Sakonnin Masu Karatu (2011) (5)

A yau kuma ga mu dauke da wasikunku da kuka rubuto don neman karin bayani ko kuma gamsuwa da kasidun da ke bayyana a wannan shafi a duk mako.  Kafin nan, ina baiwa Malam Kamal Bala hakuri kan saba masa alkawari da nayi.  A gafarce ni.  Na shagala ne saboda lalurorin rayuwa.  Bayan haka, shafin Kimiyya da kere-kere na mika godiyarsa ga dukkan masu karatu.  Allah ya bar zumunci, amin.

62

Malam na taba karanta wani littafi da ke cewa, miliyoyin shekaru da suka wuce, gobara ce ta ci dazuzzuka da namun daji, ta gangarar da tokar ga tekuna, wanda hakan ya samar da Miniral oil. Ya gaskiyar binciken yake ne? Ka huta lafiya. Naka Khaleel Nasir Kuriwa Kiru 07069191677

Malam Khaleel, ban taba karanta wani bayani makancin wannan ba, duk iya karatu na.  Abin da na tabbatar da shi cikin kasidar da ta gabata kwanakin dai shi ne abin da dukkan masana da masu bincike suka tabbatar, kuma a iya tunani na, ina ganin shi ne abin da ya fi dacewa da hankali.  Da fatan ka gamsu.


Salamu alaikum, tambaya ta itace, Malam ya ake neman kudi daga asusun banki  ta wayar hannu?. Daga: Aliyu Mukhtar Sa’idu (I.T) Kano 08034332200 /08186624300 Email: aliitpro2020@yahoo.com

Hanyar neman kudi ko bukatar cire kudi daga asusun banki ga mai shi, ya danganci tsarin bankin da mai ajiya ke yin ajiya a cikinsa.  Kowane banki na da nashi tsarin.  Amma a kimiyyar tsarin sadarwar zamani, wannan wata sabuwar hanya ce da mai ajiya zai iya amfani da ita wajen sanar da bankinsa cewa yana bukatar wasu kudade daga abin da ya ajiye a asusunsa.  Zai kuma sanar da su wanda za a biya shi kudin, a wani reshe na bankin da ke wani gari ko birni ko unguwa daban.  Wannan tsari, a iya sani na, banki daya ne kadai ke amfani da shi a Nijeriya.  Bayan bukatar kudi ma, akwai tsarin da zai rika sanar da kai ko nawa aka cire ko ka cire daga cikin asusunka.  Wannan tsarin kusan dukkan bankuna suna da shi. A takaice dai dukkan wadannan tsare-tsare ne da kowane banki yana da irin na shi.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum, Baban sadiq don Allah yaya ake bude gidan yanar sadarwar ne, watau “Website”? Kuma bayan an bude akwai wasu kudi da ake biya a kowane wata, ko shekara ne.? Rabiu Isa Ayagi

Malam Rabi’u barka da warhaka, kwana biyu.  Bude gidan yanar sadarwa yana bukatar abubuwa masu dama.  Da farko dai idan kaine ke son a bude maka, za ka tanadi dukkan bayanan da kake so a zuba a shafin.  Wannan shi ake kira “Content”.  Daga nan sai ka nemi wadanda suke aikin gina gidan yanar sadarwa, ko “Web Designers”  a turance, ka biya su, su gina maka.  Idan kuma ka iya, sai ka gina da kanka.  Bayan haka sai ka nemi masu adana gidajen yanar sadarwa a uwar garke, watau Internet Service Providers ko Hosting Companies, a turance.  Su ne za su karbi wannan ginannen gidan yanar sadarwa da aka gina maka, mai dauke da dukkan bayanan da ka bayar aka zuba a ciki, su sanya a cikin kwamfutocinsu, su nemo maka suna ko adireshin gidan yanar, wanda da shi ne duniya za ta rika amfani don sheda gidan yanar.  Za ka biya su kudin wannan aiki na nemo maka suna ko adireshi, da yin rajistan adireshin, sannan kuma ka biya su kudin adana maka shafin yanar.

Idan kuka gama yarjejeniya, ka biya, a cikin kwamfutocinsu ne wannan gidan yanar sadarwa naka zai rika zama, daga nan za a rika ziyartarsa.  Idan shafi ne da ke bukatar a rika sabunta bayanan da ke cikinsa, dole ne ka dauki mai lura da shafin, watau Webmaster kenan, kana biyanshi shi ma.  Duk lokacin da wasu sababbin bayanai suka samu, shi za ka ba shi ya rika sanyawa a cikin shafin.  Dukkann hidima, kamar yadda ka sani, suna bukatar kudade.  Ya danganci yarjejeniyar da ke tsakaninka da kamfanin ko mai lura da shafin.  Wasu kan karbi na wata wata, wasu kuma shekara shekara.  Da fatan ka gamsu.


- Adv -

Baban Sadik Allah ya taimakeka ya raya mana Sadik. A takaice me yasa idan ka bude Imel za ka ga suna a sama kuma da wasu lambobi akan sunanka. Wai me yasa? Daga R. M. Haidar, Kano

Abin da ke faruwa shi ne, a lokacin da kake budewa ko yin rajistar akwatin wasikar Imel dinka ka bayar da sunanka da na mahaifinka ko lakabinka.  Don haka a duk sa’adda ka shigo shafin akwatinka, sai a yi maka “barka da shigowa”, tare da ambaton sunanka.  Dangane da lambobi da kace a saman suna kuma, ban taba lura da wannan ba.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum, suna na Abubakar Ayuba, dalibi a A.B.U. Don Allah ko za ka taimaka mini da kasidar “Tsaga a jikin wata: Mu’ujiza ko yawan shekaru?”, tun daga na 1 har na karshe ta abuayuba2000@yahoo.com, kasancewar zai tallafa wa fagen da nake so in yi Digiri na na biyu. Na gode!

Malam Abubakar na tura maka dukkan kasidun ta adireshin da ka bayar, kuma muna maka addu’ar Allah ya taimaka maka, ya agaza maka, ya kuma sa ka dace da dukkan sauran ‘yan uwa dalibai baki daya, amin.


Salam Baban Sadik, da fatan kana lafiya, yaya aiki? Dan Allah ina son a yi mana bayani akan “Memory Card” na wayar salula. Shin, yana da tsarin sadarwa ne shi ma kamar Katin SIM ko kuwa?  Kuma mene ne a makare a cikinsa? Wasu lokuta sai in ga an ce wannan “126MB” ko “256MB” ko “512MB” ko kuma “1GB,” amma kuma duk girmansu daya a ido. Mun gode.  Mustafa A. Kazaure.

Malam Mustafa barka da warhaka, wannan tambaya taka tana da ma’ana sosai.  Da farko dai, lafazin “Memory Card” shi ne katin ma’adanar bayanai irin na wayar salula, wanda take zuwa da shi ko kuma ake iya saya a sanya mata.  Amfaninsa shi ne, baiwa mai wayar damar adana wasu bayanai da suka shafe shi, na sauti, ko na haruffa, ko hotuna, ko kuma bidiyo.  Bayan haka, a duk lokacin da mai amfani da wayar salula ya shiga Intanet don saukar da wasu bayanai, idan ma’adanar wayar ta cike, watau Phone Memory, nan take za ta karkatar da akalarta ne zuwa cikin wannan kati don adana bayanan.  Idan kuwa katin ya cike, to ba za ta iya adana bayanan ba.  Bayan haka, katin SIM ya sha bamban da katin ma’adanar bayanai da ake kira Memory Card.  Katin SIM ne ke dauke da tsarin sadarwa na kamfanin wayar da ke bayar da shi.

Amma katin ma’adanar bayanai na zuwa ne wayam, babu komai a cikinsa.  Dangane da abin da ya shafi mizani, katin ma’adanar bayanai na Memory Card nau’i-nau’i ne.  Mai daukan bayanai iya nauyin haruffa miliyan dari da ashirin da shida, watau 126MG, da mai daukan nauyin miliyan dari biyu da hamsin da shiga, watau 256MG, da mai daukan nauyin miliyan dari biyar da goma shabiyu, watau 512MG, sai kuma wanda ke daukan nauyin biliyan daya, watau 1GB.  Bayan wadannan, akwai masu daukan nauyin biliyan biyu, da uku, da hudu, da biyar, har zuwa talatin da shida ma.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.