Sakonnin Masu Karatu (2009) (9)

Sabanin yadda nayi alkawari cikin shekarar da ta gabata cewa a duk mako zan rika buga sakonnin tes ko na Imel da masu karatu ke aikowa, tare da amsa su, hakan bai faru ba saboda shagala irin tawa.  Da fatan za a min hakuri kan abin da ya wuce, kuma zan ci ga da ganin cewa na lazimci wannan dabi’a, don tafi sauki.  A yau zan amsa dukkan sakonnin tes da kuka aiko a baya, sannan kuma a makonni masu zuwa in ci gaba da bin tsarin da nayi alkawari.

Kamar kullum, muna mika godiyarmu ga dukkan masu aiko da sakonnin godiya da gamsuwa, da masu bugo waya don yin hakan su ma; musamman ganin cewa baza mu iya ambaton sunayensu ba, saboda yawa da kuma maimatuwan hakan a lokuta dabam-daban.  Mun gode matuka.

81

Salamun Alaikum Baban Sadik, don Allah ko zan iya saukar da Opera Mini a cikin waya ta nau’in “Sagem My X-7”, don shiga Intanet a saukake?  –  Dalibinka, Abdu Maigyada, Jas: 07031297258.

Malam Abdu Maigyada sannu da kokari, kuma mun gode da wannan sako naka.  Saukar da manhajar “Opera Mini” a wayar salula ba wani abu bane mai wahala.  Sai kaje inda ake shigar da adireshin gidan yanar sadarwa a wayar, ka sanya wannan rariyar likau din: http://mini.opera.com.  Idan shafin ya budo, sai ka zabi zubin (version) manhajar (“Version 4.2”), ka matsa.  Nan take wayarka zata saukar da manhajar a cikinta, sannan ta tambayeka ko kana son a loda maka wannan manhaja ta yadda za ka iya amfani da ita.  Idan ka amsa, sai ta loda maka.  Daga nan sai kaje inda aka ajiye maka ita, don ci gaba da amfani da ita.  A karshe, ka tabbata kana da rajista da kamfanin wayarka, in kuwa ba haka ba, to baza ka iya mu’amala da fasahar Intanet a wayar ba.  Da fatar ka gamsu.


Assalaamu Alaikum, don Allah ka taimaka min wajen samar da hanyar karanta jarida ta hanyar Intanet a waya ta.  Wayar ita ce “TECNO 570”.  –  07084085752

Bayanai kan yadda ake iya mu’amala da fasahar Intanet a wayar salula sun sha maimaituwa a wannan shafi.  Amma a gurguje, kayi rajista da kamfanin wayarka don samun damar iya mu’amala da fasahar Intanet a wayar, sannan ka tabbata akwai ka’idojin WAP da ke taimaka ma wayar salula yin hakan.  Wadannan, a takaice, su ne muhimman hanyoyin.  Idan ana tare damu cikin silsilar da muka faro kan Wayar Salula da dukkan tsare-tsarenta, za a samu cikakken bayani in Allah Ya so.  Da fatan za a amfana da dan abin da ya samu yanzu.  Mun gode.


Assalaamu Alaikum Baban Sadik, ina fatan kana cikin koshin lafiya, Allah sa haka, amin.  Don Allah ina son ka sanar dani game da yadda zanyi saitin fasahar Intanet a waya ta.  Domin duk sadda na tashi don na ziyarci shafin yanar sadarwa, sai a ce dani: “GPRS Not Subscribed”.  Da na tuntubi kamfanin layin wayar, sai su ce: “Cannot Send Setting to this Type of Phone, Please Visit www.mtnonline.com.  Idan na tuntube su, sai suce bazan samu damar tuntuba ko kuma “Subscribe” din “GPRS” ba.  To ko akwai wata hanyar da zan bi ba tare da ita “General Packet Radio Service” ba?  Da fatan za ka amsa min.  –  Mustafa Rabi’u, Kano: 08131904162

Malam Mustafa sannu da kokari.  Lallai ka sha zagaye-zagaye.  Kuma ga shi baka gaya mana nau’in wayar da kake amfani da ita ba.  Domin ba kowace irin waya bace ke karba, tare da iya sarrafa sakonnin da kamfanin waya ke aiko mata.  Abin da wannan ke nufi shi ne, sai an je an sanya maka dukkan ka’idoji da kuma kalmomin da ake bukata, da hannu, wato “manual configuration”.  A ka’ida, kamata yayi ace da zarar kamfanin waya ya aiko sakon tes, wayar ta kalli sakon da ya aiko.  Idan na mai wayar ce, sai ta adana masa, tare da sanar dashi cewa ya samu sako. Idan kuma sako ne irin wanda waya ke iya sarrafa shi nan take, za ta ajiye masa ne. Da zarar ya budo ya karanta, zai ga abin da ake bukatar yayi da sakon.

Idan bai fahimci sakon ba, kuma yayi kokarin rufewa, wayar za ta sanar dashi abin da ya kamata yayi da sakon, ta hanyar tambayarsa. Wannan na yiwuwa ne a galibin wayoyin salula na zamani, kuma na asali.  Akwai wasu wayoyin da ba a tarbiyyantar dasu yin hakan ba tun wajen kera su.  Ire-iren su sune irin wayoyin da ke zuwa daga kasashen Asiya.  Shawarata a nan ita ce, kaje wajen duk wani mai gyarar wayar salula da ka sani, kwararre (zan maimaita: kwararre), don ya maka saitin wayar da hannu.  Allah sa a dace, amin.


- Adv -

Assalaamu Alaikum Baban Sadik, ina amfani da waya nau’in SonyEricsson Z520i, don Allah ina son a taimaka min da yadda zan rika aikawa da sakonni da bude su idan an aiko mani.  –  Ibn Fiqh, Saabiqus-Thabaty, Trikania, Nassarawa, Kaduna: 08131392572

Malam Saabiq barka da war haka, da fatan ana lafiya.  Baka sanar damu ko a halin yanzu kana iya mu’amala da fasahar Intanet a wayarka ba.  In kana iyawa, sai kaje inda ake shigar da adireshi a wayar, ka sanya: http://mobile.yahoo.com/mail/p  Ga masu amfani da wayar salula nau’in “iPhone”, su shigar da: http://mobile.yahoo.com/mail/iPhone  Wannan shi ne adireshin shiga manhajar Imel na kamfanin Yahoo! a wayar salula.  Shafi zai budo inda za ka shigar da suna (username) da kalmomin shiga (password), sannan ka matsa inda aka rubuta “login” ko “enter”, don shiga.  Idan ka shiga, za ka ga sakonninka, sai ka matsa duk wanda kake son karantawa. 

Idan kuma sako kake son aikawa, sai ka dubi sama a shafin, za ka ga alamar “compose”, sai ka matsa.  Shafin allon rubutu zai budo maka, sai ka shigar da adireshin wanda kake son aika masa, ka gangaro kasa don shiga allon rubutun, in ka gama rubutawa kuma, sai ka gangaro kasa har wa yau, ka matsa alamar “Send”, don aikawa.  Idan baka mu’amala da Intanet a wayar, sai ka nemi kamfanin wayarka ya aiko maka da tsarin da zai taimaka maka wajen yin hakan.  Gamsassun bayanai kan wannan tsari na nan tafe a silsilar da muka faro kan wayar salula.  Da fatar ka gamsu.


Assalaamu Alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya.  Bayan haka, wai shin don Allah  me yasa idan kana lilo a Intanet ta wayar salula, baka samun shafin da ka ziyarta gaba dayansa, ba kamar yadda kake samu ba idan a kwamfuta ce, sai dai kawai a dan tsakuro maka wasu bayanai?  –  Ahmad M. Umar, Na’ibawa, Kano: 07068196146

Malam Ahmad barka da war haka.  Ai “kama da wane, ba ta wane”.  Ma’ana, babu yadda za a yi a samu daidai tsakanin shafin kwamfuta da na wayar salula wajen bayyana shafukan gidajen yanar sadarwa a wayar salula. Saboda girman shafukan da ke gidajen yanar sadarwar, baza su yi daidai da girman shafin da ke wayar salula ba.  Abu na farko kenan. Abu na biyu kuma shi ne, a halin yanzu galibin gidajen yanar sadarwa suna kera shafuka na musamman da wayoyin salula ke iya shigansu ba tare da wata matsala ba.  Za ka samu muhimman abin da kake bukata a shafin baki daya.  Gidajen yanar sadarwa na manyan kamfanonin kwamfuta irinsu “Yahoo!”, da “Google” da “MSN” duk suna da irin wannan tsari. 

Don haka idan kana amfani da rariyar lilon da ke wayar ne (wato “Phone Brower”), wacce wayar ta zo dashi, to kana iya samun shafuka wadanda suka dace da yanayin wayarka.  Da zarar ka shiga shafin, sai a loda maka wadannan shafukan na musamman da suka dace da wayar. Amma idan kana amfani ne da “Opera Mini”, misali, kana iya zuwa wajen “Settings”, ka tsara masarrafar ta yadda shafukan da ka shiga zasu rika budowa daidai da yanayin wayarka.  Da fatan ka gamsu.


Assalaamu Alaikum, don Allah me yasa wayoyin salula na kasar Sin (China) basu iya shiga Intanet?  –  Sa’idu Danjuma, Kawo, Kaduna: 08096420965

Malam Danjuma, ban taba amfani da wayoyin salula na kasar Sin ba, amma nakan ji jama’a na korafi kansu sosai.  Tabbas na gansu, na kuma shiga cikinsu don ganin yanayi da tsarinsu a fasahance.  Suna da nakasu sosai ta bangaren sadarwa da mu’amala da wata waya ‘yar uwanta.  Don haka, matsalar rashin iya mu’amala da fasahar Intanet a wayoyin Sin na komawa ne zuwa ga dayan dalilai biyu: na farko, ko dai ya zama saboda yanayin kiransu ne – ma’ana basu da ingancin da zasu iya taimakawa wajen yin hakan ta dadi. Na biyu kuma yana iya zama saboda rashin samun sinadaran da zasu taimaka mata don yin haka daga mai wajen mai ita ne. Misali, dole ne a samu tsarin da ke taimaka wa waya daga kamfanin waya, wato “Configuration Settings” kenan, kuma ya zama wayar tana da ka’idar mu’amala da Intanet, wato “Wireless Application Protocol”, ko “WAP” a gajarce.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.