Sakonnin Masu Karatu (2011) (18)

Ci gaban sakonnin da na fara amsa makon jiya.  A sha karatu lafiya.

53

Assalamu alaikum, ka yi bayani dalla-dalla kan makalarka ta na’urar ATM, amma ban ga ka ambaci na’urar daukar hoto ba, ko babu ita?  Allah ya kara maka basira da lafiya. Alh. Ado Damaturu

Alhaji Ado mun gode da wannan tsokaci naka. Hakika akwai na’urar daukar hoto (Camera) a jikin wannan mashin.  Mancewa na yi ban ambace ta ba.  mun gode.  Allah sa mu dace.


Baban Sadiq, ina gaisheka da kokari. In na fahimceka, shi kamfanin Interswitch ke da ma’aikatan da ke rarraba kudaden ga bankunan da abin ya shafa kenan kullum in gari ya waye? Kuma ladansu shi ne Naira 100 nan? Bashir Ibrahim, Port Harcourt

Malam Ibrahim wannan wani abu ne da ba zan iya ce maka eh ko a a ba. Sai dai ta la’akari da yadda ake gudanar da wannan abu a kullum; dare da rana safe da yamma, zai yi wahala ace ma’aikaci ake turawa a duk safiya ya biya bankuna.  Abin da ke faruwa shi ne, akwai cibiya ta musamman wacce ke tantance adadin kudaden da kowane bangare ke samu, da kuma hanyar da ake bi wajen biya.  Wannan shi ake kira Electronic Clearing System.  Da fatan ka gamsu.


Salam, zanso baban sadik yayima ‘yan uwa yadda ake yin “money tranfer ta hanyar na’urar ATM zuwa wani bankin. Daga Baban Mus’ab, Kaduna

An gaida Baban Mus’ab. Aiwayatar da wannan tsari na “Money Transfer” bai da wata wahala ko kadan.  Idan ka je inda na’urar take, ka sa katinka, sai ka shigar da kalmomin sirrinka (watau “Password”), za a budo maka inda za ka zabi “Funds Transfer.”  Sai ka matsa, ka zarce inda za ka shigar da lambar asusun wanda kake son aika masa, da bankin da yake ajiya, da kuma adadin kudaden da kake son aika masa.  Wadannan su ne abubuwan da ake bukata. Tsarin bai da wahala ko kadan.  Abin da za ka kiyaye kawai shi ne, wajen shigar da lambar asusun wanda kake son aika masa, ka tabbata ka shigar daidai, don kada a jefa kudaden zuwa asusun wani.  Idan haka ta faru kuwa, kafin a mayar maka da kudadenka zai dan dauki lokaci.  Don sai sun yi amfani da kundin adana bayanan da na’urar ke taskancewa, don tababtar da da’awarka.  Sai a kiyaye.


Salam, Baban Sadiq muna matukar farin ciki da rubutunka. Munji dadin bayanin yadda ake mu’amala da katin ATM, wanda daman mafi yawanmu mata bamu fahimce shi sosai ba. Allah ya yawaita mana irinka a cikin al’umma musulma, amin. Daga Maman Abdulsamad Gombe.

Allah saka da alheri da wannan jinjina mara iyaka.  Bai kamata albarka da rahamar da ke cikin wannan addu’a su shafe ni ni kadai ba.  Ina rokon Allah ya sadar da su ga dukkan masu karatu, da masu lura da wannan shafi a ofishin AMINIYA,  da editan jaridar baki daya, kai, da ma kamfanin Media Trust baki daya.  Allah tara mu cikin alheri, ya sa mu cikin sahun masu ciyar da al’umma gaba baki daya, amin. Mun gode.


- Adv -

Salam, barka da kokari Baban Sadik. Dan gyara ne akan makalar da ka yi a Aminiya ta 23 ga watan Satumba, inda kace “Marigayi Mudi Sipikin.”  Yana nan da ransa. A huta lafiya.  Bashir Gwale, Kano

To, malam Bashir na gode. Kafin wannan sako naka ma akwai wadanda suka bugo waya suka mini gyara kan haka.  Gaskiya ba gani nayi a rubuce ba, illa dai na dade ban ji duriyarsa ba tsawon shekaru, sai na dauka ya rasu.  Don ina da mantuwa sosai; akwai wadanda Allah ya musu rasuwa, amma saboda tsawon zamani sai in dauka suna raye.  Wannan nakasa ce daga gare ni.  Allah sa mu cika da imani.  Na gode.


Shin, me ke haifar da rikicewar sauti idan aka yi amfani da wayar salula a kusa da rediyo ko talabijin? Daga Ashiru Dan’azumi Gwarzo.

Malam Ashiru ai kuwa mun sha yin bayani a wannan shafi a baya.  Watakila ba ka riski bugun da ke dauke da bayanin da nayi ba.  Abin da ke haddasa haka shi ne, da sauti, da haske, da iska, duk kowanne daga cikinsu yana da hanyarsa daban ne a sararin wannan duniya ta mu.  Duk sadda wani ya shiga hanyar wani, nan take ake samun tangarda.  Kamar ruwa ne da muke sha da kuma iskar da muke shaka; kowanne hanyarsa daban.  Idan wani ya shiga tafarkin wani, dole a samu matsala.  In abin ma yazo da karen kwana, shikenan.  Tsarin yanayin sadarwar rediyo ta sha bamban da na wayar salula.  Idan aka samu cin karo a tsakaninsu dole a samu matsala.  Haka tsarin sadarwa idan ya ci karo da hanyar wutar lantarki, a kan samu matsala.  Shi yasa idan ka kusanci dirkan wutar lantarki da rediyonka, za ka ji tashoshin sun rikice.  Da fatan ka gamsu.


Salam Baban Sadik, ya aiki? Kullum idan na shiga shafin Blog di na na google, sai na ga sako cewa “zan iya samun kudi ta hanyar Adsense.” Shin ya abin yake ne? Bashir Ahmad

Malam Bashir kenan!  Ai wannan wata sabuwar hanya ce da kanfanin Google ya kirkira don samun abin masarufi ga masu gidajen yanar sadarwa ko shafukan Mudawwanai (Blogs).  Idan ka je kayi rajista, za ka basu adireshin gidanka, da lambar taskar ajiyarka, da adireshin gidan wayarka, da kuma adireshin gidan yanar sadarwarka.  Bayan wasu ‘yan kwanaki za su turo maka wasu shafuka da za ka shigar a shafinka, masu dauke da tallace-tallace kan abin da ke da nasaba da bayanan da ke shafinka.  Duk wanda ya ziyarci shafinka, idan ya matsa wadannan bayanai na tallace-tallace masu dauke da bayanai da ke shafinka, akwai masarrafar da ke kididdige yawan matsawar da masu ziyara ke yi.  A karshen wata sai a duba yawan shafukan da aka matsa na tallace-tallace, sannan a kirga maka kudinka.  Kowane matsawa akwai adadin kudinsa.  Wannan shi ake kira “Pay Per Click.” 

Idan a karshen wata kudinka ya kama dala dari biyar ne, sai su aiko maka da “Money Order.”  Takardar kudi ce mai dauke da adadin kudinka.  Kana iya zuwa banki ka sanya cikin taskarka, idan kana da taska mai daukan daloli (Dormiciliary Account).  Amma dole mu sani cewa, Google na da masarrafar da ke lura da wadanda ke matsawa. Haramun ne a gareka a matsayinka na mai shafin, ka matsa kowanne daga cikin wadannan bayanai na tallace-tallace. Idan ka matsa, sun sani.  Domin wasunmu sai su dauka ko Google wawaye ne, sai su ta matsawa.

Wannan zamba cikin aminci ne, kuma suna iya ganewa, kuma ba za su kirga da irin wadannan matse-matse na cuta ba.  Haka idan ka umarci wasu su rika matsawa don dabara, duk suna lura. Domin suna da bayani kan inda kake zama, don haka idan yawan masu matsawan suna wuri guda ne da kai, duk baka tsira ba.  Abin da ake so shi ne, ka bar abin yadda yake, duk wanda ya matsa, za a kididdige maka.  Ko a musulunci bai kamata ka matsa ba, bai kuma kamata ka umarci wani ya matsa maka ba. Ka hakura da abin da ka samu na halal, shi yafi mai yawa na haram.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.