Sakonnin Masu Karatu (2011) (20)

Wadannan sakonnin tsokaci ne da wasu cikin masu karatu suka rubuto.  Sakon a fili yake, ba ya bukatar karin bayani ko wata amsa.


Baban Sadik Allah ya kara basira.  Na ji dadin wannan bayani.  Zan kira shi “Mabudin Ilmi.” Hakika duk ilmin da ba imani, da sanin mahalicci, da yarda da dokokinsa, da aiki da shi a cikinsa, to bata ne.  A huta lafiya.  –  Mustapha, Kofar Nasarawa, Kano: 08052228790


Assalaamu Alaikum, na ji dadin bayananka kan addini.  A “Kundin Gwamna Lugga” shafi na 131 da 135, akwai tsokaci game da karatun boko, (cewa):  “Dole ne mu tsaya mu ga an koyar da duk wani abu na kyautata halayen yara da ke makarantu, domin su zama masu alkunya da sanin ya kamata. Ba wai a yi ta ba yara ilmi kawai ba, satata babu kyawawan halaye.  Dole ne Gwamnati ta tsaya tsayin daka ta ga an samar wa addini gindin zama.” 

 

A shafi na 135 kuma ya sake cewa: “Mai hankali hattara yake yi da abin da ya samu waninsa. (Tsantsar) karatun boko ya jawo tsiya, da bala’i, da tajrifi a kasashe kamar Hindu, da Sin, da nahiyar Afirka, a sanadin bokon da ba a gauraya shi da addini ba.  Duk wanda ya yi bokon da ba addini, to ya shiga uku, domin ba zai girmama iyayensa ba balle magabatan garinsu.  Shi kansa ma ba zai iya yi wa kansa abin alheri ba.  Wannan yana daga cikin abin da Lugga ke baiwa ma’aikatansa a cikin kundinsa mai suna: “Political Memoranda.”  – Mahfouz Tasiu Abdullahi, Kano: 08026506085

Baban Sadik

Baban Sadik marubuci ne, kuma mai bincike a fannin kimiyya da fasahar sadarwar zamani da tasirinsu ga al'umma a kasashen Afrika, musamman Najeriya. Ya tanadi wannan shafi ne don taskance dukkan kasidun da yake gabatarwa a shafinsa na jaridar AMINIYA mai take: "Kimiyya da Kere-kere," wanda ya faro tun shekarar 2006; shekaru goma kenan a takaice. Bayan kasidun shafin jarida, wannan shafi har wa yau yana dauke da wasu kasidun da ya gabatar a tarurruka da aka gayyace shi, ko wasu hirarraki da gidan rediyon BBC Hausa yayi dashi a lokuta daban-daban. Baban Sadik na zaune ne a birnin tarayyar Najeriya, wato Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *