Sakonnin Masu Karatu (2010) (7)

Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.

86

Salam Baban Sadik ina maka fatan alkairi a cikin wannan dare.  Nine El-bashir daga kano, kuma ni ma’abocin wannan makaranta ce tun lokacin kafa ta kusan shekaru biyu kenan, ban taba turo maka sako bane.  Ina so dan Allah ka turo min bayanin da kayi a kan “‘Yan Dandatsa”, saboda ina so in yi amfani da bayanan da kayi ne don fitar da wasu bayanai.   Wassalam, ka huta lafiya.  – El-basheer, Kano: ashareef@yuurok.com

Malam El-Bashir mun gode da wannan wasika taka, kuma Allah saka da alheri.  Kuma na tura maka dukkan bayanai ko kasidun da muka rubuta ko fitar kan “’Yan Dandatsa” a wannan shafi.  Da fatan  ka same su.  Idan akwai abinda baka fahimta ba, ko kana iya neman karin bayani kan wani bangare na musamman da bamu tabo a cikin kasidun ba, kana iya sanar dani sai in tanada maka.  Saboda gaba, duk kasidun da kake nema idan kaje Mudawwanar wannan shafi da ke http://fasahar-intanet.blogspot.com  ko http://kimiyyah.blogspot.com, zaka same su in Allah Ya yarda.  Allah sa mu dace, kuma mun gode.


Assalamu alaikum, da fatan Baban Sadik ya wuni lafiya. Bayan haka, gidan rediyon Sashen Hausa na BBC suna ta sanarwa cewa za’a iya sauraronsu ta hanyar Intanet ta amfani da wayar hannu, amma na shiga na rasa yadda zan saurare su.  Yaya abin yake ne Malam? Daga dalibinka Danlami Muhammad Doya, Bauchi: danlamindoya@gmail.com

Malam Danlami sannu da kokari kuma da fatan kana cikin koshin lafiya. Watau abinda ke faruwa shine, sauraron labaru ta hanyar wayar salula  ya danganci tsari da kuma nau’in wayar salular, ba kowace iri ake iya yin hakan da ita ba.  Da farko dai kamar yadda muka sani, dole ne ya zama wayar na da ka’idar mu’amala da fasahar Intanet, watau “WAP”.  Na biyu kuma ya zama akwai kudi a cikin katin wayarka, ba wai da holoko ake yin lilo ba.  Domin da zarar ka shiga Intanet ta wayar, to nan take kamfanin wayarka zai fara zaftare kudin da ke ciki; iya gwargwadon yawan kalmomi ko haruffa ko kuma bayanan da wayar ke nuna maka.  Kuma kasancewar tsarin “sauti” ko “hoto mai motsi” ko “daskararre”  da wayar zata budo maka daga Intanet yafi cin kudi fiye da tsantsar bayanai na labaru da zaka karanta, ta sa dole ka zuba kudi mai yawa a wayar kafin ka fara sauraro.  Abu na uku kuma shine ya zama wayar tana da masarrafan da ke taimakawa wajen budo maka jakunkunan bayanan sauti da ke dauke da labarun da kake son sauraro. 

Ba kowace wayar salula mai iya shiga Intanet ne ke da ire-iren wadannan masarrafa na kwamfuta ba.  Shahararrun cikinsu dai sune: “Real Player” da kuma “Windows Media Player”.  Idan wayar salularka bata da wadannan masarrafai, to baza ka iya sauraron labaru ba, ko da kuwa ka shiga gidan yanar sadarwar BBC. Abu na karshe kuma shine ya zama kayi rajistar layin wayarka da kamfanin wayarka, don baka damar mu’amala da fasahar Intanet a wayar.  Wasu kamfanonin wayar (irinsu “Etisalat’ da “MTN” – a layukansu masu 0803) nan take suke maka rajista da zarar ka sanya Katin SIM dinka a wayar da ke da ka’idar mu’amala da Intanet.  Zaka ji nan take an turo maka sakon tes don sanar da kai hakan.  Amma wasu kamfanonin wayar kuma sai ka aika musu da sakon tes na bukatar yin hakan sannan zasu turo maka.

Idan kuma aka dace kana da dukkan wadannan, to sai ka zarce gidan yanar a www.bbc.co.uk/hausa.  Da zarar ka shigo, sai ka zarce bangaren dama, inda aka rubuta “Saurari Shirye-shiryenmu”, a kasa zaka ga nau’ukan shirye-shiryen; da na safe, da na hantsi, da na rana da kuma na yamma.  Sai ka matsa wanda kake son sauraro.  Shafi zai budo, dauke da wadannan masarrafan jin sauti da bayaninsu ya gabata, watau “Real Player” da kuma “Windows Media Player”.  Idan ka zabi wanda kake son amfani dashi wajen sauraro ko kuma wanda wayarka ke dauke dashi, sai ka gangara kasa daga hannun dama inda aka rubuta “Ok”, ka matsa.  Da zarar ka matsa sai kawai ka kishingida ka fara sauraron labaru radau-radau; kai kace a tafin hannunka gidan rediyon BBC da ke Landan yake. 

Kada a mance Malam Danlami, a zuba kudi da yawa cikin wayar, idan kuwa ba haka ba, kana cikin sauraron zaka ji shiru.  Ba sadarwar wayar salula bace balle na’urar tace maka “kudinka ya kare”.  Sai dai kawai kaji shiru!  Da fatan ka gamsu.


- Adv -

Assalaamu Alaikum, na karanta shafinka na “Kimiyya da Kere-kere” a cikin jaridar AMINIYA.  Allah Ya kara hazaka.  Don Allah a taimaka mani da wasu bayanai masu alaka.  Ga adireshin Imel dina: yunusayunusa43@yahoo.com.  Daga Yunusa Hussaini, Samaru, Zaria.

Malam Yunusa mun gode da addu’a.  Kai ma Allah kara maka hazaka da juriyar kasancewa tare damu.  Dangane da bukatarka, na rasa me zan aika maka, musamman ganin cewa dukkan abin da nake rubutawa a wannan fanni ne ake bugawa a shafin.  Sai dai idan kana da bukatar kasidun da suka gabata a baya ko shekarun baya, kana iya zuwa shafin Makarantar Kimiyya da Fasahar Sadarwa da ke http://fasahar-intanet.blogspot.com, ko wanda muka kebe don zuba kasidun Kimiyya da Fasahar Kere-kere, da ke http://kimiyyah.blogspot.com.  Duk kasidun da da ke bayyana a wannan shafi suna can a taskance.  Da fatan ka gamsu.


Assalaamu Alaikum, Malam Abdullahi yaya kokari?  Tambayata ita ce:  in har Malaman Kimiyya da Fasaha a wajensu komai ya faru, akwai abin da ya haddasa shi, ba Allah ba, to wai me za su ce, ko me suka ce dangane da masu tsafi, wanda ke hada wani abu sai wani abu ya tashi; ba kuma a kimiyyance suke yi ba?  Daga Khaleel Nasir Kuriwa, Kiru, Kano: 07069191677

Malam Khaleel barka da kokari.  Hakika har yanzu dai basu yarda da ire-iren wadannan abubuwa ba, kuma ba su kididdige su a matsayin wata ci gaba ta ilimi a fannin Kimiyya.  Kamar yadda kai ma ka kira su da “matsafa”, haka su ma suke kiransu.  A turance sukan kira su “magicians”.  Su malaman kimiyya suna da wasu ka’idoji ne da suke bi wajen bincike, masu basu irin sakamakon da suke bukata dangane da kowane irin yanayi.  A tsarinsu, duk wani bincike da bai da asali daga wadannan ka’idojin, to ba su bashi wata kima.  Da fatan ka gamsu.


Salamun Alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: yaya tsarin amfani da Intanet na tafi-da-gidanka (wato Datacard Internet ko “F@stlink”) da kamfanonin wayar salula na kasar nan ke bayarwa? Kuma kasashen ketare ma suna da irin wannan tsarin?  –  Aliyu Mukhtar Sa’idu (IT), Kano: 08034332200

Malam Aliyu, wannan tsari na “F@stlink” kamar yadda kamfanin MTN ke kiransa, ba wani tsari bane sabo.  Hasali ma dai an dade ana amfani da shi a wasu kasashe kafin zuwansa nan kasar.  Tsari ne da ya kunshi amfani da fasahar Intanet a kwamfutar tafi-da-gidanka, wato Laptop, ta hanyar amfani da Makalutun Sadarwa, wato “Internet Modem”.  Idan ba a mance ba, bayanai sun gabata cewa kwamfuta na iya mu’amala da fasahar Intanet ko Giza-gizan sadarwa ne ta hanyar wannan makalutun sadarwa, wacce ke zakulo bayanan da ke Intanet a matsayin siginar lantarki, ta kuma juya su zuwa haruffa ko hotuna ko sauti, kamar dai yadda suke a uwar garken da ta zakulo su. 

Wannan tsari na zakulo bayanai a siffarsu, a mayar da su zuwa siginar lantarki, sannan idan sun zo muhallin da ake son amfani da su su bayyana kamar yadda aka dauko su, shi ake kira “Modulation and Demodulation”, wanda kuma daga wadannan sunaye biyu ne aka samo sunan wannan makalutu da ake kira “Modem” a turancin Kimiyyar sadarwa ta zamani.  To wannan makalutu kuwa asalinsa babba ne, kamar dai irin wayoyin tarho da muke amfani dasu a da.  Idan ka saya za ka jona shi ne da kwamfutarka, ta wayar da yazo da ita.  To amma da zamani ya ci gaba, sai aka mayar da su kanana, sirara, wasu ma girmansu bai wuce dan yatsan hannu,  wasu kuma kamar tafin hannu suke.  Ya dai danganci kamfanin da ya kera su. Da zarar ka saya, sai ka tsofa shi a jikin kwamfutar tafi-da-gidanka, ka kuma loda mata masarrafar da take zuwa da shi a faifan CD ko makamancin wannan, don ta haddace dukkan tsare-tsaren da ke ciki. 

Har wa yau, wannan tsari na amfani ne da lambar wayar tarho da ke dauke cikin katin SIM da kamfanin wayar ke bayarwa.  Idan ka tashi shiga Intanet, sai ka sayi katin kira (wato “Recharge Card”) ka loda mata, sannan ka fara tsallake-tsallakenka.  Kamar yadda bayanai suka gabata a sama, sauran kasashe ma na amfani da wannan tsari, kusan shahararsa a wasu kasashen ma yafi na nan Nijeriya.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.