran kimiyya masu tasiri wajen kare muhallin da muke rayuwa a ciki ta hanyar aiko da wasu sinadaran maganadisu, watau “Magnetic Waves”. Kamar dai yadda bayanai suka gabata ne kan tsarin Turawa wajen binciken Kimiyya: ba yarda da Allah suka yi ba, don haka binciken su bai nuna cewa akwai wani abu a karkashin wadannan sindarai da ke can cikin wannan kasa ba.  Amma kamar yadda muka karanta kuma muka amince, Allah Ya bayar da labari cewa wannan kasa guda bakwai ce, haka ma sama take.  Shin, wannan adadi na cikin nau’ukan gundarin sindaran da ke karkashin wannan kasa ne, ko a kasan wannan duniya suke?  Allah shi ne Masani.


Dan Allah Malam ka daure ka maimaita bayani da ka taba yi kan “Shiga Fasahar Intanet ta hanyar GSM”, don mutane su dada fahimta da kyau.  Daga Kabiru SKB, Rikkos, Jos: 08092399978

- Adv -

Malam Kabiru barka da kokari kuma mun gode da shawara.  Sai dai a yi hakuri, domin kamar yadda muka sha fada ne, bayanai sun yi ta maimaituwa a wannan shafi kan abin da ya shafi Amfani da Fasahar Intanet a Wayar Salula.  Idan muka ce za mu ci gaba da maimaitawa, to karshenta za mu wayi gari bamu da wani abin yi sai shi.  Domin a daidai lokacin da wani ya saba karantawa, a lokacin abin yake bako ga wani.  Magani kawai shi ne a je Mudawwanarmu (Blog), inda muke taskance dukkan kasidun da ke wannan shafi, don samun Karin bayani.  Ga adireshin Mudawwanar: http://fasahar-intanet.blogspot.com.  Ko ka aiko adireshin Imel dinka don in aika maka da kasidar, musamman.  Da fatan ka gamsu.


Assalaamu Alaikum, ya aiki?  Allah Yai mana jagora.  Hakikanin gaskiya mutane da yawa iri na basu gane mene ne ma Kimiyya da Fasaha ba, saboda an koyar dashi ne da wata hanya mai wuyar fahimta.  Wannan yasa duk da mun je an koya mana, amma sai mu kasa fahimtar abin. A takaice dai a karshe bamu gane abin da muka koyo.  Ina ganin da za a dauki irin yadda ka dauko a makarantunmu, da an fitar da jaki daga duma.  A nan nake son nayi tambaya a kan “TSAUNIN MAMUDA TRIANGLE”: wai shin gaskiya ne an kasa gano abin da ke cikinsa?  Muna godiya bisa kokarika a kan wannan shafin.  Daga Khaleel Nasir Kuriwa, Kiru, Kano: 07069191677 (GZG274)

Malam Khaleel Nasir mun gode, Allah saka da alherinsa, amin.  Daman a tabbace yake cewa muddin ana son mutum ya fahimci abu daram-dakam, to fa dole ne a koya masa da harshensa.  Wannan tasa muka gabatar da kasidu kashi hudu kwanakin baya kan muhimmancin farfado da karantar da ilimin kimiyya da fasaha cikin harshen Hausa. Dangane da abin da ya shafi bayani kan Tsibirin Bamuda (ba “Mamuda” ba), akwai kasidu na nan tafe kusa.  Mun gode.


Salam Baban Sadik, yaya za ayi na hada wayar salula ta da na’urata mai kwakwalwa don shiga yanar gizo? – Tijjani, Malikawa Petroleum, Kano: 08036919511

Malam Tijjani barka da warhaka.  In na fahimci tambayarka da kyau, kamar kana son yin amfani da wayar salularka a matsayin makalutun sadarwa kenan, wato Modem.  Duk wayar salular da ake iya shiga Intanet da ita, to, ana iya amfani da ita a matsayin makalutun sadarwa ga kwamfuta, don shiga Intanet din.  Ya danganci irin wayar da kake amfani da ita.  Idan nau’in Nokia ce, dole sai ka sauko da masarrafar Nokia PC Suite, daga gidan yanar sadarwar kamfanin wayar.  Ko kuma ka yi amfani da faifan CD din da wayar ta zo da shi, akwai masarrafar a ciki.

Aikin wannan masarrafa shi ne taimaka wa wayar salula yin mu’amala da kwamfuta cikin sauki, wajen loda bayanai, ko sauko da su, ko kara wa wayar tagomashi (Update), ko amfani da wayar a matsayin makalutun sadarwa don shiga Intanet da dai sauransu.  Idan ka gama loda wa kwamfutarka wannan masarrafa, sai ka budo, ka je inda aka rubuta Connect to the Internet.  Da zarar ka matsa, za a bukaci ka jona wayarka da kwamfutarka ta hanyar wayar shigar da bayanai da ta zo da wayar, wato Data Cable.  Idan ka jona, kwamfutar za ta nemo yanayin sadarwar kamfanin wayarka, wato Network. 

Bayan ta hada alaka a tsakaninta da kamfanin wayar, sai ta hada ka da Intanet kai tsaye.  Dole ne ya zama akwai kudi a cikin wayarka, sannan ya zama ka hada layin wayarka da tsarin Intanet din kamfanin wayar da kake amfani da layinsu, in kuwa ba haka ba, to sadarwa ba ta yiwuwa.  Idan ba wayar Nokia kake amfani da ita ba, sai ka nemi wannan masarrafa daga faifan CD din da wayar ta zo da shi, ko kuma ka je gidan yanar sadarwar wayar, za ka samu kyauta.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.