Sakonnin Masu Karatu (2010) (6)

Ga wasu daga cikin sakonninku kamar yadda aka saba. A sha karatu lafiya.

57

Neman Afuwa

Mun samu wasiku ta hanyar Wasikar Hanyar Sadarwa ta Intanet, watau Imel, masu dimbin yawa.  Da dama cikinsu duk na bayar da jawabinsu, musamman wadanda ke bukatar amsoshi na musamman da suka kebanci tambayoyin da aka aiko.  Akwai kuma wadanda ke bukatar bincike mai dan zurfi da bazan iya amsa su nan take ba, na jinkirta sai wani lokaci.  Ga kadan cikin wadanda aka rubuto masu nasaba da yanayin shafinmu wajen rashin tsawo.  Ina kuma sanar da Malam Abbass Ameen da ya taimaka ya aiko da jadawalin da ya taba aiko min watannin baya, mai dauke da kalmomi da yake neman a fassara masa su.  A wancan lokacin na shagaltu da aiki ne, kuma wasikar na bukatar daukan lokaci don tantance kalmomin tare da ware musu ma’anonin da suka cancance su a harshen Hausa.  Na duba wannan wasika sama ko kasa a cikin Jakar Wasikar Imel dinmu, amma na kasa gani.  A gafarce ni a sake aikowa.

Haka ma ina sanar da Malam Aliyu Mukhtar Sa’idu (IT) da ke Kano, cewa sakonnin tes masu dauke da tambayoyin da ya aiko mani cikin watan da ya gabata, sun salwance a lokacin da na bayar da wayar salula ta aka farfado da ita (flashing) sanadiyyar kwayoyin cuta (virus) da suka kama ta.  Kamar yadda aka sani ne, da zarar an sumar da waya aka sake farfado da ita, to duk bayanan da ke ciki an rasa su kenan.  Don haka dukkan sakonnin da ya aiko, da wasu ma da bazan iya tuna wadanda suka aiko su ba, duk sun salwance.  A yi hakuri a sake aiko min su.  A halin yanzu ga wadannan sakonni nan.


Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Na hadu da kasidun da kake rubutawa ne a Internet, hakan ya sa ni in bayyana ma gamsuwa na. A gaskiya na fa’idantu da wannan kokari naka. Kuma Allah ya taimakeku. Sai an jima. —  Isma’il Adam, Jumhoriyar Nijer: samaila_ada@yahoo.com

Malam Ismaila mun gode da wannan wasika taka kuma Allah saka da alheri, ya kuma bar zumunci.  Kai ne mutum na uku da ya taba rubuto mana wasika daga wajen Nijeriya.  Don haka mun gode.  Kuma kamar yadda na sanar da kai kwanakin baya, da fatan zaka ci gaba da ziyartar wanann shafi namu da ke Intanet don samun kasidun da ake fitarwa a duk mako. 


- Adv -

Assalaamu Alaikum, bayan gaisuwa ta addinin Musulunci, Malam ya aiki ya kokarin ilmantar da al’umma? Bayan haka Malam ina da tambayoyi kamar haka: ina kokarin gina mudawwana ce tawa, amma da Blogger. A yanzu ina son in fara tura sakonni cikin mudawwanar ta hanyar amfani da WordPad, to Malam ya zan yi in tura rubuntun cikin mudawwana? Saboda ba na son in bi ta hanyar Blogger wajen tura sakonnin, don ina son in yi amfani da hanyoyin Web Designne, ta amafani da  “vertical table” da “radio button”. Kuma ance (za a iya amfani da) WordPad ko kuma Notepad, to shine na ke son Malam ya gaya min yadda zan yi wajen tura sakonnin.  Sai kuma idan ina son in sanya adireshin wani gidan yanar sadarwa a ciki shi ma yaya zan yi?  A huta lafiya.  —  Aliyu Abdullahi, Kano: malakhum@yahoo.com

Malam Aliyu na samu sakonka, kuma ina neman a min afuwa saboda tsawon lokacin da na dauka ba tare da na aiko maka da jawabin da kake nema ba.  Na karanta sakonka kuma na fahimci wasu cikin tambayoyin, kamar yadda zaka gani, ba dukkan wasikar na kalato mana ba.  Na yago iya inda na fahimta ne, kuma a kan haka zan baka amsa.  Da farko dai kamar yadda ka sani, manhajar gina Mudawwanai na Blogger na dauke ne da dukkan hanyoyin da ake bi wajen zuba bayanai da gyatta su, da kuma canza musu launuka ko launin da ake so, da kuma hanyar tsara alamomi a Mudawwanar a gefen da ya dace da dai sauransu.  Yin amfani da masarrafar “Wordpad” ko “Notepad” bai dace ba saboda dalilai biyu: na farko dai shine, Manhajar Blogger bata bayar da damar shigar da bayanai ta amfani da wadannan masarrafai; domin ko ka tsara bayanai a cikinsu ka kuma gyatta su, da zarar ka debo su zuwa Blogger, tsarin da kayi zai watse gaba daya. 

Na biyu kuma shine, yin amfani dasu bata lokaci ne.  Sai idan kana nufin zaka killace wata kwamfuta ce mai zaman kanta, a gidanka ko ofishinka, ya zama kayi amfani da Blogger ne kadai don samun adireshi, to kana iya tsara shafuka ta hanyar amfani da wadannan masarrafai, ka loda su cikin kwamfutar, ta yadda duk wanda ya shiga shafin, zai ci karo da bayanan da suke dauke dasu.  Kamar dai gidan yanar sadarwa kenan ka bude. Amma in har a Blogger zaka ajiye shafinka, to ban ga dalilin da zai sa ka yi amfani dasu ba.  Ina dada nanata mana, amfaninsu wajen gina gidan yanar sadarwa ne kadai, ko gyara bayanan da ke gidan yanar sadarwa da sake loda su.  Amma basu da alaka da abinda ya shafi amfani dasu wajen shigar da bayanai a Blogger.  Amma idan wanda ya sanar da kai na da wata sabuwar hanya ko fasahar yin hakan a aikace, to ka iya sanar damu don mu karu.

Kawai idan kana da bayanan da kake son dorawa ko shigarwa a cikin Mudawwanar, ka kwafe su (copy), ka zuba (paste) a cikin allon Mudawwanar.  A inda ka zuba bayanan, kana iya gyatta su.  Idan so kake ka sanya musu launi, a nan zaka zaba.  Idan so kake ka mayar dasu ta bangaren hagu, akwai inda zaka yi.  Idan a tsakiyar shafin kake son ajiye su, duk akwai inda zaka zaba.  Maganar amfani da masarrafar “Notepad”  ko “Wordpad” ma duk bai taso ba, sam ko kadan.  Duk abinda ka zuba cikin mudawwana, a nan zaka gyatta musu zama ta kowane yanayi ko hali kake so.

A karshe, masarrafan “Wordpad” da “Notepad” ana amfani dasu ne kawai idan kana gina gidan yanar sadarwa na musamman, kamar yadda bayani ya gabata.  A ciki zaka shigar da bayanan, ka yi amfani da ka’idojin gyatta su, kamar yanayin launi, ko bigiren da kake son gyatta su da dai sauran hanyoyi.  Hakan kuma na samuwa ne ta amfani da fasahar Hypertext Markup Language (HTML tags), wadda muka asha ambato a lokutan baya.  Amma a manhajar Blogger duk baka bukatar haka.  Domin manhajar na dauke ne da wannan fasaha ta HTML tags; zuba bayananka kawai zaka yi, manhajar za ta gyatta maka su.  Sannan idan kana son sanya adireshin wasu gidajen yanar sadarwa a shafin Mudawwanarka, duk babu wahala.  Idan ka je “Settings”, sai ka karasa “Layout”, a can zaka kirkiri inda zaka sanya adireshin, tare da lakabin gidan yanar, da adireshinsa gaba daya.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.