Sakonnin Masu Karatu (2013) (2)

Kamar yadda aka saba lokaci zuwa lokaci, ga wasu daga cikin sakonninku nan.  Wannan kashin farko ne, a mako mai zuwa in Allah yaso zan turo kasha na biyu.  Don Allah a rika turo sakonni masu ma’ana, kuma a rika rubuto wuri da sunan mai aikowa.  Allah sa mu dace, amin.

53

Malam meye ingancin kwamfuta nau’in HP da DELL wajen rike caji?  Daga: 08073188022

A gaskiya ya danganci abubuwan da kwamfuta ke dauke dasu na masarrafai, da tsarin babbar manhajar da ke dauke a cikinta.  Amma la’akari da kamfanin da ya kera kwamfuta don gano ingancin batir ba abu bane da zai bayar da kyakkyawar sakamako.  Abin nufi, idan ana son gano karkon batir din kowace kwamfuta, ba a la’akari da kamfanin da ya kera kwamfutar, sai dai a yi la’akari da nau’in babbar manhajar da ke kwamfuta, da yawan masarrafai ko manhajojin da take dauke dasu.  Wani abin lura bayan wadannan kuma shi ne tsawon rayuwar batir din tun sadda aka kera shi.Idan babbar manhajar da ke dauke cikin kwamfutar tana da nauyi, sanadiyyar darurun manhajoji da masarrafan da ke taimaka mata wajen aiwatar da ayyukanta, wannan na nufin kwamfutar za ta rika zukar makamashi sosai.

Haka idan akwai wasu abubuwa da aka makala mata don sadar da bayanai, kamar ma’adanar filash, da faifain CD/DVD, da makalutun sadarwa na Intanet (Internet Modem); duk wadannan na jan makamashi musamman idan kwamfutar ba a jone take da wutar lantarki ba.  Amma la’akari da kamfanin da ya kera kwamfuta kadai ba ya nuna ga batir din ya yafi karko.

Idan kana son batirinka yayi karko, ka rage yawan mu’amala da wasannin kwamguta (computer games).  Ka cire duk wata na’ura da makala wa kwamfutar da zarar ka gama amfani da ita.  Ka rage mizanin sautinta (system volume).  Idan akwai CD ko DVD  a cikin ma’adanar CD ROM dinka, ka rika cire shi da zarar ka gama amfani da shi.  In so samu ne, da zarar ka sa CD ko DVD mai dauke da sauti ko bidiyo, ka kwafe shi zuwa babbar ma’adanar kwamfutar kawai, don rage mata mizanin makamashi da za ta rika zuka.  Sannan ka rage kaifin hasken shafin kwamfutar (Screen Brightness).  Sannan ka bi duk inda wata masarrafa mai gudanuwa ta karkashin kasa (Background tasks) take aiki, wacce ba ka bukatarta, ka dankwafe ta.  Wadannan, kadan ne daga cikin abubuwan da mai kwamfuta zai yi don rage yawan makamashin da kwamfutar take zuka idan ya zare ta daga kan wutar lantarkai kai tsaye.  Da fatan ka gamsu.


Assalaamu alaikum Baban Sadik, don Allah wai yaya Facebook suke hada mutum da dan uwansa ko wani wanda ya sani (People you may know)?  Abin yana bani mamaki, sai in ga hoton wanda na sani an kawo, ko ma dan uwana na jini; duk da ba ni na nema ba.  Ya abin yake ne?  Daga: Usman Muazu Funtua, Katsina

Wa alaikumus salam Malam Usman, barka dai.  Wannan abin da kake gani kuma yake baka mamaki ba maita bace, ba kuma sihiri bane; kintsi ne irin na manhajar kwamfuta ta musamman da hukumar Facebook ke amfani da ita wajen hada alaka tsakaninka da wadanda ka sani ko ka san wadanda suka sansu, ta la’akari da nau’ukan bayanan da ka shigar a shafinka sadda kake bude shafin ko bayan ka bude.  Kada ka mance, a sadda kake bude shafin ka bayar da sunanka, da gari ko wurin da aka haife ka, da jiharka, da kasarka, da addininka, da ra’ayoyinka na siyasa ko addini watakila, sannan ka fadi sunan makarantun da kayi a baya ko kake kanyi, da wuraren da kayi aiki a baya ko kake kanyi; wadannan bayanan ne suke amfani dasu wajen nemo wadanda bayanansu suka dace da naka, don haka alaka a tsakaninku.  Domin, in har bayanan da kuka bayar  (kai da su) a sadda kuke bude shafinka sun zo daidai, to babu yadda za a yi a kasa samun alakar sanayya a tsakaninku.

- Adv -

Wannan shi ne abin da suke yi.  Amma cikakken bayani kan yadda hakan ke faruwa ba abu bane mai sauki.  Akwai sarkakiya sosai cikin lamarin.  A takaice ma dai, a duniyar Intanet ta zamanin yau, samun shafi mai dauke da cunkoson manhajoji, da sarkakiya ta kwarewa (professional sophistication), irin shafin Facebook.  Abin sai wanda ya kware a fannin kimiyyar sadarwa na zamani zai iya fahimtarsa cikin sauki.  A takaice wannan shi ne abin da hukumar Facebook ke yi wajen bijiro maka da wadannan mutane da kake ganin ka sansu, amma baka bukaci a bijiro maka dasu ba, watakila ma ba ka tunanin ganinsu a shafin.  Da fatan ka gane.


Assalamu alaikum Baban Sadik, tambayata akan Google ne; shin, ta yaya aka samar dashi, kuma yaya yake ajiye bayanai a cikin kwamfutocinsa, sannan kuma shin, ko akwai hukuma mai kula da wannan shafi?  Daga: Nasiru Dauran, Talata Mafara, Zamfara

Wa alaikumus salam, Malam Nasir barka ka dai.  Shafin Google, ko Manhajar Google, ko Kamfanin Google, duk abu abubuwa ne da suka dunkule zuwa abu daya.  Idan kace “Google”, to, hakan na ishara ne zuwa ga dukkan ukun nan, ko biyunsu, ko kuma daya daga cikinsu.  Asali manhaja ca ta zakulo bayanai da wasu samari su biyu suka gina, tun cikin shekarar 2005.  A sannan suna karatunsu na digiri na uku a Jami’ar Stanford dake kasar Amurka.  Wadannan samari dai su ne: Larry Page da Sergey Brin.  Sannan shekarunsu duk basu shige 25 ba a duniya.

Samar da wannan manhaja ta neman bayanai ne ya haddasa kafa kamfani, da gidan yanar sadarwa mai dauke da manhajar, don taimaka wa masu neman bayanai don bincike ko gamsarwa ta ilimi, samun bayanai ba tare da wata matsala ba. Wannan gidan yanar sadarwa na Google (www.google.com) yana dauke ne da wata manhaja mai suna “Google Crowler,” wacce ke yawo a giza-gizan sadarwa ta duniya (World Wide Web) don debo bayanai, ta amfani da rariyar likau (Web Links), tana zuba wadannan bayanai a kwamfutocin kamfanin, a tsarin ABCD…XYZ.

Wannan tsarin adana bayanai shi ake kira “Indexing” a harshen kimiyyar sadarwar zamani.  Da zarar ka shiga gidan yanar sadarwar ka shigar da kalma, nan take sai wannan manhaja ta zakulo maka dukkan bayanai masu alaka da wannan kalma da ka shigar, ta zuba maka su a gabanka; zabi wanda kake so.  Idan ka latsa nau’in bayanin da kake son isa gare su, sai a cilla ka asalin gidan yanar sadarwar da ke dauke da bayanan kai tsaye, ka duba da kanka.

A hakikanin gaskiya babu wata hukuma da ke lura da wannan gidan yanar sadarwa domin na kamfani ne ba na hukuma.  Wannan kamfani na Google na kasar Amurka ne, duk da cewa yana da rassa a kusan dukkan nahiyoyin duniya. Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.