Sakonnin Masu Karatu (2011) (9)

Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.

157

Aminci ya tabbata ga Baban sadiq, ina fatan kana cikin koshin lafiya. Ina rokon Allah ya kara basira. Don Allah kayi min karin bayani kan yadda zan yi rijista a imel? Godiya nake Daga Aliyu mai sa a T/wada zaria 08033760456

Malam Aliyu hakika Baban Sadik na godiya da addu’o’in da ake ta yarfo masa.  Dangane da abin da ya shafi bude Imel, sai ka je gidan yanar yahoo da ke http://mail.yahoo.com, kada ka haruffan “www”, domin a gidan yanar shafin yake.  Idan shafin ya budo, a kasa daga hannun dama za ka ga inda aka rubuta “Sign Up” sai ka matsa, za a budo maka fom da za ka cika, sai ka aika musu.  Daga nan za ka iya aiwatar da sadarwa ta hanyar Imel.  Ka lura, ba kowace wayar salula ke iya bayar da damar yin rajistar Imel ba, idan ba irin su Blackberry bane.  Don haka nake bayar da shawarar zuwa “Cyber Café” a yi rajista ta kwamfuta, don haka ya fi sauki.  Da fatan an gamsu.


Assalamu Alaikum Baban Sadik, na ga amsar tambayar da ka bayar game da zanen hannu. To tambayata a nan ita ce: tunda zanen hannun kowa daban yake, ba mutun biyu masu zanen hannu iri daya, yaya sakanin hannun dama da na hagu na mutun daya, daidai suke ko su ma daban-daban suke? Muhammad Ibrahim Kaduna

Malam Muhammad ai wannan tambaya ce mai sauki, kana iya gano amsar da kanka. Amma tunda har ka rubuto, amsar ita ce su ma akwai bambanci a tsakaninsu.  Ka duba yatsun hannayenka ka gani, za ka tabbatar da hakan.  Da fatan an gamsu.


Baban Sadik ina maka fatan alheri, Allah ya saka maka da gidan aljanna bisa gwagwarmayar da kakeyi, muna godiya. Don Allah me ye ma’anar “USB Cable?” Kuma wanda bai san kan kwamfuta ba yana son mu’amala da Intanet ta waya, ya zai yi?  Kuma ya za a yi a san waya mai intanet?  Kuma za a iya bude imel din da aka rufe yanzu?  Harira Said BK KD.

Malama Harira barka da warhaka, da fatan ana lafiya.  Ma’anar “USB”  dai a takaice shi ne tsarin shigar da bayanai ga kwamfuta ko na’urar sadarwa ta hanya mafi sauki.  Cikakken lafazin haruffan USB shi ne: “Universal Serial Bus.”  Duk kwamfutar da ke dauke da wannan tsari na USB, akwai wayar da ake shigar mata don aiwatar da sadarwa ta wannan tsari.  Wannan waya ita ake kira “USB Cable.”  Ba kwamfuta kadai ba, hatta wayoyin salula suna da wannan tsari mai tasiri.  Bayan haka, wannan tsari shi ya fi saurin sanar da kwamfuta ko na’urar sadarwa cewa “ga wasu bayanai nan da ake son shigar miki ko karba daga gareki, don haka ki shirya.”  Da zarar an tsofa wa kwamfuta wannan waya, nan take yake zarcewa cikin kwakwalwarta ba bata lokaci.  Bayan haka, mu’amala da fasahar Intanet ta hanyar wayar salula ba ya bukatar kwarewa a fannin kwamfuta.  Abin da ake bukata mafi karanci shi ne mutum ya iya rubutu da karatu, sai a koya masa yadda zai yi.  Hakan ba zai yi a rubuce ba sai a aikace. 

Sannan ana iya gane wayar salula na dauke da Intanet ne ta hanyar shiga “Menu”, a can kasa za a ga alamar “Web”, ko “Internet”, wannan ke nuna cewa wayar tana dauke da tsarin Intanet. A karshe, ana iya bude ko farfado da akwatin Imel din da aka rufe, wannan shi ake kira “Reactivation of Account”, kamar yadda ake farfado da taskar ajiya a banki idan aka dade ba a yi amfani da shi ba.  Sai a shiga ta hanyar sanya adireshin Imel din da kalmomin iznin shiga wato “Password”, da zarar an matsa enter, shafi zai budo da ke nuna cewa wannan akwatin Imel din an dakatar da shi, idan kana son farfado da shi ka matsa nan, a misali.  Da zarar an matsa, nan take za a bude. Da fatan Malama Harira ta gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadiq, barkanka da war haka. Da fatan kana lafiya. Baban sadiq a duba min madawwana da na bude mai wannan adireshi kamar haka: http://b-techcoms.blogspot.com. Shin, na bude ta kamar yadda ya dace? Ko akwai kurakurai? In akwai ta yaya zan gyara? Ina bukatan shawarwari ta yadda zan dada ingantata. Na gode, Allah Ya saka da alkhairi, Ya kuma dada basirah, amin. Wassalam! Daga Uncle Bash, Jimeta-Yola. bysalihu@gmail.com

Uncle Bash na shiga wannan shafi naka, kuma  lallai ka yi kokari.  Ai na dauka da harshen Hausa ne, ashe da yaren Ingila ne.  To Allah taimaka, amin. Abin da na gani wanda ke bukatar gyara shi ne, ka cire bayanan da ka sa a karkashin sunan Mudawwanar, wanda na ga kamar taken kasidar da ka sa a shafin ne.  Ba a nan ya kamata ka rubuta taken kasidar ba.  Tunda har ka sanya taken a saman kasidar, ka cire wanda ke karkashin sunan Mudawwanarka.  Sannan abu na biyu, ka cire adireshin Imel dinka daga jikin Mudawwanar, ka kura cire lambar wayarka.  Domin ‘yan dandatsa na iya amfani da wannan dama su rika turo maka sakonnin bogi, wato “Spam Mails”, haka ma ‘yan 419, suna iya daukan lambar wayarka su yi ta damunka.  Kana iya cire su, ka je wajen “Settings” ka shigar da su. 

- Adv -

Duk mai neman Karin bayani kan saduwa da kai na iya zuwa can ya samu.  Sannan idan ka zo zuba kasidu a shafinka, ka rika gyatta tsayuwansu, wato “Formatting”, ka rika “Justify” din kasidun, wannan zai sa su samu diri mai kyau, ka gansu tsaf-tsaf, kuma rau-rau.  Sannan ka lazimci nau’in “font” guda daya.  Allah sa a dace, amin.


Assalaamu Alaikum Abban Saddiq, na ga wata ammsar da ka bayar, (Aminiya juma’a 10 ga yuni 2011) cewa sai mutum na da adireshin imel kafin ya samu damar ma’amala da dandalin facebook. To a yanzu an samu gyara; mutum zai iya amfani da lambar waya don bude dandalin facebook kamar kowa ka huta lafiya. Muh’d auwal kurna fagge kano.

Malam Auwal na gode da wannan fadakarwa.  Alal hakika haka dama lamarin yake ga masu amfani da wayar salula musamman wajen aika sakonni zuwa shafukansu, ba daga baya bane suka samar da abin.  Abin da yasa nake yawan ambaton cewa sai da adireshin Imel shi ne don galibi a kan shiga ne ta shafin facebook mai dauke da tsarin shafin kwamfuta, wato “Normal Mode,” kuma a wannan tsarin, ana amfani ne da adireshin Imel, saboda idan ka bude, za su tura maka wasu kalmomi na sirri, wadanda za su bukaci ka sanya su idan ka sake dawowa don bude shafinka.  Duk da haka wannan fadakarwa ce mai kyau da muhimmanci musamman ga wadanda basu sani ba.  Mun gode.


Assalamu alaikum Baban Sadiq, barkanka da aiki. Ina fatan kana lafiya, Allah Yasa haka, amin. Tambaya na shi ne: mutum zai iya saka manhajar kariya daga kwayar cutur ‘kwamfuta (Anti-virus software) guda biyu, kamar Avast da AVG Anti-virus a ‘kwamfuta daya suna aiki ba tare da wata matsala ba? Ko Kuma yin hakan zai iya kawo wa kwamfutar cikas wajen sarrafata? Wassalam. Daga Uncle Bash, Jimeta-Yola. bysalihu@gmail.com 08185292655

A gaida Uncle Bash na mu.  Ai ba zai taba yiwuwa ka sanya wa kwamfuta masarrafar kariya guda biyu ba.  Saboda kowanne daga cikin wadannan masarrafai yana da tsarinsa wajen kariya da ya sha bamban da na dan uwansa.  Misali, manhajar kariya ta McAffe ta sha bamban da na AVG.  Domin wasu bayanan da ba kwayoyin cuta bane, amma za ka ga wasu manhaojin suna nuna maka cewa “ka yi hankali, ga wani abokin gaba nan zuwa,” misali.  A taikaice dai, sanya wa kwamfuta manhajar kariya guda biyu ba abu bane mai fa’ida.  Idan ka sa za su shiga, amma kuma ba za su yi aiki ba. 

Sannan kwamfutar za ta rika baka sanarwa cewa “akwai cin karo a tsakanin manhajojin kariyarka.” Kamar dai mai gida ne ya dauko masu gadin gida guda biyu, daga wasu wurare daban-daban, da tare da kowannensu ya san wannan mai gadin wannan gidan bane.  Ka ga duk sadda wannan ya hangi dan uwansa, zai dauka barawo ne, haka shi ma dayan.  Don aiki daya ne suke yi, amma kowa da tsarinsa, kowa da irin ma’anar da yake baiwa “kwayar cutar kwamfuta” wacce ta sha bamban da fahimta ko tsarin dan uwansa.  Da fatan Uncle Bash ya gamsu.


Assalaamu alaikum Baban Sadik, ya sadik? Da fatan yana lafiya. Dan Allah mai yake sa yawan daukewar sabis? Ko kuma in kayi kira ga shi wayar a bude amma sai taki shiga?

Abin da ke kawo daukewan tsarin sadarwa, ko sabis kamar yadda kace, shi ne rashin ingancin tsarin sadarwar a inda ake, ko dai sanadiyyar matsalar na’urorin sadarwa daga kamfanin, ko sanadiyyar rashin yawaitar cibiyoyin na’urorin sadarwa a jiha ko bigiren da ake.  Har wa yau akwai matsalar yanayi, da matsalar rashin ingancin wayar salula wajen jawo tsarin sadarwa.  Wayoyin salula da kake gani kowacce na da tsarinta wajen inganci ko rashinsa, na abin da ya shafi jawo tsarin sadarwar, don taimaka wa mai kira aiwatar da kira ko karban kiran. 

A karshe, idan komai daidai yake, to yana da kyau har way au mu san cewa ana iya samun tsaiko wajen sadarwa saboda tsarin da ake amfani das hi wajen sadarwar wayar tarho, wato “Radio Waves”, tsari ne da haka kawai yana iya daukewa, sannan ya dawo.  Ya danganci bigire, da tsarin yanayi, da kuma na’urar sadarwa.  Da fatan an gamsu.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. anas gmg says

    Allah yasaka da alheri baban sadiq tambayata shin xan iya sayan software na computer a wayata naturawa computer ?

Leave A Reply

Your email address will not be published.