Sakonnin Masu Karatu (2010) (3)

Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.

91

Baban sadiq, don Allah yaya zan yi in canza “password” din jakar Imail dina? Rabiu Isa Ayagi

Malam Rabi’u a min afuwa, kuma da fatan an yi salla lafiya.  Canza kalmomin shiga (wato Password) na jakar wasikun Imel ba shi da wahala ko kadan.  Idan ka budo zauren Imel dinka, wato “Email Home”, ko kuma da zarar ka shiga zauren Imel dinka, ka daga kanka sama zuwa bangaren hagu ko tsakiya, za ka ga inda aka rubuta “My Account”, sai ka shiga wurin.  Da zarar ka shiga za ka inda aka rubuta “Change Password”, sai ka matsa kawai.  Za su bukaci ka sake shiga da sunan da ka shiga da shi da farko, da kuma kalmomin da ka ke amfani da su, wadanda kake son canzawa.  Da zarar ka sake shiga, sai a kaika inda za ka bayar da tsohon “Password”, sannan da sabon da kake bukata.  Allah sa a dace, amin.


Assalam alaiKum, Abba na kayi mini bayani kan tsarin karatu a jami’o’in tsallaken kasar nan ta yanar gizo. Yan’uwa kuma barka da SALLAH.  Daga Sadiq Tukur Gwarzo

Malam Sadiq barka da war haka, kuma da fatan kana lafiya.  Tsarin karatu ta yanar gizo ko “Online Distance Learning” ana gudanar da shi ne ta hanyar Imel; za ka je shafin makarantar, ka yi rajista ko ka cika fam, ka kuma loda dukkan takardun karatunka na baya, sannan ka aika musu.  Idan lokaci ya yi za su aiko maka sako muddin ka yi nasara, sannan da kimar kudin da za ka biya, da kuma yanayi ko tsarin da ake bi wajen daukan darasi, da kuma rubuta jarabawa.  Idan ka gama karatun kuma, nan take za su aiko maka da takardar shedar gama karatu.  Wannan tsari ne da hatta a nan Afirka akwai kasashen da jami’o’insu ke yi.

Misali, Jami’ar Afirka ta Kudu, wato University of South Africa, tana gudanar da wannan tsari na karatu.  A karshe, muddin za ka yi karatu ta wannan tsari, to fa dole ne ka tanadi kwamfuta, ko ka tabbata kana da inda za ka rika zuwa kana samun damar mu’amala da fasahar Intanet, domin kusan komai ta Intanet ake gudanar da shi.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum. Baban Sadik yaya aiki? Ina yi maka fatan alheri. Ina da Imail yanzu, yaya zan yi rijista ta “Google Mail”. Allah ya saka maka da alheri.  Musa Y Muhammad.

Malam Musa yin rajistar wasikar Imel ta kamfanin Google bas hi da wahala ko kadan.  Idan akwai kwamfuta da ke jone da fasahar Intanet, ka je http://mail.google.com, da zarar shafin ya budo, a kasan shafin daga hannun dama za ka ga inda aka rubuta “Sign Up for Gmail”, sai ka matsa.  Nan take za a budo maka fam da ake son ka cika.  Da zarar ka gama cikewa sai ka aika musu.  Magana ta kare.  Idan kuma a wayar salula kake nufi, to ya danganci wayar da kake amfani da ita.  Idan Blackberry ce, ko wata babbar waya da ke da tsari irin nata (misali Nokia E63, E52, E73), to duk kana iya kwatantawa kamar yadda na sanar da kai.  Amma idan ba wata babbar waya bace, to dole ne sai kaje kan kwamfuta mai zaman kanta.  Da fatan ka gamsu.


Salaam Baban Sadiq, ya aka ji da mu? Na iya shiga BBC Hausa, amma na kasa samun facebook.

Ka shiga ta wannan adireshin: http://mobile.facebook.com, ko kuma ta wannan adireshi: http://www.facebook.com/mobile.  Allah sa a dace, amin.


- Adv -

Assalamu alaikum Baban Sadik, taimako nake so game da sakon Imail da kuma facebook ta wayar salula.  Ko sai ta kwamfuta? Ka huta lafiya.  Ni ne Alh Dan Azumi 2ic, Fatakwal.

Alhaji Dan azumi ai ba sai lalai ta kwamfuta ba kadai, ko ta wayar salula ma kana iya mu’amala da fasahar Intanet.  Abin da ya kamata ka yi shi ne, ka nemi waya wacce ke iya mu’amala da fasahar Intanet, sannan ka samu wanda ya kware wajen hakan don ya nuna maka. Domin hakan zai fi muhimmanci.  Allah sa a dace, amin.


Assalamu alaikum Baban Sadik, ina son a yi mini cikakken bayani game da Google.  Daga Bashiru Umar Achida Iddo: 08036295411

Malam Basharu, Kalmar “Google” suna ne na kamfanin masarrafa da harkokin sadarwa a Intanet, kuma ofishin kamfani na kasar Amurka ne.  A fayyace, gidan yanar sadarwa ne da ke http://www.google.com da ke dauke da manhajar wasikar Imel, da manhajar Manemar Bayanai, wato “Search Engine”, da sauran manhajoji ko masarrafan kwamfuta masu kayatarwa da ilmantarwa.  In kana neman Karin bayani, sai ka je shafin da ke bayani kan kamfanin baki daya, a http://www.google.com/about. Da fatan ka  gamsu.


Salam Abban sadik, ina da waya (Tecno system WAP2.0, GPRS class 12 H/W, N5, China) zan iya komai da ita kamar BlackBerry ta Kanada, ma’ana mu’amala da intanet kamar a kwamfuta?  Zan so samun amsa ta wayata. Daga masoyinka Aliyu A. Lawan HMB (I D H) Kano.

Malam Aliyu, wayoyin kasar Sin, wato China Phones, suna da matsala guda daya wajen ta’ammali da fasahar Intanet.  Ba kowacce bane ke iya sarrafa sakon “Settings” da kamfanin waya zai turo mata ba. Bayan haka, galibinsu kan zo ne da tsare-tsare (wato Settings) na musamman daga wasu kamfanonin waya da ke can kasar.  Wannan ke nuna cewa dole sai sanya wadannan tsare-tsare da hannu, wato “Manual Configuration” kenan.  Hakan kuma, a daya bangaren, ya danganci kwarewa da sanayyar mai sanya tsare-tsaren ne.  In kuwa haka ne, to zan bayar da shawarar cewa a je wajen masu gyaran waya ko masana harkar tsare-tsaren waya.  Za su iya taimakawa gaya wajen nemo masalaha dangane da haka.  Da fatan an gamsu.


Assalamu Alaikum Baban Sadiq. Da fatan kana cikin koshin lafiya tare da abokan aiki, Allah Yasa haka, amin. Baban Sadiq mene ne “Data Card”, kuma ko akwai bambamci da ke tsakaninsa da “SIM Card” ne – ganin cewa dukkansu biyu ana kira ko amsa kira, sannan kuma ana iya lilo a yanar giza-gizai (Browsing) a wayar salula da su. Wassalam Daga Uncle Bash, Jimeta-Yola. bysalihu@gmail.com

A gaida Uncle Bash namu.  Lallai akwai bambanci nesa ba kusa ba tsakanin wadannan nau’ukan kati guda biyu, wato “Data card” da kuma “SIM Card”. Da farko dai, shi “Data Card” nau’i biyu ne; akwai wanda ake amfani da shi, kamar yadda kace, wajen yin lilo da tsallake-tsallake a shafin Intanet.  Wannan shi ne kamfanonin waya ke bayarwa don samun damar mu’amala da Intanet a kwamfutocin tafi-da-gidanka.  Na biyun kuma shi ne wanda ake iya taskance bayanai kadai a ciki, sannan a shigar wa kwamfutar tafi-da-gidanka, wato Laptop.  Wannan na biyun a matsayin katin ma’adanar bayanai na wayar salula yake, wato “Memory Card”.  Sai dai shi ya kebanta ne da kwamfutar tafi-da-gidanka kadai.  Domin suna da ‘yar kafar da aka kebance musu, inda ake tsofa wannan kati, don lodawa ko saukar da bayanan da ke cikinsa baki daya.

A daya bangaren kuma, shi “SIM Card”, ko “Subscriber Identification Module”, kati ne da ke dauke da ma’adana (wato Memory ko Storage) nau’uka biyu biyu zuwa uku.  Akwai inda ake taskance lambar katin, sai inda ake taskance lambobin mai katin, da kuma inda ake taskance kalmomin sirri (PUK ko Pin Cord ko Security Cord) da mai katin yake sanyawa don bude wayar da su.  Kowane katin SIM na yade ne da sinadarin tagulla da ke taimakawa wajen tabbatar da mu’amala tsakanin siginar sadarwar kamfanin waya, da kuma wayar salular da ke dauke da katin.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.