Sakonnin Masu Karatu (2010) (4)

Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.

58

Assalamu alaikum Baban Sadiq, bayan gaisuwa da jinjina, nake so in yi amfani da wannan damar domin rokonka a kan ka fadada wannan baiwar da Allah yayi mana da kai, ka rika buga bayanai muhimmai, su zama littattai domin na baya. Daga Comrade Abdul Dantata, Waratallawa, Kano.

Dubun gaisuwa da fatan alheri ga Comrade.  Wannan shawara ce mai kyau, kuma in Allah Ya so zan duba yiwuwar hakan ko da ba yanzu ba.  Domin muddin zan yi hakan, dole sai na hada da kwararru ko masana a fannin, wadanda za su yi bita na kwarai kan abin da za a yada.  Allah sa mu dace baki daya, amin.


Baban Sadiƙ barka da aiki, da fatan Allah ya baka fasaha da zalaƙa wajen ilmantar da jama’a game da kimiya da kere-kere, kan da abubuwan da suka shafi zamani, amin.  Allah bamu alheri. Daga Nasiru Sani GS

Malam Nasiru na gode da tarin addu’a, Allah karba, ya kuma albarkace mu baki daya, amin.


Baban sadik barka da aiki da fatan duk iyali lafiya, Allah ya kara ilimi.  Na karanta shafin Kimiyya da Kere-kere na wannan makon, don ina da tambayoyi, ina fatan Allah ya baka ikon amsawa.  Ga su kamar haka: na farko shin Architect Thomas Andrews dan wata kasa ne? Kuma yanzu wannan jirgin shi ne babba a duniya ko da wani?

Architect Thomas Andres dan kasar Ingila ne ko Ireland.  Shi dai jirgin Titanic shi ne mafi girma a shekarar da aka kera shi.  Amma a halin yanzu akwai jiragen ruwa manya da aka kera wadanda suka fi shi girma nesa ba kusa ba; sun kai wajen talatin.  Da fatan ka gamsu.


- Adv -

Assalamu alaikum Baban Sadik, Allah ya kara fasaha amin. Ka yi bayanin an shirya fim din “Titanic” a 1997, to shin abin da aka nuna a fim din shi ya faru a wancan Jirgin na asali (ko tarihi ne)?. Daga Aminu Shehu, Kano: 08036236878.

Malam Aminu wannan fim din daga baya ne aka shirya shi, bayan shekaru kusan tamanin da biyar da faruwar wancan lamarin.  Na kawo bayanin fim din ne don misali da kuma hada alaka a tsakaninsu.  Amma asalin jirgin yana karkashin tekun Atilantika a halin yanzu, kamar yadda bayanai suka gabata a shafin.  Da fatan ka gamsu.


Salam Baban Sadiq, barka da aiki. Tambayata a nan ita ce, kamar manyan jiragen ruwa ana kera su ne a cikin ruwa, ko kuma sai an gama a sa su a ciki? Na gode, Allah karo basira. Daga Dahiru One One, Kubwa Abuja

Malam Dahiru sai bayan an kera su ake sanya su a cikin ruwa.  Galibi kamfanonin kera jiragen ruwa musamman manya suna gina masana’antarsu ne a bakin teku, ko kusa da inda tekun yake.  Wannan ke sawwake jigilar daukowa da sanyawa cikin ruwa.  Da fatan ka gamsu.


Meye bambancin “Computer Literacy” da “Computer Science”?  Khaleel Nasir Kuriwa Kiru 07069191677

Malam Khaleel, bambancinsu a fili yake.  Shi “Computer Literacy” shi ne tsarin iya mu’amala da kwamfuta a aikace, shin, zuwa ka yi ka koyo, ko kuma da rana tsaka ka kama kwankwasata; muddin ka iya mu’amala da kwamfuta a aikace, to a iya cewa “You are computer literate”, a misali.  A daya bangaren kuma, “Computer Science” fanni ne mai fadi da ke lura da dukkan wani ilimi da ya shafi rayuwar kwamfuta baki daya; daga tarihin samuwarta, zuwa ci gaban kere-kere da aka samu a bangaren kwamfuta, zuwa yadda ake taskance bayanai da hanyoyin yin hakan, har aka kai yadda ake tsara manhajoji ko masarrafan da kwamfutar ke amfani da su, duk wadannan suna karkashin wannan fanni ne.  Kai a takaice ma dai, hatta shi kanshi fannin “Computer Literary” yana karkashin wannan fanni ne.  Don haka fannin “Computer Science” ya fi fadin ma’ana fiye da “Computer Literacy”, duk da cewa asalinsu daya ne.  Da fatan ka gamsu, kuma a mika gaisuwata ga Anti.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.