Sakonnin Masu Karatu (2012) (2)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

79

Baban Sadik barka da bincike. Ni dai idan nayi kira a waya ko aka kira  ni, bayan na gama sai inji hajijiya tana dauka ta, wani lokacin kuma sai inji kunne na ya toshe yana kara kamar kukan gyare.  Don Allah Baban Sadik kayi mini bincike; me ke kawo min hakan?  Daga Ali Fancy, Garko, Kano: 08027921665

Malam Aliyu wannan al’amari ne da ke da alaka ta kai tsaye da kwarewa a fannin likitanci, wanda kamar yadda na sha bayyanawa, ni ba likita bane.  Duk wani illa da na’urorin kimiyyar sadarwar da kere-kere ke haddasawa, ko da an ga na fadi wani daga cikinsu, na hakaito ne daga kwararru, amma ban da kwarewa ta musamman wajen tabbatar da daidai ko kuskuren ire-iren wadannan abubuwa.  Don haka ina bayar da shawara da ka mika wannan kuka naka ga Dakta Auwal Bala a shafin “Kiwon Lafiya.”  Da fatan za a gafarce ni sanadiyyar rashin samun gamsuwa kan wannan mas’ala. Allah baka lafiya, ya kuma sa a dace wajen gano matsalar da ke haddasa wannan lalura gareka, amin.  Na gode.


Assalaamu Alaikum, Baban sadik ga jinjina ta gareka, Allah ya kara maka kwazo, amin.  Na gode: 08162424124

Wa alaikumus salam, ina godiya matuka gare ka/ki da wannan addu’a da jinjina.  Allah saka maka/miki da alheri, amin summa amin.  Na gode.


- Adv -

Baban sadik, ina fatar Allah ya kara maka lafiya, tare da mu, amin summa amin. Daga Nasiru Sani Gusau: 07064340375

Na gode matuka Malam Nasiru, kaima Allah saka maka da alheri mai dimbin yawa. Allah kara mana fahimta da juriya wajen daukan ilimi da aiki da shi, amin.


Assalaamu alaikum, me yasa idan sakon tes bai tafi ba, amma kuma sai a cire wa mutum kudi?  Musa Bamalli, Zariya: 08035951530

Wa alaikumus salam, da fatan ana lafiya.  Hakan ya danganci tsarin kamfanin waya ne. Galibinsu sun saita na’urarsu ne ta rika debe kudin hidimar aika maka sakonka da zarar ka masa maballin aika sakon da ke wayarka.  Idan aka samu tangardar girgidin yanayin sadarwa (Network Fluctuation), sakon bai je ba, shikenan, kudinka sun sha ruwa. A ka’ida ba haka ya kamata abin ya zama ba.  To amma tunda hakar na’urar take, ba yadda suka iya.  Kamfanin waya daya ne na sani a kasar nan wanda ke iya dawo maka da kudinka nan take idan tes bai je ba, ko da bayan kwana daya ne.  Wannan kamfani shi ne na Visafone, wanda kuma bai yadu ba sosai a kasar nan.  Don haka sai dai hakuri.

Wannan wata masala ce wacce idan mutum na da lokacin da zai iya batawa, yana iya gyatta ta, ta hanyar zuwa da sanar dasu halin da kake ciki.  To amma nawa za ka kashe zuwa ofishinsu? Nawa za ka kashe wajen dawowa?  Idan suka ki, kace dole sai an biya ka, sai dai kotu.  Nawa za ka kashe wajen tsayar da mai kwato maka hakkinka, wato Lauya?  Don haka sai dai hakuri.  Allah sa mu dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.