Sakonnin Masu Karatu (2011) (19)

Ci gaban sakonnin masu karatu.


Allah ya kara lafiya da ilimi da nisan kwana. Allah ya raya iyali. Allah ya sa mu dace, amin.  Abba Ibrahim Gwan-Gwan, Mai bibiyar rubutunka a kodayaushe.

 

Malam Abba mun gode da addu’ar fatan alheri, kuma Allah biya mana bukatunmu gaba daya, baki daya, amin.  Duk matsalolin da muke fama da su a al’ummance, Allah mana maganinsu, amin.


Assalamu alaikum Baban Sadiq, dan Allah a taimaka mini; duk sadda na shiga masarrafar Google Maths don aiwatar da wani lissafi, amsar ba ta fitowa, sai dai a kawo mini wasu misalai daban.  Daga Sadiq Usman, Bauchi

 

Malam Sadiq yana da kyau ka san cewa masarrafar “Google Maths” masarrafa ce mai dauke da tsarin mu’amala.  Duk sadda ka zo amfani da ita don neman amsar wata ka’ida ta lissafi (maths formular solution), dole ne ka shigar da ka’idojin da suka kamata.  In kuwa ba haka ba, ba za ka samu amsar da kake so ba.  Sai dai ta yi ta rubuto maka misalai, don ka samu misali kan abin da ya kamata ko yadda ya kamata ka shirya tambayarka.  A tunanina wannan shi ne abin da yasa suke ta aiko maka da  wasu misalan.  Ka tabbata ka shigar da ka’idar lissafi (maths formular) sananniya, kafin neman a baka amsa. Sai a kiyaye nan gaba.


Salam, Baban Sadiq ina karuwa da kuma samun annashiwa game da rubuce-rubucen kimiyyarka a cikin jaridar Aminiya. Sai dai na so in san tazarar Tauraron binciken daga duniya a zamanin shawaginsa a kololuwar sama da kuma irin nasarar da ya cimma a lokacin rayuwarsa.  Ibrahim Zubairu, Kufena College Zaria

 

Malam Ibrahim bayanai makamantan wannan sai dai a je gidan yanar sadarwar NASA, watau Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta kasar Amurka.  Gidan yanar sadarwarta na www.nasa.gov in Allah ya yarda za a samu dukkan wadannan bayanai.  Kada a mance, sunan wannan Tauraron dan adam dai shi ne: Upper Atmosphere Research Satellite (UARS).  Da fatan an gamsu.


Assalamu alaikum. Yanzu na gama karanta makalarka. Allah Ya saka da hairan, kuma Ya taimaka. Nadabo Idris Dabi, Ringim.

 

To amin, Malam Nadabo.  Muna godiya har kullum.  Allah saka da alherinsa, amin.


Assalamu Alaikum, Baban Sadik Allah ya saka ma da alheri akan wannan karantarwa da kake yi a jaridar Aminiya, a filin Kimiyya. Da fatan Allah ya kara maka fahimta da ilmi mai amfani, domin anfanarwa, Allah kuma ya yi jagora, amin.  Daga Muhammad, Kyari, Aumtco.

 

To ni ma ina godiya sosai Malam Muhammad.  Allah mana jagora baki daya, ya kuma sa mu zama haske ga al’umma ba duhu ba, amin.


Salam Baban Sadik, barka ya aiki. Don Allah ina so ka turomin mukalolin da ka rubuta a AMINIYA kan Facebook, Twitter, Youtube, Wikileaks da Wikepedia, ta auwalabdulqadirsani@yahoo.com. Wassalam

 

Malam Auwal duk cikin wadannan ina kyautata zaton “Wikileaks” ne kadai muka yi rubutu kansu.  Sauran duk sai dai amsoshin tambayoyi da suka dangance su. Amma a hankali za mu yi bayani musamman kansu.  Idan ka ga haka, sai ka tuna mini, don ba lalai bane in tuna; kwakwalwar tawa ba ta ja sosai wajen halarto abubuwan baya.  Na tura maka wanda muka rubuta kan “Wikileaks” inshallah.  Da fatan an gamsu.

Baban Sadik

Baban Sadik marubuci ne, kuma mai bincike a fannin kimiyya da fasahar sadarwar zamani da tasirinsu ga al'umma a kasashen Afrika, musamman Najeriya. Ya tanadi wannan shafi ne don taskance dukkan kasidun da yake gabatarwa a shafinsa na jaridar AMINIYA mai take: "Kimiyya da Kere-kere," wanda ya faro tun shekarar 2006; shekaru goma kenan a takaice. Bayan kasidun shafin jarida, wannan shafi har wa yau yana dauke da wasu kasidun da ya gabatar a tarurruka da aka gayyace shi, ko wasu hirarraki da gidan rediyon BBC Hausa yayi dashi a lokuta daban-daban. Baban Sadik na zaune ne a birnin tarayyar Najeriya, wato Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *